Aikatau a gidajen manya na gurbata tarbiyyar manyan gobe
Aikatau a kasar Hausa wani abu ne da ya zama ruwan dare, musamman yadda ake amfani da yara masu kananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka hada da shagunan sai da kayan kawa ko abinci, otel otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko jami’o’i (Hostel/Campus). […]
Aikatau a kasar Hausa wani abu ne da ya zama ruwan dare, musamman yadda ake amfani da yara masu kananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka hada da shagunan sai da kayan kawa ko abinci, otel otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko jami’o’i (Hostel/Campus). Akasarin yaran ‘yan kasa da shekaru 15 ne, kuma ana daukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka hada da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, debo ruwa, renon jarirai da kula da yayayyun yara da sauran wasu uzurirrika. Haka kuma mafiya yawan yaran ana kawo su cikin birni daga kauyuka lokaci zuwa lokaci, ta hanyar uwar aikatau bisa amincewar da yawa daga cikin iyayensu, don tunanin samar musu da abin duniya da bai taka kara ya karya ba, musamman idan aka yi la’akari da irin illar da aikatau ke haifarwa a cikin al’umma.
Idan aka duba zuwa aikatau za a tabbatar da illolinsa masu yawa, wadanda suke shafar yaran da ke yinsa da kuma yaran da iyayensu ke daukar ‘yan aikin kai har ma da sauran al’umma baki daya. Babbar matsalar ita ce yadda ake tauye wa ‘yan aiki hakkinsu da kuma gatansu da ya kamata su samu a lokacin kuriciyarsu, misali ilimi na daga cikin hakkin da ya zama tilas a bai wa yara don inganta rayuwarsu da nufin samar da jagorori na gari a nan gaba, sai dai wannan damar takan kubuce wa akasarin ‘yan aiki, musamman yadda ake amfani da su wajen bautar da su a lokutan da ya kamata a ce suna makaranta. Na tabbata irin yadda ake mayar da su tamkar bayi a wasu wuraren ko kare ba a yi masa haka, za ka ga ana yi musu tsawa, ana hantararsu kai wasu har dukansu ake yi, a kuma hana musu abinci, musamman in sun saba umarnin da uwar dakinsu ta ba su. Hakazalika in ka ga makwancinsu a wasu gidajen ko kajin gidan gona sun fisu wajen kwanciya mai kyau, ga rashin hutu da kuma rashin samun wadataccen barci, wanda hakan ka iya yin barazana ga lafiyar jikinsu, kuma duk wannan kuncin ana biyansu wani dan abu kankane ne.
Wata babbar matsalar aikatau ita ce yadda jahilci ke addabarsu a inda mafi yawansu ba su san yadda za su bautawa ubangijinsu ba, sai ka ga tsarki da cikakkiyar alwala na gagararsu, kuma iyayen dakinsu ba su cika damuwa da su rika koyar da su abubuwa masu amfani, musamman yadda za su rika gabatar da ibada tunda ta zama tilas a rayuwarsu, wannan yakan jawo musu ballagazanci da rashin kamun kai idan girma ya zo musu, al’amarin da ka iya jansu ga harkar banza, ko kuma yawon ta-zubar, tunda mafi yawansu ba su iya komawa karkararsu inda suka fito, mazan kuma su zamto marasa aikin yi, wanda illarsa take da yawa a cikin al’umma. Kodayake ba duka aka taru aka zama daya ba, don kadan daga cikin iyayen dakinsu sukan tura su makarantun islamiyya na yamma ko na dare, amma akasari wannan bai cika samuwa ba. Haka kuma tsangwama da barazanar hukuncin muzantawa ko kuma kora gaba daya na zama fargaba a zukatansu.
Wata matsalar kuma ita ce yadda wasu masu gida ko yara matasa da ke gidan kan lalata ‘yan aiki bisa tirsasasu su amince da bukatarsu.
Ina mafita daga wandannan matsalolin?
A hakikanin gaskiya wannan matsalar tana bukatar hada hannuwa domin magance ta, musamman yadda take barazanar lalata tarbiyar yara a matsayinsu na manyan gobe. Da farko iyayen yaran na da mihimmiyar rawa wajen rage wannan matsalar, kodayake halin kunci na talauci da daga cikin babban dalilin dake jawo matsalar amma duk da haka bai dace su rika bada ‘ya’yansu don kaiwa birni bisa rashin sanin takamaiman gidan da za’a kaisu da kuma halin da suke ciki a can ba kuma duk akan dan abin da baikai ya kawoba. Duk da a rayuwar duniya Allah da ya halicci bayinsa ya sanya wasu sunfi wasu, kuma wasu sai sun yi wa wasu aiki za su samu abin da za su ci, to in har ya zama dole ayi aikatau to iyayen yaran su sanya sharadi akan duk mai bukatar ‘yarsu don yin aikatau to dole su sanya ta a makaranta don samun ilimi musamman don sanin yadda zasu gabatar da addininsu.
Hukumomin da ke da alhakin kare mutuncin yara su yunkuro don sanya kwakkwarar doka akan yadda ake azabtar da yara da sunan aikatau a kuma sa doka mai tsauri ga duk wanda aka sameshi da cin zarafi ko kuma bautar da yara. Haka kuma ya kamata gwamnatoci su rika kafa wuraren koyarda sana’o’i don yara maza da mata musamman a yankunan karkara da suka hada da dinki, saka,rini, kere- kere, girke-girke, aikin kafinta da dai sauransu da nufin samar musu da madogara a gaba. Wannan zai hana su yawan fitowa neman abin duniya ta hanyar da ba ta daceba.
A karshe jama’a su bada gudummawa don hana gurbata tarbiyar yara. Masu musgunawa ‘yan aikinsu suma suji tsoron Allah, su sani rayuwa bata da tabbas don kuwa suma yaransu ka iya kasancewa a irin wannan halin kuma su lura da cewar duk abin da ka shuka shi zaka girba, don masu iya magana na cewa “yi alheri kaga alheri, in ka shuka irin sharri kuwa sharrin dai zaka girba a gaba”.
Mudassir ya rubuto daga tashar talabijin ta kasa, wato NTA Zariya.
[email protected]