Aiki da kayan noma irin na zamani ne mafita ga kasar nan

Rungumar aiki da kayayyakin dabarun noman irin na zamani ne mafitar da za ta kai ga kasar nan ta samu damar ciyar da kanta da abinci har ma ta fitar kasashen waje.  Babban Manajan Hukumar Bunkasa Harkar Noma ta Jihar Kaduna, Malam Sabi’u Sani Isma’il ne ya shaida wa Aminiya haka a zantawar da aka […]

Aiki da kayan noma irin na zamani ne mafita ga kasar nan

Rungumar aiki da kayayyakin dabarun noman irin na zamani ne mafitar da za ta kai ga kasar nan ta samu damar ciyar da kanta da abinci har ma ta fitar kasashen waje.

 Babban Manajan Hukumar Bunkasa Harkar Noma ta Jihar Kaduna, Malam Sabi’u Sani Isma’il ne ya shaida wa Aminiya haka a zantawar da aka yi da shi. “Hukumar ta Bunkasa Harkar Noma ta Jihar Kaduna watau (KADA) ta kuduri aniyar tallafa wa manoma da karin sanin dabarun harkar noma irin na zamani don samar da yalwar abinci a jihar Kaduna da kasa baki daya.”

 Ya kara da cewa, lokaci ya yi da za a rungumi dabarun noman zamani da kayan zamani daga yadda aka gada kaka da kakanni. Kuma rungumar tsarin na zamani yana bude kafar samar da karin samun kudin daga kafafen rance ko bankunan noma na gwamnati da taraktoci da za su kara samar da yabanya da abinci ninkin ba ninki.

 Malam Sabi’u Sani Isma’il ya kuma shawarci manoma da su tabbatar sun rika adana kayan amfanin gona ta yadda ya dace don gudun kar ya gurbata ko ya lalace har ya zamanto an yi asara ,wadda ba a fatan haka.