Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (6)

Siffar Hajj a takaice Mai Hajji idan ya zo yin niyyar Hajji, wato Ihrami, zai fara da yin wanka. Idan ya kare wanka ya sa tufafin Hajji, ya taso wa Makka, yana talbiyya. Idan ya kawo gab da Makka, sai ya yi wankan shiga Makka. Da isowarsa Makka, sai ya je Masallaci ya yi Dawaful-Kudumi […]

Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (6)
Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (6)

Siffar Hajj a takaice

Mai Hajji idan ya zo yin niyyar Hajji, wato Ihrami, zai fara da yin wanka. Idan ya kare wanka ya sa tufafin Hajji, ya taso wa Makka, yana talbiyya. Idan ya kawo gab da Makka, sai ya yi wankan shiga Makka. Da isowarsa Makka, sai ya je Masallaci ya yi Dawaful-Kudumi na wajibi, ya je ya yi Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa.

Idan ranar takwas ga Zul-Hajji ta zo sai ya je Mina ya kwana. Kashegari, wato ranar tara ga Zul-Hajji, sai ya je Arfa ya tsaya a Arfa har bayan faduwar rana. Zai yi wankan tsayuwar Arfa tun da fari bayan rana ta fadi duhu ya dan shigo, sai ya taso wa Muzdalifa, ya kwana a nan kashegari, wato ran 10 ga Zul-Hajji sai ya yi Sallar Asuba a nan Muzdalifa, ya tsaya ya yi addu’a a Mash’arul Haram. sa’annan ya nufo Mina.

Da isowarsa Mina sai ya je ya jefi Jamratul Akaba da dutse bakwai. Ya yi aski ko saisaye ya yanka dabbarsa ta hadaya. Daga nan sai ya taso wa Makka don yin Dawaful Ifala. Idan ya kare shi sai ya dawo Mina ya kwana biyu ko uku, don jifar jamrorin nan guda uku. A ranar 13 ga Zul-Hajji, sai ya komo Makka. Idan ranar barinsa Makka ta zo, sai ya je Masallaci ya yi Dawafin Ban-Kwana da Ka’aba. Shi ke nan.

Umara: Umara wata ibada ce mai kama da Hajji. Ana yi mata Ihrami da Dawafi da Sa’ayi kadai. Hukuncin yinta Sunnah ce a kan kowane Musulmi ko Musulma sau daya tak a cikin rayuwarsu ta duniya. Idan mutum zai yi Umara, sai ya fita bayan garin Makka, har ya isa Hillu, sa’annan ya kudurta niyyar yin Umara Sunnah, akwai wata iyaka wadda ta gewaye garin Makka a wata jiha nisan iyakar nan ya kai kamar mil goma, a wata jiha kuwa ya kasa haka. To abin da ke cikin iyakar nan shi ake kira Harami abin da ke wajen iyakar nan kuwa shi ake kira Hillu. Ma’anar Harami shi ne cewa zub-da-jinin mutum ko dabba ta farauta a cikin wannan wurin ya haramta. Amma ana iya kashe dabba ko kwaro mai cutarwa a cikin wannan wuri. A cikin Hillu kuwa yin farauta ya halatta ta kowace irin dabba. To tilas ne mai yin Umara ya fita ya je har Hillu don yin niyya. Wuri mafi kusa da Hillu shi ne Masallacin A’ishatu, nisansa daga Ka’aba mil hudu ne. ya sa tufafi irin na yin Hajji. Ya zo ya yi Dawafi ga Ka’aba kewayo bakwai, ya yi Sallah raka’a biyu a Mukamu Ibrahim. Sa’annan ya je Safa da Marwa don yin Sa’ayi shudi bakwai. Sa’annan ya yi aski ko saisaye. Shi ke nan Umararsa ta cika. Ana iya yin Umara a cikin kowane lokaci na shekara. Rukunan Umara uku ne, Su ne Ihrami da Dawafi da Sa’ayi. Yin aski ko saisaye a bayan kare ta wajibi ne za a yi hadaya domin barinsa.

Tamattu’i: Yin Umara a cikin kwanakin Hajji sa’annan mutum ya yi Hajji kuma a cikin wannan shekarar, shi a ke kira Tamattu’i. Kwanakin Hajji su ne daga 1 ga watan Shawwal har zuwa karshen rana ta 9 ga watan Zul-Hajji.

Yadda ake yin Tamattu’i shi ne mutum idan ya isa Saudiyya sai ya yi niyya daga mikatinsa, wanda yake zaune ko ya sauka a Makka sai ya yi niyya daga Hillu. Ya je ya kewaya Ka’aba sau bakwai, ya yi Sallah a Makamu Ibrahim. Ya je Safa da Marwa ya yi Sa’ayi a tsakaninsu sau bakwai. Sa’annan ya saisaye gashin kansa. Ba zai yi aski ba, domin ana son ya rage gashin da zai kare masa zafin rana ko sanyi a lokacin aikin Hajjinsa. Da kare Sa’ayinsa da saisayensa, shi ke nan ya gama aikin Umarar Tamattu’i, sai ya sa tufafinsa irin na al’ada ya koma zamansa irin na marasa Ihrami a kansu. Babu wani abu saboda ya haramta a kansa kuma shi ke nan sai ranar takwas ga Zul-Hajji ta zo, sai ya tafi zuwa Mina a ran nan. Ya je su Arfa ya dawo su Muzdalifa su Mina. A ran 10 ga watan Zul-Hajji ya je Ka’aba ya yi Dawaful Ifala a bayansa kuma ya yi Sa’ayi na farilla, wato rukuni. A da can bai yi Sa’ayi na Hajji ba, don Umara ce kadai ya yi.

Kirani: Kirani shi ne mutum ya yi ayyukan Hajji da na Umara a hade a kunshe. Wato shi ne aikin Umara a shigar da shi a cikin na Hajji. Wato idan mutum zai yi Dawafi ko Sa’ayi sai ya yi su da niyyar zaman ko wannensu a kan na Umara ne da Hajji gaba daya.

Yadda mutum zai yi kirani shi ne ya yi niyya ya ce: “Na yi niyyar yin Umara da Hajji a hade.” Zai fara da ambaton Umara sa’annan Hajji. Shi ke nan sai ya ci gaba da aikinsa kamar Hajji ne kadai yake yi haka kuma idan mutum ya yi niyyar yin Tamattu’i wato Umara a rabe, daga baya yana iya juyar da aiki ya zama Kirani, matukar dai bai kare Dawafin Umarar nan ba. Wato sai ya kara a cikin niyyarsa, ya ce: “Na dada Hajji a kan wannan Umara” daga nan sai hukuncinsa ya komo kamar na mai Kirani. Wanda ya yi Kirani, zai yi hadaya sadaka.

Wato kun ji hanyoyin yin Hajji guda uku. Hanya ta daya ita ce Ifradi. Wato kadaita Hajji shi kadai. Sa’annan a yi Umara daban ba a cikin kwanakin Hajji ba, kamar mutum ya yi ta da kamar kwana biyar a bayan Sallah babba. Hanya ta biyu ita ce Kirani. Hanya ta uku ita ce Tamattu’i. a cikin wadannan hanyoyi uku, Ifradi ya fi su lada, sa’annan Kirani, sa’annan Tamattu’i.

Hadaya: Mun ambaci laifuffuka da dama a can baya wadanda za a yi hadaya dominsu. To yadda mutum zai yi wannan hadaya shi ne ya yanka dabba sadaka. An ba mai yin hadaya zabi a kan irin dabbar da zai yanka ko ta zamo daga cikin rakuma ko shanu ko tumaki ko awaki. Amma wacce take da aukin nama ake bukata a wajen hadaya, an fi son a yi hadaya da rakuma, sa’annan shanu, sa’annan tumaki sa’annan awaki. A wajen layya lada akasin haka aka fi so, daya da ke dadin nama aka fi bukata sai dai a wajen layya an fi son tumaki fiye da awaki.

Amfanin yi wa dabbar hadaya ish’ari ko rataya shi ne don matalauta su fahimci wannan dabba tasu ce domin su bi ta zuwa mayanka. Dalili na biyu kuwa shi ne idan ta bata sai wanda ya tsince ta ya koro ta zuwa mayanka a Mina, ba sai ya yi cigiyar mai ita ba.

Ana yanka dabbar hadaya a Mina idan an samu wadannan sharudda:

  1. Idan an tsaya da dabbar nan a Arfa
  2. Idan an yanka ta a cikin kwanakin zaman Mina, wato ranar Sallah da yini biyu na bayan Sallah.
  3. Idan hadayar an yi ta ce game da aikin Hajji, wato ba don laifin Umara kadai ba ce, kuma ba fidiya ba ce, ba kuma sakamakon farauta ba ce.

Idan an rasa dayan wannan sharudda uku, to wajibi ne a yanka ta a Makka. Sai dai wajibi ne a ja dabbar hadaya ta kowane hali a shiga Hillu da ita, sa’annan a ratso Harami, kafin a kai ta mayanka

Mutum ko da bai yi laifi ba ko guda a cikin Hajinsa, an so ya yi hadaya ta jin dadin rai, sadaka.

Ana yanka hadaya ce domin a ba da komai na jikinta sadaka ga fakirai. Amma ya halatta ga mai yin hadaya ya ci naman hadayarsa kuma har ya diba ya yi guzuri daga ciki. Kuma ya halatta gare shi ya diba ya bayar kyauta. Wato dai ya halatta ya ci, ya yi sadaka, ya yi kyauta da namanta. Yana iya yin sadaka da shi dukkansa. Amma idan har mutum ya yi alwashi ga Allah cewa zai yanka hadayar nan domin miskinai ko fakirai kadai to bai halatta kuma gare shi ya ci komai daga cikinta ba. Don haka da ya yanka ta sai kawai ya janye jikinsa, matalauta su dauki abarsu.

Dabbar da za ta isa yin hadaya ko fidiya, sharuddanta daidai suke da dabbar Layya.

Ga wasu laifuffuka da suke wajabta yin hadaya:

  1. Yin Ihrami bayan mutum ya ketare Mikati.
  2. Jinkirta fara yin Talbiyya bayan mutum ya kulla Ihrami.
  3. Barin Dawaful Kudumi
  4. Barin tsayuwar rana ta Arfa
  5. Barin sauka Muzdalifa da dare
  6. Barin yin jifa
  7. Barin kwana a Mina
  8. Barin yin aski ko saisaye, ko jinkirta yin dayansu har mutum ya dawo gida
  9. Yin ayyukan Hajji, kamar Dawafi da za a yi a kan dabba ko a dauke ga lafiyayye. Sai fa idan ya sake maimaita ainihin aikin nan a kan kafafunsa,
  10. Yin Tamattu’i
  11. Yin Kirani
  12. Mutum yana iya goya Hajji a kan Umara. Wato kamar mutum ya yi Ihrami da Umara kadai, sai kuma daga baya ya shiga da Ihramin Hajji a kan na Umara, ya zamo mai Kirani yana kuwa iya goya Hajjin na ko da kuwa ya yi nisa da aikin Umrarsa. Misali kamar ya yi Sa’ayi ba abin da ya rage sai yin aski. To wanda ya yi irin wannan ribanye, haramun ne a gare shi ya yi aski bayan kare Umrarsa. Zai dakata ne har ayyukan Hajji su kare, sa’annan ya yi aski guda domin su duka. Amma duk da haka nan zai yi hadaya domin jinkirta askin nan na Umara. Idan kuwa ya ki jinkirta shi wato ya yi wa Umara askinta, to zai yi hadaya game da fidiya don ya yi aski a cikin Hajji.

Fidiya (Fansa) Fidiya tana wajaba a kan mutum idan ya yi wani abu na jin dadi ga jikinsa ko ya gusar da wata ’yar cuta daga jikinsa kamar dauda ko kwaro. An ba mutum zabi a kan ya yi daya daga cikin abubuwan nan uku:

  1. Ko dai ya yanka dabba sadaka, wato zai yanka akuya ko rago ko saniya ko rakumi, duk abubuwan da aka shardanta ga dabbar Layya, irinsu ne aka shardanta ga dabbar Fidiya. Mutum zai yanka dabbar Fidiya a lokacin duk da ya ga dama, kuma a wurin duk da ya ga dama, ko da garinsu ne, amma idan mutum ya yi niyyar Hadaya da ita wannan dabbar ta Fidiya, ko ya yi mata ish’ari ko rataya to hukumcinta ya zama kamar na Hadaya, Saboda haka za a yanka ta a Mina ko a Makka.
  2. Ko kuwa ya yi azumin kwana uku a inda yake so. Idan ya ga dama yana iya yinsu a Makka ko a cikin Kwanakin Mina, ko kuwa a garinsu.

Hafna: Idan laifin da ke wajabta da yin Fidiya a kan mai Hajji ya zama dan kadan ne kwarai, to sai a ba da Hafna daya tak, Hafna ita ce cikin tafi daya na abinci. Wato mutum ya sa hannunsa daya a cikin kwandon hatsi ya kamfato. Ko ya tara hannunsa daya a bude, a zuba hatsi a cikinsa har ya cika. Za a ba da wannan Hafna sadaka ga miskini.

Za a iya tuntubar Imam Ahmad Adam Kutubi (SP) ta 08036095723