Ahmed Musa zai gwangwajen tawagar Flamingos da kyautar N3m
Flamingos ta doke tawagar Jamus da ci uku da biyu.
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya yi alkawarin Naira miliyan uku ga tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ’yan kasa da shekara 17.
Kyaftin din zai gangwaje tawagar wacce ake yi wa lakabi da Flamingos a sakamakon samun nasarar lashe kyautar tagulla a Gasar Kofin Duniya ta mata ‘yan kasa da shekara 17 ta bana.
- Ahmed Musa ya ba wa Zawarawa tallafin Naira miliyan 100 a Filato
- AFCON 2021: Ahmed Musa ya ba da tallafin $1,500 don kammala ginin masallaci a Kamaru
Tawagar ta Flamingos dai ita ce ta doke tawagar Jamus da ci uku da biyu yayin fafatawar neman mataki na uku da suka yi ranar Lahadi a Mumbai, babban birnin Kasar Indiya.
Flamingos ta doke tawagar ta Jamus a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan sun tashi kunnen doki 3-3.
Cikin wani sakon taya murna da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ahmed Musa ya ce, “Miliyan uku lakadan na jiranku a Abuja.”
Wannan nasara da Najeriya ta samu, ya sa yanzu ta zamo ta biyu a Nahiyar Afirka da su ka kai ga wannan nasarar bayan kasar Ghana wacce ita ma ta ci lambar tagulla a irin wannan gasar a 2012.
Tawagar matan Sfaniya ce dai ta lashe Gasar Kofin Duniyar ta mata ’yan kasa da shekara 17 yayin da ta lallasa tawagar Columbia da ci daya mai ban haushi a ranar Lahadi.