Aikin gina sabuwar kasuwar Ogere ya kankama
Gwamnatin Jihar Ogun, ta fara aikin share makeken dajin Ogere, domin gina sabuwar kasuwar duniya da za ta maye gurbin kasuwar Mil 12 da karar shanu ta Isheri da Gwamnatin Jihar Legas ta fara yunkurin tashinsu daga inda suke a yanzu.An girke manyan motocin katafila da tifofin kwasar kasa tare da wasu jami’ai da gwamnati […]
Gwamnatin Jihar Ogun, ta fara aikin share makeken dajin Ogere, domin gina sabuwar kasuwar duniya da za ta maye gurbin kasuwar Mil 12 da karar shanu ta Isheri da Gwamnatin Jihar Legas ta fara yunkurin tashinsu daga inda suke a yanzu.
An girke manyan motocin katafila da tifofin kwasar kasa tare da wasu jami’ai da gwamnati ta aika domin lura da irin ayyukan da ake yi a cikin wannan makeken daji mai nisan kilomita 2 a gabas da yamma da kudu da arewa.
Kwanan baya ne Gwamnatin Jihar Legas ta rufe kasuwar Mil 12 a dalilin rikicin kabilanci da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi, wanda ya sanya daruruwan ’yan kasuwa suka fara tarewa a sabuwar kasuwar ta Ogere da ke kan hanyar Ibadan zuwa Legas. Da yawa daga cikin wadannan ’yan kasuwa sun koma bayan umarnin bude kasuwar na wucin gadi da Gwamnatin Legas ta bayar.
Wakilinmu da ya ziyarci sabuwar kasuwar ta Ogere, ya gane wa idanunsa irin aikin share wannan daji da motocin katafila da tifofi suke yi ba kaukautawa a gaban jami’ai masu sanya idanu da Gwamna Ibikunle Amosun na Jihar Ogun ya aika domin fara aikin gina sabuwar kasuwar. A gefe daya, akwai wasu wakilai maza da mata da fadar Ologere na Ogere, Oba Oladele Ogungbade ta aika a karkashin Cif Olumide Ogunlana da jagorar mata ’yan kasuwa Iyaloja, Uwargida Olorunfumi Odutona da suka shimfida tabarmi suka yi zaman dirshan a wani kebabben wuri a wuraren da aka fara sharewa domin amfanin ’yan kasuwa.
Bayan zagayawa da wakilinmu zuwa cikin sabuwar kasuwar, Sarkin Hausawan Ogere, Alhaji Abdullahi Abubakar Saminaka, godiya ya yi ga Allah ne “wanda Ya nufi Gwamna Ibikunle Amosun da ya tausaya wa al’ummarmu ’yan Arewa wajen daukar matakin share mana hawaye ta fannin amincewarsa da bayar da umarnin gina mana sabuwar kasuwa. Duka abun da uba yake yi wa dansa, Gwamnan ya yi mana wajen gina wannan kasuwa ta duniya mallakar ’yan Najeriya; wacce aka tsara ta sashe sashe da zai samar wa kowane bangare na ’yan kasuwa matsunguni ba tare da an cakuda su ba. Akwai makeken fili da aka tanadar a matsayin garejin tsayuwar kanana da manyan motoci tare da fili na musamman domin gina ofishin ’yan sanda domin kare lafiyar jama’a da dukiyarsu.”
Ya kara da cewa: “Mun riga mun dauki matakin wayar da kan mutanenmu a game da irin hadin kai da goyon baya da za mu bayar ga Gwamna Ibikunle Amosun domin cin ma burinsa musamman wajen samo hanyar dinke barakar bambancin addini ko kabila da zai kyautata zamantakewa a tsakanin al’ummomi daban-daban da za su hadu a cikin wannan kasuwa. Kuma mun fara kafa kwamitoci musamnman kwamitin da ya shafi tsaron lafiya mai dorewa. Akwai masu unguwanni da shugabannin kungiyoyi da muka nada da muke yin kira ga jama’armu su rika mika koke-kokensu gare su ba tare da yankewa kansu hukumci ba.”
A game da ’yan kasuwar da suka fara komawa kasuwar Mil 12, sai Sarkin Hausawan na Ogere ya ce za su sake dawowa domin Gwamnatin Legas ta bude kasuwar na wucin gadi ne. Ya bayyana cewa yanzu haka ma fadarsa ta fara tattaunawa da shugabannin kasuwar Mil 12 da karar shanu ta Isheri domin tafiya da murya daya a kan wannan sabuwar kasuwa.