Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (3)
Siffa Hajji: Rukuni na farko (Ihrami) Ihrami: Tun farko sai mutum ya kudurci yin Hajji a cikin zuciyarsa ya ce: “Na yi niyyar yin Hajjin Dakin Allah Mai alfarma da ke Makka. Wato dai a takaice shi ne ya dauka a ransa cewa ya dabaibiye kansa da dukan sha’anunnukan Hajji na aikatawa da na bari. […]
Siffa Hajji: Rukuni na farko (Ihrami)
Ihrami:
Tun farko sai mutum ya kudurci yin Hajji a cikin zuciyarsa ya ce: “Na yi niyyar yin Hajjin Dakin Allah Mai alfarma da ke Makka. Wato dai a takaice shi ne ya dauka a ransa cewa ya dabaibiye kansa da dukan sha’anunnukan Hajji na aikatawa da na bari.
Mikati:
Mikati shi ne wurin da ake kudirta niyyar Hajji. Jama’ar kowace nahiya suna da nasu mikati daban-daban. Yin niyya a mikati wajibi ne. Akwai wuri biyar daban-daban na yin niyya a kan ta jihar da mutum ya bullo wa Makka. Ga sunayen wuraren:
- Juhfa: Rabiga shi ne garin a yanzu Juhfa ta zama kango. Juhfa wani gari ne, mutanen da ke kudirta niyya a nan su ne wadanda suka fito ta wajen kasashen Sham (Siriya) da Masar da Turai da mutanen yammacin Makka kamar Sudan da Najeriya da kasashen yammacin Afirka. Idan kuwa mutumin da ya fito daga dayan wadannan kasashen ya biyo ta cikin tekun Maliya (Bahar Maliya) ne, to zai yi niyya daga nan cikin tekun a lokacin da jirginsu ya kawo daura da ita Juhfar. Mutanen Siriya da Masar da Sudan da Najeriya da Chadi da Kamaru. Nisan kilomita186 zuwa Makka
- Zul-Hulaifa: Zul-Hulaifa wuri ne tsakanin Madina zuwa Makka, wadanda suke kudirta niyya a nan su ne mutanen Madina. Haka duk mutumin wata nahiya da ya biyo ta Madina, to shi ma a nan Zul-Hulaifa zai yi niyya. Mutanen Madina nisan kilomita13 sai nisan kilomita428 zuwa Madina kafin Makkah
- Zatul-Irak: Zatul-Iraki wani kangon gari ne, wadanda suke kudirta niyya a wannan wuri su ne mutanen kasar Irak da Farisa (Iran) da Khurasan da Sauran gabasawa.
- Yalamlamu: Yalamlamu wani dutse ne da mutanen da suka fito daga wajen kasar Yemen da Indiya da Pakistan da sauran makwabtansu suke yin niyya a nan wurin.
- Karnu-Manazil: Karnu-Manazil shi ma wani dutse ne, mutanen da suka fito ta wajen Najdu su suke yin Ihrami a nan.
Wanda yake zaune a cikin garin Makka zai yi niyyar Hajji a kowane wuri ya ga dama a cikn garin. Sai dai an fi son ya yi niyyar a cikin Masallacin Ka’aba. Mutanen Najad, gabashin Irak da Iran na da nisan kilomita 78 zuwa Makkah.
Sunnonin da Mustahabban Ihrami: Da zarar maniyyaci ya isa mikatin da aka ce zai yi Ihrami a wurinsa to, gabannin ya yi niyyar Hajji, Sunnah ce gare shi ya yi wanka tukunna. Zai yi wankan nan kamar yadda ake yin na janaba, sai dai ga niyya kadai suka bambanta. Don wanka goma sha biyu ne, guda hudu na wajibi.
Wajibai su ne:
- Wankan Janaba.
- Wankan Haila
- Wankan Jinin Biki
- Sai wankan da kafiri ke yi idan ya shiga Musulunci.
Wanka na sunnoni guda hudu:
- Wankan zuwa Juma’a.
- Wankan Haramar Hajji.
- Wankan Gawa
- Wankan Tsayuwar Arfa
Sai na Mustahabbi guda hudu:
- Wankan Ranar Idi.
- Wankan shiga garin Makka ga matafiyi.
- Wankan da mutum zai yi wa kansa bayan ya kare yi wa gawa wanka.
- Wankan daukewar jinin Istihala.
Wato wani jinin rashin lafiya ne da ya kan zo wa mata, ba a lokacin haila ba, kuma ba a lokacin jinin biki ba.
Wadannan su ne wanka goma sha biyu dukkansu yin su iri daya ne, niyya kawai suka bambanta.
Shi wannan wanka ana kiransa wankan Ihrami. Mace ko da tana haila ko jinin biki za ta yi wannan wanka. Yin hadaya ko sadaka ba zai kama mutum ba idan ya bar wannan wanka. Kuma mustahabbi ne wato an so, ga mai Hajji kafin ya yi wannan wanka ya yanke farcensa ya aske gashin mararsa, kuma ya saisaye gashin bakinsa. Amma ba zai aske gashin kansa ba, domin gashin ya zamar masa kariya ga zafi ko sanyi a lokacin aikin Hajji.
Bayan wannan idan maniyyaci namiji ne zai tube tufafin jikinsa na al’ada tun gabanin ihrami, ya sanya tufafi irin na yin Hajji. Wato su ne gyauto da mayafi da takalma fade. Ya daura gyauton, ya laga mayafin. Wadannan kaya kadai zai saka ko hula babu yin irin wannan shiga Sunnah ce.
Bayan wannan sai mutun ya yi Sallah gabannin kudirta ihraminsa. Wato zai yi Sallah ta farilla idan lokacin kudirta niyyarsa ya dace da lokacin wata Sallah ta farilla. Idan kuwa bai dace ba, to sai ya yi Sallah ta nafila raka’a biyu.
Da kare Sallar nan sai mutum ya kudirta niyyar yin Hajjinsa. Idan kuwa Umara ce yake son ya fara aikatawa, to sai ya kudirta niyyarta ita kadai. Zan ba da bayanin yadda Umara take nan gaba. Idan kuma yana bukatar ya gwama Umara da Hajji ne, to sai ya kudirta niyyarsu baki daya a hade.
Da kare kudirta niyya sai mutum ya kama hanyar isa Makka, ya fara yin Talbiyya, Talbiyya ita ce fadar:
“Labbaikallahumma labbaik. Labbaika la sharikalaka labbaik, Innal hamda wan ni’amata laka wal mulk la sharikalak.”
Ma’anarta ita ce: ‘Na karba kiranKa ya Allah! Na karba kiranKa na karba kiranKa, babu abokin tarayya gare Ka, na karba kiranKa, Hakika yabo da ni’ima da mulki duk sun tabbata gare Ka. Babu abokin tarayya gare Ka.’
Yin Talbiya wajibi ne, don haka idan mutum ya bar ta dungum zai yi hadaya. Amma zamowarta hade da niyya shi Sunna ne, wato da yin Ihrami sai a fara yin ta a bayyane da sauti matsakaici, amma mace za ta fade ta a asirce yadda ita kadai za ta iya jin abin da take fada. Mutum zai ci gaba da yin Talbiyya a bayan kowace Sallah da kuma yayin da zai hau wani tudu, ko yayin da zai gangaro a cikin kwari da kuma lokacin da ya gamu da wasu ayari. Idan ya isa Makka zai daina yin Talbiyya, sai bayan ya yi Dawafi da Sa’ayi. Sa’an nan ya koma ga yin ta lokaci- lokaci, har zuwa faduwar rana a Ranar Arfa, wato 9 ga Zul-Hajji. Sa’an nan ya daina yin ta a ranar Sallah, wato 10 ga Zul-Hajji da hantsi, bayan ya jefi (Jamratul-Akaba) (Shaidan).
Idan mutum ya kusa isa Makka, mustahabbi ne, wato an so, ya yi wankan shiga garin Makka. An fi son ya yi wankan nan a wurin da ake kira Zu-Duwan, ga mai haila ko jinin biki ba za ta yi wannan wanka ba; domin ana yins a ne don shiga masallaci. Mustahabbi ne mai Hajji ya shiga birnin Makka ta kofar Hajjinsa duka-duka, ya yi niyyar komawa gida, to, an so ya bar garin Makka ta kofar da ake kira Kudan. Babu wani laifi a kan mutum idan ya bar wadannan mustahabbai.