Aikin Fasaha: Anya yaron nan ba aljani ba ne?

Yaron nan yana ba ni mamaki matuka, Kamal Y. Iyantama, domin kuwa har ma na fara tunanin anya mutum ne shi kuwa, ba aljani ba?Hannunsa kaifin tsiya, kwakwalwarsa zafin tsiya. Ga shi marubucin kirkira, ga shi gwanin zayyana, ga shi kuma fasihin mawaki, duk shi kadai! A kullum zana mutane yake ba kaukautawa. Da zarar […]

Aikin Fasaha: Anya yaron nan ba aljani ba ne?
Aikin Fasaha: Anya yaron nan ba aljani ba ne?

Yaron nan yana ba ni mamaki matuka, Kamal Y. Iyantama, domin kuwa har ma na fara tunanin anya mutum ne shi kuwa, ba aljani ba?
Hannunsa kaifin tsiya, kwakwalwarsa zafin tsiya. Ga shi marubucin kirkira, ga shi gwanin zayyana, ga shi kuma fasihin mawaki, duk shi kadai! A kullum zana mutane yake ba kaukautawa. Da zarar ya dora fensir kan takarda, sai ka ga fuskar kyakkyawar yarinya ta fito radau, kamar ka ce keee, ta yi maka magana. Wannan fikira ta yi yawa!
A rayuwata, sau daya na taba ganinsa ido-da-ido, duk kuwa da cewa garinmu daya, Malumfashi. Na fara ganinsa ne a kwanakin baya, lokacin da ya kawo mani gaisuwar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyata, shi da hazikin marubuci, Malam Nasir G. Ahmad.
Barkanku, yanzu dai na gane cewa lallai mutum ne shi ba aljani ba. Na gane cewa dAN BAIWA NE SHI!
Yabawa da hazakarsa, shi ya sanya na rubuta masa baituka 11, kamar haka:

Ruwan wakokin yabon fasahar Kamal

Godiya ga Allah mai baiwa,
Shi ne Yai yi nufin ba kowa;

Baiwa daidai da kimar kowa,
Ya ba Kamalu yaro dan baiwa.

Yaron akwai fikira tattarawa,
Ga zane-zane kullum zanawa.

A  waka kullum yana rerawa,
Katib yake aikinsa rubutawa.

Halittun Ubangiji siffantawa,
Hikima Kamal yana zayyanawa.

Giwa, zakin dawa har da barewa,
Aikin ajabi Allah na yassarewa.

Jirgi mota babur abin sarrafawa,
Samfurin gidaje, ga zanen fulawa,

Dandalin gwanin kaye, shakatawa.
Kamal ya wassafa don gwanintawa

Sarakuna, shugabanni, malamawa,
Har ni Bashir Yahuza yana zanawa.

Nasir GAhmad ko ka ga dan baiwa?
Ka isar mini da godiyata jimlatawa.

Addu’a nake kullum Allah kara budawa,
Kamal ka sam nasara nan har lahirawa.
                         ***
Baitukana na tsayawa nan sai kuma shi ma Sada Bn Suleiman Usman ya zo da ta’aliki, yana cewa:

Yabo na kyauta, tukuitawa
Kamalu zane, zam godewa.

Kai Rabbu baiwa yai damkawa
Yo godiya garai, ze karowa.

Kai Bashir, Malami nawa
Dadin zuma, shi ka sa lashewa.

Duk dan halak, zai halastawa
Gaishe ka nai, hada karawa.

dabi’un Kamal, mutuntawa
Raini ga babba, tiris be yowa.

kanne garai, yana tafiyarwa
Fada ya kama, ze nusarwa.
                 ***
Shi ma Kamal Y. Iyantama, wanda aka yi baitukan farko gare shi, sai ya biyo baya da nasa ta’alikin, yana cewa:

Amin summa amin nai godewa,
Allah saka ma yai yo karawa.

Addu’ar da kake min ba gocewa,
Rabbi Sarki Allah zai amsawa.

Zanen da nike ba kakkautawa,
Wane inji mai kyakkerawa.

Kuma hannun hagune lefty nawa,
Da shi nike using in zanawa.

Fensiri da biro da takardawa,
Ko fenti da kala in yi hadawa.
Na san Allah ne yai horewa,
Kullum a Sallah sai nai godewa.

Shi ya sa abin ba ya jinkirtawa,
Hikima da fasahar na kutsowa.
***
Kamal na aje alkalaminsa, sai Ukhasha Abuu Albaniy ya maye gurbinsa, yana cewa:

Tabbas Katsinawa kui godewa,
Rabbil izzati mai bayarwa,

Wanda Ya ba ku mutane manya,
Irin su Bashir mai Aminiya,

Tare da Iyantama mai zanawa,
Rabbi Ka kare mani su duka jumla.
***

Daga nan sai shi kuma Auwal Yobo ya dauki nasa, ya rubuta cewa:

Ka ji fasihai na bayyanawa,
Hakimar da rabbi yai azawa.

Bisa kan wannan dan baiwa,
Wato Kamal da yake zanawa.

Hazikan da suke jajircewa,
Sun daidaita babu gazawa.

Ya rabbi ka kara budewa,
kwakwalwar wannan dan baiwa.
***

Shi ma Nasir G. Ahmad, ba a bar shi a baya ba, ya tofa nasa albarkacin bakin da wadannan baitocin:

Tabbas kai batu Malam Bashiru,
A kan hikimar Kamalu abar yabawa.

dan baiwa abin a nuna ko’ina ne,
Mutafanninu ne fasihin nadirawa.

Wannan zane da yai ya nuna tabbas,
Gwani ne shi muna karin yabawa.
***

Salman Paris Muntari Kallamu, a nasa ta’alikin, cewa yake:

 A gaida Kamalu dan baiwa,
Gwani ne shi a zanawa.

In ya so zane ya tsarawa,
Yanzu sai ka ga ya yi karewa.

Kan batun wakar rubutawa,
Yanzu tsaf sai yay yi rairawa.

kirkira labari jerawa,
Yanzu sai ka ga yai rubutawa.
***

A lokacin da Salman Parisi ya dakata, sai shi fasihin, Kamal Y. Iyantama ya jona nasa ta’alikin, yana cewa:

Ku ji Salman dan kanina,
Baitukanka gwanin biyawa.

Sai naj ji kamar fa ni ne,
Lokacin wakar Arewa.

Ga shi dai ka yo su saiti,
Wajibi na yi jinjinawa.

Ka ga ni ma sai in koya,
A gare ka na zam iyawa.