Aikin injiniya ba na maza ne kawai ba – Injiniya Amina Sallau Aliyu
Injiniya Amina Sallau Aliyu ita ce Shugabar kungiyar Mata Injiniyoyi reshen Jihar Kano, a tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa aikin injiniya ba na maza ne kawai ba, mata ma suna da gagarumar gudummawar da za su iya bayarwa a aikin injiya. Haka kuma ta bayyana cewa idan har ana so a shawo kan matsalolin […]
Injiniya Amina Sallau Aliyu ita ce Shugabar kungiyar Mata Injiniyoyi reshen Jihar Kano, a tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa aikin injiniya ba na maza ne kawai ba, mata ma suna da gagarumar gudummawar da za su iya bayarwa a aikin injiya. Haka kuma ta bayyana cewa idan har ana so a shawo kan matsalolin da ake fuskanta a rayuwa to dole sai iyaye sun kula da tarbiyyar ’ya’yansu maza kamar yadda suke kulawa da ta mata:
Tarihin rayuwa:
An haife ni a garin Kano. Na yi karatun firamare a Makarantar Firamare ta Magwan daga 1983 zuwa 1988. Bayan na kammala sai na tafi Sakandiren ’Yan mata ta WTC Kano, a can na yi karamar sakandare. A shekarar 1991 sai na yi jarrabawar kimiyya inda na tafi Kwalejin Kimiyya ta Jahun a Jihar Jigawa. Bayan na kammala a shekarar 1994 sai na samu gurbi a Jami’ar Bayero a bangaren share fagen digiri. Daga nan sai na samu gurbin karatu a bangaren Injiniya.
Lokacin da na samu wannan gurbin karatu hankalin ’yan gidanmu ya tashi kasancewar ba a saba ganin mata suna karantar wannan fanni ba. Tun ina karama burin mahaifiyata shi ne na zama likita, ni ma kuma da wannan tunani na tashi. Don haka da aka ce zan karanci injiniya sai hankalin gidanmu ya tashi. Kowa yana maganar yaya za a yi na yi wannan karatu bayan karatu ne na maza. Haka ya sa muka je jami’a muka nemi a canza mini kwas.
A lokacin sai malamin namu ya yi kokarin kwatar mana da hankali cewa mata ma suna iya karantar fannin injinya, don haka muka koma gida. Amma dai duk da haka ‘yan gidanmu ba su gamsu ba. Da mahaifina ya ga ana ta kai wa da komowa akan maganar sai kawai ya kirani ya ce na hakura na je na yi wannan karatun tare da yi mini addu’ar Allah Ya sa albarka a ciki. A haka dai na tafi na yi karatun ba don raina ya so ba, domin zan iya cewa shekarar farko da na yi babu wata natsuwa da na samu na karatu, domin kullum tunanin za a canza mini kwas amma da yake haka Allah Ya so sai ba a canza mini ba.
Daga baya sai na fahimci cewa ashe tunaninmu a kan karatun injiniya ba daidai ba ne, kamar sauran karatu ne kowa ma zai iya yi matukar ya dage. Haka na ci gaba da karatuna har na kammala cikin nasara a shekarar 2003. A shekarar 2004 kuma sai na je na yi bautar kasa a Jihar Kwara. A shekarar 2005 na koma karatu don samun digiri na biyu. A cikin wannan shekarar ce kuma na samu aikin koyarwa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil. A yanzu haka kuma ina karatun digiri na uku a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Ayyukan kungiyar mata injiniyoyi:
Kasancewar al’ummarmu ba su da wayewa game da karatun injiniya a wajen mata. Hakan ya sa kungiyarmu take kokari wajen wayar wa al’umma kai musamamn ma yan makaranta. Kin san tunanin mutane idan aka ce injiniya wani aiki ne na karfi ko na hawa falwaya da sauransu. Ire-iren wannan tunanin muke kokarin kawarwa a zukatan mata musamman ’yan sakandare inda muke nuna musu cewa mace ma za ta iya yin wanan karatu har kuma ta yi aiki. A aikin injiniya akwai abin da ake kira family engineering, wato yanayin yadda ake gudanar da aikin, akwai injiniya a sama wanda shi zai tsara yadda yake son abu ya kasance, ko gini ne ko kuma wani abin daban, to zai bayar da shi ga wadanda za su yi aikin, don haka a matsayin Injiniya ba dole ne sai ka je ka yi wani aikin karfi ba.
Ga ’yan jami’a kuma mukan wayar musu da kai cewa su daina sa damuwa a cikin ransu game da aikin da za su samu bayan kammala karatu. Muna nuna musu cewa su mayar da hankalinsu ga karatunsu yadda za su samu su ci jarrabawa, idan ya so batun aiki ya zo daga baya, ma’ana bayana an kammala karatu.
Sannan kuma muna shirya gasar darussan kimiyya a tsakanin makarantun sakandare, muna da wani shiri da muke kira ‘catch them young’ inda muke kokarin shirya wa yaran gasar darussansu na makaranta da kuma muhawara a tskanain su daliban. Muna kuma koyar wa ’yan sakandare kwamfuta kyuta. A kwanakin baya ma mun shirya irin wannan gasar inda Kamfanin Gongoni suka taimaka mana da kyaututtukan da muka raba wa daliban da suka samu nasara.
Nasarorin da ta samu:
Ina ganin bayar da gudummawata ga ci gaban al’umma nasara ce, domin idan har a matsayina na injiniya na tsara yadda titi zai kasance aka kuma gina shi mutane suka yi amfani da shi na samu nasara. Haka kuma a yanzu da muke koyarwa a makaranta idan dai har muka bayar da ilimin da kyakkyawar niyya mun san cewa muna da lada.
kalubalen da take fuskanta:
kalubale akwai shi. Misali tun a makaranta abokan karatunmu maza suna yi mana wani kallo na wanda muka yi masu shisshigi cikin hakarsu. Haka ma a wurin aiki wasu sai rika ganin idan an bai wa mace aiki kaza ba za
ta iya ba. Yawanci abin da muke yi shi ne mu nuna musu cewa za mu iya din ba wai a baki ba har a aikace, ta yadda za su gane cewa mata ma suna da kwakwalwa. Idan kika duba za ki ga duk wasu ayyuka da ake yi a jihar nan da suka hada da tituna da gadojin sama za ki tarar da sa hannun ’yan uwanmu injiniyoyi mata a ciki.
Iyalinta:
Na yi aure a shekarar 2009. A yanzu haka ina da ’ya’ya hudu mace daya da maza uku.
Mutane abin koyi:
Babu shakka mahaifiyata ita ce abar koyi a gare ni, domin ita mace ce mai jajircewa a kan duk wani abu da ta sanya a gaba. Haka kuma ina kallon matan Manzon Allah (SAW) a matsayin matan da nake koyi da rayuwarsu.
Burinta a rayuwa:
Burina shi ne na ga na farantawa mutane rai, ta hanyar kawo musu abin da zai zama ci gaba a rayuwarsu. Haka kuma ina burin na ga mata musamman ma na yankin Arewa sun zama injiniyoyi ta yadda mu ma za mu iya bayar da gudummawarmu a wannan fanni kamar sauran fannonnin ilimi da mata ke samun kwarewa a kai.
Abin da take so a tuna ta da shi:
Ina so ko bayan raina a tuna da ni a matsayin wacce ta bayar da guddumawa wajen taimakawa al’umma da kuma dabi’u nagari. A tuna da ni a matsayin wacce ta kawo ci gaba cikin rayuwar zamantakewar al’umma.
Shawararta ga mata:
Shawarata ga mata musamman ma’aikata shi ne su kame kansu su rike mutuncin kansu. Ki sani cewa ke wata a bar kwaikwayo ce ga wasu mutane da ke kusa da ke. Ba tare da saninki ba, ke kina ta rayuwarki, wata na can gefe tana kwaikwayon rayuwarki ko kuma ana misali da ke, ma’ana irin yadda kike gudanar da rayuwarki. A dalilinki wani zai iya barin ’yarsa ko matarsa ta yi karatu ko kuma ta yi aiki. Haka kuma akasanin hakan zia iya faruwa idan ba ki kame kanki ba.
Sannan ina kiran ’yan uwana mata mu yi amfani da iliminmu wajen ganin mun ba al’umma gudummawa. A duk wani lokaci da muka samu kanmu a cikin taro mu yi tunanin abin da za mu fada wanda zai amfanar da al’umma ba wai kawai a je a yi hirar duniya a tashi ba. Kai ko a irin hirar nan da ake yi ta kafofin sada zumunta mu yi kokarin ganin muna kara wa junanmu sani game da abin da zai amfane mu a rayuwarmu da ta iyalinmu.
Mata mu yi kokarin ganin mun tsaya sosai wajen tarbiyyar ‘ya’yanmu. Kada mu mayar da hankali ga a abin da ya shafi neman ilimi kawai. Idan muna so mu ga tasirin ilimin to dole sai mun hada da tarbiyya. Tarbiyyar nan kuma ba bangare daya ba, yadda muke bai wa ‘ya’yanmu mata tarbiyya ya kamata mu sanya maza a ciki. Idan za ki sa ‘yarki mace aikin gida to shi yaronki namiji sa shi ya wanke wa kannensa koda safa ce, ki aike shi ya sayo miki kayan miya, ko ya gyara kwatar gidan da sauran ayyuka. Hakan shi zai sa ya tashi da sanin cewa shi ma akwai wani nauyi da yake kansa a rayuwa. Ba wai kawai don yaro yana namiji mu kyale shi ba tare da yin wasu ayyuka a cikin gida ba, ko kayan shimfidarsa sai mahaifiyarsa ta kwashe masa. Mu sani hakan ba gata ba ne kuma ba karamar illa yake yi a rayuwar yaro ta nan gaba ba.
Kamar yadda muke yi wa yarinya tarbiyya cewa za ta yi aure don haka ta yi kaza, shi ma namijin lokaci ya yi da za mu rika nuna masa hakan.
Idan za mu sanya shi aiki mu nuna masa cewa shi ma nan gaba aure zai yi, nauyi zai hau kansa don haka ya fara gwadawa tun daga matakin yarinta.
A nuna masa cewa idan ya girma ya dauki nauyin gidansa don ya samu cikakkiyar kima a wurin iyalansa.
Haka kuma dole a matsayinmu na iyaye mu nuna wa ’ya’yanmu cewa muna da muhimmanci gare su don haka iyayenmu suka nuna mana. Za ki ga ’ya’yan yanzu iyayensu na yi musu magana amma suna can suna latse-latsen wayar hannu hankalinsu sam ba ya kan iyayen, wannan yana samuwa ne saboda rashin nuna wa ’ya’yan muhimmancin da muke da shi a gare su.