Aikin hanyoyin Jihar Zamfara ya fi na sauran jihohi inganci – Kwamishina

Kwamishinan Ayyukan na Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sharu Anka ya ce aikin ginin hanyoyin da gwamnatin jihar ta yi a cikin shekara uku da suka gabata ya fi na sauran jihohin kasar inganci da aminci saboda amfani da ingantattun kayan aiki da injiniyoyi da suka san matsalar hanyoyin jihar.Kwamishinan ya fadi haka ne a tattaunawa […]

Aikin hanyoyin Jihar Zamfara ya fi na sauran jihohi inganci – Kwamishina
Aikin hanyoyin Jihar Zamfara ya fi na sauran jihohi inganci – Kwamishina

Kwamishinan Ayyukan na Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sharu Anka ya ce aikin ginin hanyoyin da gwamnatin jihar ta yi a cikin shekara uku da suka gabata ya fi na sauran jihohin kasar inganci da aminci saboda amfani da ingantattun kayan aiki da injiniyoyi da suka san matsalar hanyoyin jihar.
Kwamishinan ya fadi haka ne a tattaunawa da manema labarai a Gusau, inda ya ce Gwamna Abdul-Aziz Yari Abubakar ya ba da umarnin gina hanyoyin da suke da inganci da aminci a wuraren da aka bayar da kwangila, domin magance yawan hadari da ambaliyar ruwa da rashi hanyoyin ke haifarwa. “Gwamna Yari ya umurce mu, mu tabbatar duk ’yan kwangilar suna aiwatar da hanya kamar yadda aka yi alkawari da su, kamar aza harsashinsu da duwatsu da za a cakude su sosai da kankare ta yadda hanyar za ta zauna daram. Ba shakka sai mun aza wannan harsashi mai kauri sannan ake shimfida kwalta, wani wuri ma kwalta har sau biyu,” inji Kwamishinan.
Ya ce, gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan 70 don gina hanyoyi masu nisan kilomita
dubu daya a lungu da sakon jihar.
Ya ce, baya ga birnin Gusau da hedkwatocin kananan hukumomi, sun aiwatar da hanyoyi daga yammacin Zamfara zuwa gabashinta da ta fara daga Gumi zuwa Gayeri da Bardoki zuwa Gyalange. “Akwai kuma ta daki-Takwas zuwa Gumi zuwa Bukuyyum zuwa Anka da kuma babbar hanyar Gusau zuwa wadda ta tashi daga Bakura zuwa Sakkwato. Sai wadda ta taso daga kauran Namoda zuwa Kasuwar Daji zuwa Gusau da sauransu. Kuma an fara aikin hanyar kaura zuwa Birnin Magaji,” inji shi.
Alhaji Sharu Anka ya ce dalilinsu na bai wa aikin hanya muhimmanci shi ne domin bunkasa birane da kauyuka da kuma inganta sufuri da samar da saukin fitowa da amfanin gona.
Wannan inji shi, ya sanya an samu saukin fitar da amfanin gona a tsawon shekara uku da suka gabata da kuma inganta rayuwar mazauna karkara da kuma magance matsalar ambaliyar ruwa da rashin magudanun ruwa ke haifarwa. Ya nemi hadin kai da goyon bayan al’ummar jihar domin ba gwamnati damar ci gaba da ci alkawuran da ta yi na bunkasa rayuwarsu.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya