Aikin dan majalisa ya wuce bayar da injin taliya – Aminu Tukur
dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi daga mazabar Lere-Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa Alhaji Muhammed Aminu Tukur ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa ba ana zaben dan majalisa ba ne don ya rika raba kyautar injin taliya ga mutane, domin aikin dan majalisa shi ne yin doka wadda za ta amfani al’umma baki […]
dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi daga mazabar Lere-Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa Alhaji Muhammed Aminu Tukur ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa ba ana zaben dan majalisa ba ne don ya rika raba kyautar injin taliya ga mutane, domin aikin dan majalisa shi ne yin doka wadda za ta amfani al’umma baki daya.
Alhaji AminuTukur ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi, inda ya ce shi ba ya kyautar injin taliya kuma ba ya ba da ragon suna, saboda ba don haka aka zabe shi dan majalisa ba, ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa ya gabatar da kudirin dokoki masu dimbin yawa da suka shafi mazabarsa ta Lere/Bula da jihar baki daya.
“Babu wanda ya zabe ni domin na ba shi tallafin kudi domin ya yi aikin gona da kiwo, kuma babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya na1999 ya ce in ba da kyautar injin taliya ko ragon suna ga mutanen mazabata.
Amma kuma ina ba da tallafi ta fuskar bunkasa ilimi da bunkasa kiwon lafiya kuma na ba da gudunmawar sama da Naira miliyan 10 ga mutanen mazabata duk da kowa ya san cewa ana fama da karancin kudi a kasar nan. Yanzu haka muna aikin tona bohul-bohul 41 domin wadata mutanen mazabar da ruwan sha, aikin na hadin gwiwa ne da Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara,” inji shi.
Ya ce saboda akidarsa a siyasa ce mutanen mazabar suka zabe shi a matsayin dan majalisa har sau biyu, inda ya ce zai yi wahala ka ga dillalan siyasa a kofar gidansa.
“Ni tsohon dan NEPU ne mai siyasar akida saboda haka ya kamata kowa ya kama sana’a domin ita ce mutucin mutum,” inji shi.