Aikin hanya ya gurgunta kasuwancinmu – ‘Yan Kasuwa

Masu gudanar da harkokin kasuwanci a kan titin Unguwar Sabuwar Gandu sun koka game da rashin kammala aikin hanyar da ake yi musu wanda  aka soma tun a farkon shekarar bara. Wani mai sayar da kayan marmari akan titin mai suna Malam Ya’u Ahmad ya bayyana cewa su ma suna fuskantar matsala saboda yanayin yadda […]

Aikin hanya ya gurgunta kasuwancinmu – ‘Yan Kasuwa

Masu gudanar da harkokin kasuwanci a kan titin Unguwar Sabuwar Gandu sun koka game da rashin kammala aikin hanyar da ake yi musu wanda  aka soma tun a farkon shekarar bara.

Wani mai sayar da kayan marmari akan titin mai suna Malam Ya’u Ahmad ya bayyana cewa su ma suna fuskantar matsala saboda yanayin yadda kura ke lullkube musu kayayyakin sayarwarsu, ya jawo sun rasa abokan cinikinsu. “a duk lokacin da mutum ya kasa kaya a wanan wuri to haka zai yi ta fama da karkade kura wani lokacin ma idan muka ga kurar ta yi yawa ba ma kasa kayan sai mun ga ta lafa. Irin wanann kura ta janyo mun rasa abokan cinikinmu da dama, domin ba kowa ne zai sayi kayan da kura ta lullube su ba.”

Shi ma wani mai kanti da ke sayar da kayan masarufi a kan hanyar ya yi korafi game da hanyar, inda ya ce a duk lokacin da kurar ta lullube kayansu sai mutane su ki sayen kayan domin tunaninsu kayan sun dade ko ma wani ya yi tunanin kayan sun dade da lalacewa.

‘Yan kasuwar sun bayyana cewa kammala titin zai taimaka musu wajen saukaka musu zirga-zirga da kuma dawo da martabar harkokin kasuwancinsu, don haka suka yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki ta hanyar kammala aikin hanyar akan lokaci.

Har ila yau al’ummar unguwar sun bayyana cewa rashin kammala hanyar ba wai kawai ga harkokin kasuwancinsu ya tsaya ba ne, ya na haifar musu da matsaloli da dama ta fuskar lafiyarsu kasancewar mutane na shakar kura da ke tashi koyaushe. “a yanzu haka wadanda ke da ciwon asma kullum a cikin damuwa suke, wadanda kuma ba su da shi, su ma akwai yiyuwar su kamu da wasu cututtukan saboda irin kurar da ke tashi a wurin wanda ko kaki mutum ya yi sai ya ga kura a ciki”

Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Aliyu Aminu Aliyu Wudil inda ya ce ba dakatar da aikin titin aka yi ba, a cewarsa za a kamamla aikin nan ba da jimawa ba. “Wannan titi shi ne wanda ya tashi daga Sabuwar Gandu ya je Gidan Maza ya zarce har Kumbotso. Ana ci gaba da aikin wanan hanya ba wai an dakatar da aikin ba ne. Sannan kamar yadda kika sani aikin tituna ana yin sa daki-daki ne. An gama zuba wanann kasa da ki ka gani bayan an kankare shi. Yanzu kuma za ki ga aikin lambatu ake yi hagu da dama. Shi kuma wannan aiki idan ana yi ba a taba kasa don gudun kada ta koma cikn ramin. Shi dan kwangilar yana kokarin yin hakan ne don a samawa ruwa hanya, domin gab muke da faduwar damina a yanzu. Idan ruwa ya sauka ba zai bata titin ba. Idan suka gama aikin magudanar ruwan za su koma su ci gaba da aikin titin insha Allah.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya