Aikin jarida ba na maza ne kawai ba – Misis Kwapchi Bata Dibal

Kwapchi Bata gogaggiyar ’yar jarida ce da ta yi aiki a gidan Talabijin na kasa (NTA)  a Jihar Borno.   Ita ce Shugabar kungiyar Mata ’Yan jarida ta kasa (NAWOJ) reshen Jihar Borno. Kuma Babbar Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima   kan Harkokin Watsa  Labarai tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu. A zantarwarta […]

Aikin jarida ba na maza ne kawai ba – Misis Kwapchi Bata Dibal
Aikin jarida ba na maza ne kawai ba – Misis Kwapchi Bata Dibal

Kwapchi Bata gogaggiyar ’yar jarida ce da ta yi aiki a gidan Talabijin na kasa (NTA)  a Jihar Borno.   Ita ce Shugabar kungiyar Mata ’Yan jarida ta kasa (NAWOJ) reshen Jihar Borno. Kuma Babbar Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima   kan Harkokin Watsa  Labarai tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu. A zantarwarta da wakilinmu ta tabo batutuwa da dama da suka shafi rayuwarta kamar haka:

 

Tarihina:

Sunana Kwapchi Bata Dibal.  An haife ni ne a Jihar Kano amma mu ’yan asalin garin Durkwa a karamar hukumar Hawul da ke Jihar Borno ne. An kuma haife ni a ranar 29 ga watan Maris din 1980 daga zuriyar Honurabul Bata Fifi Dibal da Uwargida Mwajim Bata, dukansu Allah Ya yi musu rasuwa. Ni ce ’ya ta shida cikin ’ya’ya bakwai da suka haifa, kuma iyayena masu addini ne kuma ’yan boko. Sannan mahaifina gogaggen dan siyasa ne. Na girma a garinmu.   An sa ni a shahararriyar makarantar firamare nan ta Shehu Garbai da ke Maiduguri a 1988 zuwa 1993. Bayan na gama sai na tafi Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC)  a tsakanin 1993 zuwa 1998, ina babban aji na 2 zan je na 3 sai na rubuta jarrabawar neman shiga jami’a  (JAMB) inda na samu sa’ar cin jarrabawar na tafi Jami’ar Maiduguri a 1999 inda na samu digiri dina na farko a bangaren aikin jarida  (Mass Communication). Bayan na kammala hidimar kasa (NYSC)  ta shekara daya a Jihar Abiya a shekara ta 2006 sai na sake komawa jami’ar don yin digiri na biyu, daga baya sai na samu tallafin karatu daga Gidauniyar bolkswagen ta kasar Jamus inda na yi PGD.   Hakan ya ba ni damar  tafiya Jami’ar Koyar da Waka (Unibersity of Music) ta Hanober da ke kasar Jamus.  Sannan na sake zuwa wata jami’a a kasar Ghana da ake kira Unibersity of Legon and Cape Coast don yin karatu na daban.  Sannan na je wani gajeren kwas a Jami’ar Koyar da Aikin Jarida da ke Landan wanda gwamnatin Jihar Borno ta dauki nauyina. Na fara aiki da Gidan Talabijin na kasa (NTA) ne a shekarar 2006 bayan na dan taba aiki na kwantaragi a lokacin da nake karatu.

 

Ayyukan da na yi:

A shekarar 2006 na fara aiki da NTA kuma har yanzu ban canja wurin aiki ba, a matsayin mai gabatar da labarai.  A lokacin da na fara karanta labarai abin ya burge ni saboda tun ina karama nake sha’awar in zama mai gabatarwa ko karanta labarai a gidan talabijin. Ina samun aiki da NTA a wannan shekarar a matsayin mai dauko rahotanni sai na ji dadi matuka saboda burina ya cika kuma a wancan lokacin a dakin shirya labarai na NTA Maiduguri ni ce karamarsu amma duk da haka ban ga wani bambanci ba. Wata rana da yamma a lokacin ina sabuwar ma’aikaciya na tashi a aiki zan tafi gida saboda mai gabatarwa bai zo da wuri ba sai mai shirya labarai ya ce ni ce zan yi labarai saboda mai yin labaran ya makara ganin cewa sabuwa ce ni ana fara kidan nan na sit tune sai kirjina ya fara bugawa ina fargabar ganin zan karanta labarai ban shirya ba amma cikin ikon Allah sai na karanta lafiya. Ganin ina karantawa ina dan samun kura-kurai manya suna gyara mini har na fara kwarewa da haka har na shiga jerin masu karanta labarai.

 

Nasarorin da na samu:

Gaskiya dadin aikin jarida aiki ne na yin gayya ba na mutum daya ba, za ku yi aiki tare ne don cimma buri.  Nasarar da na samu a wannan aiki shi ne aiki ne wanda za ka ga ka gano matsalolin jama’a ka yi labari don a magance musu. Ina tuna wani lokaci da na yi wani rahoto a kan kiwon lafiya wanda ya jawo hankalin gwamnati ta magance matsalar, kuma ba ni kadai na samu wannan nasarar ba, shi ya sa na ce aiki ne na gayya. Akwai mai kyamara, akwai wanda zai rubuta labarin da kuma tace shi, editanka ga duk nasarar tamu ce baki daya hatta da direban motar da ya tuka mu zuwa aikin shi ma ya ba da tasa gudunmawar.

 

kalubale:

A aikin jarida akwai kalubale. Babu yadda za a yi ka fito yau ko gobe wani bai kalubalen ce ka ba, amma komai za ka yi, ka yi mai kyau, kuma kafin a ba ni bangaren aiki, ina dauko labarai ne da suka shafi na al’amuran tsaro wadanda mata ’yan kadan ne ke iya kasancewa a fagen  rahoton tsaro a kasar nan, a Jihar Borno kowa ya san halin da tsaro yake ciki amma dai mun gode Allah.   A shekarar 2009 ni nake dauko rahotannin rikice-rikicen da suka rika faruwa a Borno daga farko har karshe tare da Lydia Samson da Jemima Bassi da Aliyu Mshelia da masu dauko mana hoto su biyu Modumele da Zakariah Isah, wanda daga baya aka kashe shi. 

A lokacin wani rikici mun  taba kwana a benci  idonmu biyu a ofis kawai don mu rika sanar da masu kallonmu halin da ake ciki. Har yanzu kalubalen da na fuskanta a wannan aikin, wata rana mun je dauko rahoto a ofishin Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Borno a hedkwatar ’yan sanda sai aka kai wani mummunan hari lokacin ni da Jemima Bassi da mai kyamara dinmu marigayi Zakaria Isah muna tare a ofishin.  Don haka ina ganin aikin jarida ba na maza ne kadai ba.

 

Burina a rayuwa:

Kamar kowace mace, burina shi ne in zama ’yar majalisar jiha don taimaka wa mata da yara. Lallai ina da burin in zama ’yar majalisa don in inganta rayuwar al’umma musamman mata da yara kanana. A kan haka nake da burin tsayawa takarar ’yar Majalisar Dokokin Jiha a zabe mai zuwa.

Sannan na yaba da yadda Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno ya gudanar da ayyukan ci gaba a jihar, don haka zan so na kasance daya daga cikin wadanda za su gabatar da kudirin doka don a ci gaba da kare irin wadannan kyawawan ayyuka.

 

Tufafin da suka fi burge ni:

Tufafi kawai ina son wanda yake da tsari da zai sa duk wanda ya gan ni ya san na sa tufa ta kamala wadda za ta rufe mini jiki ba kawai ki sa kaya ki bar jikinki a bude ba, wai don duk wanda ya ganki ya ce wance ta sanya kaya masu tsada ba.

 

Hutu:

Hutuna ba wai ina zuwa wasu wurare na musamman ba ne, ina yin hutuna ne da iyalai saboda na rika sanin halin da suke ciki domin yanayin aiki ba koyaushe mutum yake kasancewa da su ba, idan muka zauna da su a nan ne sai mu tsara inda za mu je hutu.

 

kungiyoyi:

Ni mamba ce a kungiyar Mata ’Yan jarida ta kasa (NAWOJ) kuma yanzu haka ni ce shugabar kungiyar a Jihar Borno.  Ina kuma cikin kungiyoyi addini da wanda ba na addini ba.  Sannan ni mamba ce a kungiyar ’Yan jarida ta kasa (NUJ).

 

Kasashen da na je:

Na je kasashe da yawa a duniya amma na je ne don wasu bukatu na kaina. Ba na son in bayyana su amma dai alhamdulillahi na je Isra’ila wanda aikin ibada ne ya kai ni.

 

Shawara ga iyaye:

Ina mai bai wa iyaye shawarar sanya ’ya’yansu a makaranta don su samu ilimi domin ko ni a gidanmu iyayenmu sun haife mu mu bakwai ne amma ba sa bambanta  mace da  namiji musamman a bangaren tarbiyya.

Kasancewa mace da namiji duk ’ya’ya ne kuma ba karamin kokari iyayena suka yi ba wajen kashe mana kudi da ’yan uwana don mu yi karatu wanda a kullum mafarkin mahaifinmu shi ne Allah Ya ba shi abin da zai biya mana mu yi karatu. Karatu yana da kyau yanzu haka a gidanmu babbarmu tana da digiri na uku. Muna da injiniya muna da likita da yanzu ya zama Babban Likita a lokacin yana dan shekara 35. Muna da masanin harkar aikin gona, sannan ni kuma ’yar jarida ce, akwai kuma wanda ya karanta kimiyyar kwamfuta. Don haka ina mai bai wa iyaye shawara kada  su tauye wa ’ya’yansu ’yanci wajen hana su damar su yi karatu domin ilimi shi ne gishiri kuma tushen rayuwa. Har ila yau kada iyaye su ki sanya ’ya’yansu a makaranta saboda za su dora musu talla ko don auren wuri, wannan ba daidai ba ne.