Aikin Hajjin 2021: An fara rajistar maniyyata

Maniyyatan da suka bar kudaden kujerunsu na Hajjin 2020 za su samu fifiko

Aikin Hajjin 2021: An fara rajistar maniyyata

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta umarci hukumomin alhazai na jihohi da su fara rajistar maniyyata aikin Hajjin 2021.

Sanarwar da Kwamishinan Ayyuka na NAHCON Abdullahi Magaji Hardawa ya fitar a ranar Alhamis ta umarci hukumomin jihohin da su bayar da fifiko ga maniyyatan suka biya kudin kujerun aikin Hajjin 2020 da bai samu ba, suka bar kudadensu domin aikin Hajjin bana.

Hardawa ya ce za a ba da damar rajista maniyyata ne gwargwadon lokacin da suka bayyana aniyarsu ta yin rajista.

Ya kuma ce NAHCON za ta bude shafinta na yin rajistar maniyyata ta intanet, www.nigeriahajjcom.gov.ng, da zai rika aiki awa 24 har sai an rufe yin rajistan.

Sai dai ya yi bayani cewa daga karshe sharuddan da hukumomin kasar Saudiyya suka fitar ne za su yanke hukuncin yadda abubuwa za su kasance.