Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (7)
Abubuwan da aka hana a Hajji An haramta wa namiji mai yin Hajji ko Umara ya saka tufa gewayayyiya a jikinsa, kamar riga ko wando ko hula ko rawani ko yafa alkyabba ko takalmi wuffi ko safa ko zobe. Idan ya saka dayan wadannan zai yi fidiya. Sai fa idan sakawar ba ta yi tsawo […]
Abubuwan da aka hana a Hajji
An haramta wa namiji mai yin Hajji ko Umara ya saka tufa gewayayyiya a jikinsa, kamar riga ko wando ko hula ko rawani ko yafa alkyabba ko takalmi wuffi ko safa ko zobe. Idan ya saka dayan wadannan zai yi fidiya. Sai fa idan sakawar ba ta yi tsawo ba kamar ya dan gwada ne. Haka kuma mace idan ta rufe hannuwanta da safar hannu, ko ta rufe fuskarta kaf za ta yi fidiya.
Haramun ne ga namiji ya lullube kansa da wani abu mai shafar kansa. Idan ya yi haka zai yi fidiya. Idan a cikin barci ne ya lullube kansa da rashin sani babu komai amma da zarar ya farka sai ya kware tufar daga kansa. Ya halatta ga mai Hajji ya tsare kansa daga zafi ko sanyi ko ruwan sama ko iska da wani abu wanda ba zai taba kansa ba kamar lema. Amma ya halatta ga mai Hajji ya dauki kaya a bisa kansa idan daukar ta zama tilas, ko kuwa dako yake yi don ya ci abinci.
Farauta
Ya haramta a kan kowane mai Hajji da wanda ba mai Hajji ba ya kashe wata dabba ta daji a cikin Haramin Makka a cikin kowane lokaci na shekara. Haka ya haramta a kan mai Hajji kadai ya kashe wata dabba ta daji a cikin Hillu.
Haramin Makka wani fili ne wanda ya gewaye garin Makka daga kowace jiha. Annabi Ibrahim (AS) shi ne wanda ya fara kafa iyaka a kan gafensa. Kuma Annabi Muhammadu (SAW) ya sabunta fidda iyakafr nan ta Harami dajin da bai shigo cikin Harami ba shi a ke kira Hillu. Ga nisan iyakar Harami daga Ka’aba. Daga Arewa maso Yamma wato zuwa Tan’imi inda Masallacin A’isha (RA) yake, wato inda mutane galiban suke kudirta Ihramin Umara. Daga Jihar Arewa maso Gabas kuma daga Gabas kuwa wato wajen Arafa daga Kudu daga Yamma kuwa wato wajen Jidda wato daidai inda Hudaibiyya take.
Ya haramta a kashe dabbar daji a cikin Harami, ko kuma cikin Hillu idan mutum mai Hajji ne. Kamar yadda aka haramta kashe ta haka kuma ya haramta a aikata wani abu a kanta wanda zai yi sanadin mutuwarta, kamar a fige gashinta, ko a jefa ta rami. Haka kuma yi mata mummunan rauni wanda ake zaton zai hallaka ta, kamar kashe ta yake.
Sakamakon farauta
Idan mutum ya farauci irin dabbar da aka hana kashewa ta hanyar harbinta, ko saka mata tarko ko tura mata karen farauta, to idan tana da rai wanda za ta iya rayuwa da shi ya wajaba a sake ta ta tafi abinta idan kuwa ya yanka ta ko kuwa ta mutu to zai biya sakamakonta. A wajen biyan sakamako an ba mutum zabi ya yi daya daga cikin abubuwan nan uku.
- Ko dai ya ba da dabba ta gida hadaya, sadaka wadda ta yi kama da dabbar nan ta daji a wajen kimarta da kuma kamannin siffofinta. Hukuncin wurin da za a yanke wannan dabba ta sakamakon farauta kamar hukuncin dabbar hadaya yake.
- Ko kuwa mutum ya ba da abinci ga miskinai gwargwadon kimar dabban nan ta daji da ya kashe. A wajen kimanta za a kimanta da yawan abincin da za a iya musanya ta da shi wato ba da kudin da za a iya sayenta da shi ba. Za a kula da kimarta a halin tana mai rai, kuma babba za a kuma kula a kimanta da wurin da ta hallaka to idan an gane kimarta ta abinci, sai ya ba kowane miskini mudu daya.
- Ko kuma mutum ya yi azumi a matsayin ba da abinci, kowane mudu daya za a yi masa azumi daya cikakke. Mutum zai yi azumin nan duk wurin da ya ga dama.
Dabbar daji wadda ba ta da makamanciya, ko wadda ta yi kama da ita daga cikin dabbobin gida to abin da za a fitar mata shi ne abinci ko azumi. Ga kimar dabbobin daji bisa ga dangane ga dabbobin gida, wato sakamakon da mutum zai bayar:
Dabbar daji da madadinta ta gida Giwa -Rakumin Tulkumami
Jimina- Rakumi
Bauna – Saniya
Jakin Daji – Saniya
Barewa – Saniya
Kura – Akuya ko tunkiya
Yanyawa – Akuya ko tunkiya
Tantabarar Harami – Akuya ko tunkiya
Kurciyar Harami – Akuya ko tunkiya
Damo – Kima ta abinci ko azumi
Zomo – Kima ta abinci ko azumi
Kurege – Kima ta abinci ko azumi
Tsuntsaye – Kima ta abinci ko azumi
Tantabarar Hillu – Kima ta abinci ko azumi Kwai – Ushurin kimar uwar
Tayi – Ushurin Kimar uwar fara daya
Hafna – Tafi daya na abinci
Alkalai
To, ko da yake an ba da kwatancin dabbobin gida wadanda za a fitar a matsayin dabbobin daji, duk da haka wajibi ne mutum ya je wurin wadansu mahukunta biyu su gaya masa abin da zai bayar. Aikin wadannan mahukunta biyu shari’a ce sosai ba fatawa ta neman ra’ayi ba ce za su ce ga misali. A matsayin dabba iri kaza wadda ka kashe mun hukunta maka a kanka ka ba da dabba iri kaza hadaya ko ka ba da mudu kaza ko ka yi azumi kaza.
Idan mutum ya fidda sakamakon dabbar farauta, ba da an hukunta masa abin da zai bayar ba, sakamakon bai yi ba wajibi ne ya sake yin abin da aka hukunta masa. Mahukuntan nan wajibi ne su zamo biyu ’ya’ya ba bayi ba, baligai, adalai, masana kimar dabbobin daji.
A wajen yin kima za su kula da abubuwa uku: su ne shekarun haihuwa na dabbar daji da kibarta ko ranarta. Don haka za su gaya wa mutun ya ba da dabbar gida kaza, mai kiba ko ramamma. Amma ba za su kula da karancin dabbar ba ko girmanta ko lafiyarta ko kyanta. Wadannan abubuwa hudu da su da rashinsu duka daya tunda ita wannan dabbar ta farauta mushe ce, bai halatta a ci ta ba.
Tantabara da kurciya na cikin Harami ba su bukatar a hukunta wa mutm abin da zai fitar. Domin shari’a ta riga ta tsananta sha’aninsu, shi ne a ba da akuya ko tunkiya dalilin wannan tsanantawa kuwa, don su sun rigaya sun saba da mutane kwarai.
Za a iya samun Imam Ahmad Adam Kutubi (SP) ta 08036095723
___Ziyarar Masallacin Annabi (SAW)
Madina gari ne babba, yana wajen Arewa da Makka. A cikin Madina Masallacin Annabi (SAW) yake, kuma kabarin Annabi da na Sahabi Abubakar da Sahabi Umarul Faruku suna nan a cikin Masallacin nan an kebe su a gefen Gabas na Masallacin. Kaburburan nan uku a jere suke. Kabarin Annabi (SAW) shi ne farko daga Yamma, sa’an nan a Gabas da shi sai kabarin Sahabi Abubakar, sa’an nan na Sahabi Umaru. Ya kamata mu san cewa alkiblar masallatan Madina tana kallon Kudu ne.
Mutum yana tafiya Madina don ya ziyarci Masallacin Annabi Muhammad (SAW) da kuma don ya samu yin salloli a cikin Masallacin Annabi (SAW) domin an ruwaito cewa yin Sallah a Masallacin Ka’aba ko na Madina ko Masjidul Aksa na Baiti Makaddasi a Falasdinu ya fi yin Sallah a wasu wuraren da lada mai yawa. Sauran masallatan duniya kuwa darajarsu daya ce.
Ziyarar kabarin Annabi (SAW) mustahabbi ne, Annabi (SAW) ya ce:
“Man zara ni ba’ada mauti fa ka’annama zara ni fi hayati”
Ma’ana: “Wanda ya ziyarce ni bayan mutuwata kamar ya ziyarce ni a halin rayuwata ce.”
Ga yadda ake yin ziyarar:
- An so mutum ya dakata a wajen Madina don ya yi wanka ya sa tufafinsa masu kyau, ya sa turare kuma.
- Sa’an nan ya kama hanyar tafiya zuwa Masallaci a kasa yana mai yawaita salati ga Annabi (SAW) a lokacin tafiyarsa, zai yi salatin a cikin zuciyarsa.
- Da shigarsa Masallacin an so ya fara da yin Sallah raka’a biyu (Tahiyyatul Masjidi) idan ya halatta a yi nafila a lokacin nan. Idan kuwa yin nafila a lokacin bai halatta ba, sai ya fara da yin ziyara.
- Kowace irin Sallah mutum zai yi a Masallacin Madina ta farilla ce ko ta nafila an so ya yi ta a wurin nan da ake kira Raula. Filine a cikin Masallacin wanda ke tsakanin mumbarin liman da Hubbaren Annabi (SAW) shi ake kira Raula.
- Idan zai fara ziyara, zai tsaya ya fuskanci kabarin Annabi (SAW) wato bayansa yana kallon alkibla. An ki wato an karhanta ya lika jikinsa ga ginin hubbaren, ko ya taba shi da hannu, ko ya sumbace shi, ko ya zagayo shi da yawo. Abin da ake so shi ne nuna girmamawa ga kabarin nan. Wannan kuwa ana yin sa ta hanyar tsayawa wuri daya cikin kawaici da dan nisa daga kabarin.
- Idan ya tsaya a gaban kabarin Annabi (SAW) sai ya ce:
“Assalamu alaika ayyuhan Nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu.”
Sa’an nan ya ci gaba da yin salati a gare shi.
- Sa’an nan ya gurgusa zuwa ta damansa kamar zira’i daya ya tsaya daidai da kabarin sahabi Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya ce:
“Assalamu alaika ya Ababakarin as Siddik wa rahmatullahi wa barakatuhu.”
Sa’an nan ya kara da yi masa addu’a ta alheri.
- Sa’an nan ya sake gurguwa ta damansa kamar zira’i daya kuma ya tsaya daidai da kabarin Sahabi Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce:
“Assalamu alaika ya Aba Hafsin Umarul Faruk wa rahmatullahi wa barakatuhu.” Sa’an nan ya kara da yi masa addu’a ta alheri.
Koyaushe mutum ya shiga Masallacin Annabi (SAW), zai yi wannan ziyara kamar yadda muka siffanta.
Imam Ahmad Adam Kutubi (SP)