Aiki ga al’umma ne ya daga ni – Dokta Erisa Danladi
Dokta Erisa Sarki Danladi, manomiya ce kuma ’yar gwagwarmayar ayyukan raya karkara mai fafutika a tsakanin kungiyoyin masu zaman kansu, kuma mai kokarin taimakon marasa galihu. Ita ce Babbar Daraktar Kungiyar Motherhen Debelopment Foundation, sannan ita ce mai kula da sashen Arewa maso Gabas a kungiyar tallafa wa mata ’yan siyasa ta Women in Political […]
Dokta Erisa Sarki Danladi, manomiya ce kuma ’yar gwagwarmayar ayyukan raya karkara mai fafutika a tsakanin kungiyoyin masu zaman kansu, kuma mai kokarin taimakon marasa galihu. Ita ce Babbar Daraktar Kungiyar Motherhen Debelopment Foundation, sannan ita ce mai kula da sashen Arewa maso Gabas a kungiyar tallafa wa mata ’yan siyasa ta Women in Political Empowerment. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihita da gwagwarmayarta:
Tarihin rayuwata
Sunana Erisa Danladi Sarki, ni ’yar garin Dala Waja ne kuma ’yar kabilar Waja a Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe. Ina daga cikin mata masu kananan shekaru da suka yi fice a duniya ba a Najeriya kadai ba daga wannan yanki namu na Gombe ta Kudu.
An haife ni a 1981, na yi Firamaren ’Ya’yan Ma’aikatan Kwalejin Ilimi (FCE Staff School) ta Gombe daga nan na tafi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke garin Owerri a Jihar Imo. A lokacin saboda rikicin siyasa na 12 ga Yuni ban gama a can ba, sai na dawo Gombe na kammala sakandare dina a Gombe High School a 1999.
Da na gama sai na yi jarrabawar share fagen shiga jami’a, na samu shiga Jami’ar Maiduguri don karanta Fannin Shari’a, sai zafin garin Maiduguri ya hana ni zama. Sai na dawo Yola na rubuta IJMB na tafi Jami’ar Jos na sake cika fannin shari’a (Law) amma ba su ba ni ba, suka ba ni Wasan Kwaikwayo da Sadarwa (Theater and Communication). Haka na hakura na karba na yi digiri na farko a lokaci daya kuma ina yin Diploma a Shari’a duk dai saboda in zama lauya amma Allah bai nufa ba.
Da na gama digiri sai na tafi hidimar kasa (NYSC) a Enugu, bayan na gama sai na nemi aiki a Bankin Zenith, kuma suka kira ni jarrabawar daukar aiki. Ina nan ina jira shiru har na fara zuwa kwadago a gona wato na fitar da tsammani a kan aikin banki. Ina nan har na fara nawa noman, Allah Ya taimake ni wata shekara sai gani na noma buhun masara 78. Hakan ya sa na ji ba na sha’awar aikin gwamnati. Sai na ci gaba ina noma ina bincike wato a kan al’amuran yau da kullum, kuma noman damina kawai nake yi . Da haka na sake komawa Jami’ar Jos a sashin Wasan Kwaikwayo da Sadarwa na yi digiri na biyu daga nan na sake kuma yin digiri na uku a Wasan Kwaikwayo da Bunkasa Ci Gaban Al’umma (Theater and Community Debelopment) saboda na kware wajen aikin al’umma a karkara, inda nake mayar da hankali a kan bangaren ci gaban jinsi da mata.
Kalubale
Gaskiya na fuskanci kalubale sosai domin kafin in yi karfi mijina ya rasu ya bar ni da yara, ina ta fadi tashin rayuwa ba aiki sai noma kuma da yake an fi sanin maza da noma babu mai taimaka min. Da haka har na kai inda nake yanzu. Irin aikin al’umma da nake yi ne ya daga ni domin na zaga duk garuruwan Najeriya saboda wannan aiki na al’umma (Community Work).
Nasara
Nasarar da na samu ba za ta misaltu ba domin aikace-aikacen da nake yi sun daga ni a idon duniya na samu daukaka sosai yadda ba ka tsammani, domin na san manyan mutane kuma na ziyarci kasashe masu yawa a duniya.
Burina a rayuwa
Burina shi ne in taimaka wa wanda bai da yadda zai yi a rayuwa ko wanda bai da hanyar dogaro da kai idan na taimaka musu a lokacin ina kara samun natsuwa a raina da kuma yin barci mai dadi saboda na gyara kusancina da Ubangiji.
Abin da ya sa ni sha’awar siyasa
Abin da ya sa ni sha’awar siyasa shi ne saboda ni ’yar kauye ce kuma garinmu ba hanya, ina son ganin na taimaka wa kauyenmu, shi ya sa a kullum ba ni da bukatar da ta wuce in zama kansila ko shugabar karamar hukuma kusa da al’ummata don in samu kusanci da gwamnati ta yadda zan ga garinmu ya shiga sahun garuruwan da suka ci gaba suke da hanya da ruwan sha da wutar lantarki da kuma asibiti na zamani.
Yadda na hadu da mijina
A lokacin ina jami’a muka hadu da shi
ina aji biyu shi kuma yana ajin karshe na gamawa a nan muka hadu har Allah Ya yi muka yi aure amma yanzu Allah Ya yi masa rasuwa.
Tufafi
Na fi sanya doguwar riga ta atamfa sannan in sanya gyale don ko kasashen wajen da nake zuwa riga da gyale za ka ganni da shi ba wani kaya daban ba.
Kungiyoyi
Ni mamba ce a Kungiyar Mata ’Yan Agajin Coci (Girls Bridge) tun ina karama har na girma ina kungiyoyin Red Cross da ta masu wasan kwakwayo ta Society of Theater Arts (SONTA) wacce kungiyarmu ce ta makaranta sannan ni mamba ce a Cibiyar Kwararrun Shugabanni ta Nigeria Institutes of Management (NIM). Na yi aiki da wata kungiya mai suna Published What You Pay kungiya ce da suke kula da yadda ake hako man fetur a Najeriya, ni ce wakiliyarsu a kasashen Yammacin Afirka. Na yi aiki da BBC Media Action da kuma Gidauniyar Bills da Melinda Gate.
Kasashen da na je
Kasashe da yawa, na je Ghana da Senegal da Guinea Conakry da Liberiya da Masar da Dubai da Turkiyya da Amurka da Ingila da Beljiyam da Afirka ta Kudu da Benin da Togo da Gambiya. Sannan na je Ibory Cost da Nijar da Mauritaniya da Zimbabwe da Mali da Burkina Faso da Cape Bade da sauransu.
Lambobin yabo
Na samu lambobin yabo da dama, domin tun ina jami’a na fara samun lamba ta wacce ta fi kowa yawan murmushi (Best Smiles) saboda gaskiya ni ban iya murtukewa ba. Na samu yabo daga kwamandanmu a lokacin muna hidimar kasa. Karamar Hukumar Enugu ma ta ba ni kyauta ta ’yar hidimar kasar da ta fi kwazo. Ma’aikatar Matasa ta Kas ma ta ba ni lambar yabo ta Mutum 12 da Suka fi Kwazo (Top 12), haka Uwargidan tsohon Shugaban Kasa Dame Patience Jonathan ta sa an ba ni lambar yabo a Yeshu’a International School of Theology a Ingila ta digirin girmawa a shekarar 2013 tun ban gama digirina na biyu ba.
Kwasa-kwasai
Na yi kwas a fannonin ilimi da gyaran tarbiyya (BCC) da kula da marayu da marasa galihu (OBC), na je kwas a NIM, na kuma yi kwas kan Nuna Afirka wani jerin shiga a dama wajen ilimi da bunkasar matasa kan dimokuradiyya. Kuma na je kwas din musaya a a Ghana, na yi kwas kan horar da mata ’yan siyasa, na yi kwas namata da sauyin shugabanci.
Abin da ya fi burge ni
Ina son mai taimako, domin ko ni ce na taimaki wani ina jin na burge kaina saboda taimako yana da kyau a rayuwa, kuma ko ban san ka ba idan da hali idan na taimaka maka ina jin dadi.
Yawan iyali
Ina da ’ya’ya bakwai da ’yan uwa wadanda su ma iyalaina ne.
Shawara ga iyaye
Ina bai wa iyaye shawarar su rika barin ’ya’yansu mata suna samun ilimin zamani domin ilimi yana da muhimmanci gare su. Saboda ni ma duk wadannan nasarori da na samu ba don albarkacin karatu ba da ba zan same su ba.
Shi kuma ilimi musamman ga ’ya mace yana da kyau domin ko wajen tarbiyyar yara za a gane ’ya’yan mace mai ilimi da na marar ilimi. Ban ce kada a bar namiji ya yi karatu ba amma dai a kula da na ’ya mace sosai.
Kamar iyayen da suke kin bai wa ’ya’ya mata ilimin suna barinsu suna talla, su sani fa wajen talla kasuwanni da tashohi waje ne mai hadarin gaske da zai yi saurin lalata tarbiyyar yara saboda irin mutanen da suke mu’amala a wajen.