Aikin Hajji: Saudiya ta saka harajin Riyal dubu biyu ga tsaffin Alhazai
Hukumar kasar Saudiya ta saka harajin Riyal dubu biyu, kwatankwacin Naira dubu dari biyu ga duk wani Tsohon Alhaji ko Hajiya da ke da niyyar zuwa Aikin hajjin badi. Wannan mataki na Saudiya ya biyo bayan kokari da take yi ne na bai wa sabbin maniyyata damar sauke farali. Babban daraktan Gudanarwa na Hukumar Aikin […]
Hukumar kasar Saudiya ta saka harajin Riyal dubu biyu, kwatankwacin Naira dubu dari biyu ga duk wani Tsohon Alhaji ko Hajiya da ke da niyyar zuwa Aikin hajjin badi. Wannan mataki na Saudiya ya biyo bayan kokari da take yi ne na bai wa sabbin maniyyata damar sauke farali.
Babban daraktan Gudanarwa na Hukumar Aikin Hajjin Jihar Kaduna, Malam Lawan Yakubu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da fara sayar da kujerun hajjin shekara ta 2018.
Ya kara da cewa wannan haraji na riyal dubu biyu, Tsohon Alhaji zai biya ne bayan an bayyana ainihin kudin kujerar aikin hajjin badi.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu hukumar Alhazai ta kasa ta umarci duk sabon maniyyaci da ya ajiye naira dubu 800,000 a asusun gata, kafin a sanar da ainihin kudin kujerar hajji.
“Hukumar Saudiya ce ta daura harajin riyal dubu biyu ga duk wanda ya aiwatar da aikin Hajji shekara biyu baya zuwa wannan shekara da ake ciki. Duk wanda ya zo da fasfo dinsa cewa yana son tafiya aikin Hajji badi misali. Toh. Sai ya tanada riyal dubu biyu baya ga kudin kujera da aka sanar.
“Amma wanda bai taba zuwa ba shi bai da wannan kari a kansa. Kuma hukumar Saudiya ce ta saka wannan tsari kuma ba za a bada takardar shiga kasa ba sai mutum ya biya wannan kudi ko haraji. Ba dai za a hana ba, amma an tanadi abin da mutum zai biya kafin ya tafi,” inji shi.
Game da batun ragistar kujerar badi kuwa, sai daraktan ya ce Duk maniyyacin jihar zai ajiye naira dubu 800,000 kuma ana bukatar mutum ya ajiye akalla naira miliyan daya da dubu dari biyar kafin watan Faburairun badi kafin hukumar alhazan kasa ta bayyana ainihin kudin kujerar hajjin shekara 2018.
“An kuma hana yi wa mutum ragista ba tare da an ganshi ba, dole ne maniyyaci ya halarci wajen ragista da kansa domin a ganshi.
“ Kamar yadda aka sani, mata masu ciki an hanasu zuwa aikin Hajji saboda abubuwan da kanje ya dawo. Hukumar Alhazai ta kasa ne ta bada wannan umarni. Cikinsu har da tsaffi suma idan babu wanda zai rakasu ba za a bari su je ba.
“Aikin Hajji aiki ne mai girma kwarai da gaske, don haka ba za a so a ce mutum ya biya kudinsa masu yawa ba, amma kuma bai yi yadda ake so ba,” inji shi.
Daraktan ya kuma yabawa gwamnatin jihar a kokarin goyan baya da take ba su domin tabbatar da cewa kamar kullum jihar ta samu nasarar aiwatar da aikin Hajji cikin sauki.
daya daga cikin maniyyatan da ya biya kudinsa daga karamar Hukumar Soba, Tijjani Shekari ya yabawa hukumar aikin hajjin bana akan tsare-tsarenta domin saukakawa maniyyatan jihar.
Shima Ibrahim idris daga Soba ya ce a yanzu haka jama’a sai zuwa suke yi domin biyan kudin da aka amince su ajiye a asusun gata na hukumar tare da yin fatan Allah Ya basu ikon cika sauran kudin da ya rage kafin a bayyana kudin kujerar bara.