Aike wa Ukraine makamai: Amurka na kokarin tsokano tsuliyar dodo – Rasha

Rasha na gargadin Amurka kan ba kasar Ukraine tallafin makama

Aike wa Ukraine makamai: Amurka na kokarin tsokano tsuliyar dodo – Rasha

Biden da Putin

Rasha ta gargadi Amurka kan ba kasar Ukraine tallafin makamai, inda ta ce yin hakan tamkar rura wutar rikici ne.

Amurkan dai ta ba da gudunmawar bangaren soji har na fiye da Dalar Amurka biliyan shida tun shekara ta 2014, da kuma wata fiye da Dala biliyan uku a wata biyu da suka gabata.

Da yake jawabi a gidan talabijin na Russia 24 jakadan Moscow a Amurka, Anatoly Antonov, ya ce kai talkafin makaman na Amurka zai kara karfin yakin da yanzu ya shiga kwana na 61 da farawa.

Ya ce suna Allah-wadai da matakin na Amurkan, kuma suna kira gare ta da ta janye wannan manakisar, domin ta na yi ne kawai don kara ta’azzar yakin.

Sakataren Harakokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, da na Tsaro, Lloyd Austin, sun kai ziyara ta farko babban birnin Ukraine din a daren Lahadi, inda suka gana da Shugaban Kasar, Volodimir Zelenskyy.

Sun yi alkawarin taimaka wa gwamnatin Zelenskyy da sauran kasashe da ke yankin da zunzurutun kudi har Dala miliyan 713, tare da alkawarin yan aiken Amurkan za su sake dawowa kasar ta Ukraine nan ba da jimawa ba.

A ranar Litinin ne dai Shugaban Amurka Joe Biden ya zabi Bridget Brink wato wakilin Amurkan a Slovakia ya zamo manzon kasar zuwa Ukraine, domin dorawa da batutuwan da suka shafi diflomasiyya.