Aikin agaji yana da matuqar amfani ga qasa – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Qasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce aikin agaji aiki ne da yake da amfani ga al’umma da gwamnati. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron atisaye da ’yan agajin qungiyar reshen […]

Aikin agaji yana da matuqar amfani ga qasa – Sheikh Jingir
Aikin agaji yana da matuqar amfani ga qasa – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Qasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce aikin agaji aiki ne da yake da amfani ga al’umma da gwamnati. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron atisaye da ’yan agajin qungiyar reshen Jihar Filato suka gudanar a garin Mista Ali da ke kusa da Jos.