Aikin jarida ba na yin kudi ba ne na samun martaba ne da farin jini – Halima Jimirou

Halima Jimirou daya ce daga cikin ’yan jarida mata da ta yi fice a gidan rediyon Muryar Amurka, ’yar kasar Nijar din ita ce bakuwarmu a yau inda ta ba mu tarihin gwagwarmayarta a wannan aiki: Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?Halima: To, sunana Halima Jimirou, an haife ni a garin Mainasarowa a ranar  27 ga […]

Aikin jarida ba na yin kudi ba ne na samun martaba ne da farin jini – Halima Jimirou
Aikin jarida ba na yin kudi ba ne na samun martaba ne da farin jini – Halima Jimirou

Halima Jimirou daya ce daga cikin ’yan jarida mata da ta yi fice a gidan rediyon Muryar Amurka, ’yar kasar Nijar din ita ce bakuwarmu a yau inda ta ba mu tarihin gwagwarmayarta a wannan aiki:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?
Halima: To, sunana Halima Jimirou, an haife ni a garin Mainasarowa a ranar  27 ga Yulin 1965,  na yi makaranta a Yamai, daga firamare har zuwa jami’a sai dai ina jami’a ne na tafi Jami’ar Ife  (a Najeriya) don ci gaba  da karatun digirina a harshen Ingilishi.
Aminiya: Yaya aka yi kika tafi Jami’ar Ile-Ife daga Jami’ar Yamai?
Halima:  A lokacin akwai yarjejeniya ne a tsakanin jami’armu wato ta Abdu Mummuni Jofo da ta Ile-Ife ga masu karatun harshen Ingilishi da masu karatun harshen Faransanci, su za su zo jami’armu su yi shekara biyu mu ma mu je Ile-Ife mu yi shekara biyu, wato ana so mu kasance inda Ingilishi ne zalla ba cakuduwa da harshen Faranshi su ma haka nan ba harshen Ingilishi.
Aminiya: To, yaushe kika fara aiki na jarida?
Halima: Na fara aikin jarida ne a 1992 a kasarmu Jamhuriyar Nijar, ba da rediyo na fara ba da ta rubuce-rubuce na fara a jaridar Amfani, kafin mai jaridar ya bunkasa aikin har ya kai ga bude gidan rediyo To da ya bude gidan rediyo ne sai na koma aiki da bangaren rediyo na kamfanin Amfani.
Aminiya: Me ya ba ki sha’awar shiga aikin jarida ko shi ne dalilin da ya sa kika karanta harshen Ingilishi?
Halima: Na dade ina sauraren gidajen rediyo musamman BBC da bOA kuma koyaushe Babana da rediyo ba ina zaunawa ba ne in saurara, amma ina sha’awar na ji ko na ga rediyo na magana. Har na fara tunanin yaya mutum zai samu ya yi aiki a irin wadannan gidajen rediyo. A Muryar Amurka ba wanda nake son na ji muryarsa kamar Shehu Yusuf Kura, ta kai idan na gitta na ji Muryar Amurka idan Shehu Kura ne sai na zauna. Kullum sai na rika cewa wai yaya za a yi mutum ya yi aiki a Muryar Amurka shi ma a rika jin sa. Tun ina karama na rika irin wannan tunani. Daga baya kuma sai na yi watsi da batun har na zo na tafi jami’a da na kare jami’a sai na fara aikin jarida da jaridar Amfani. To shi mai jaridar Amfani shi ne wakilin Muryar Amurka a Nijar, cikin wannan lokacin duk ma’aikatan sashin Hausa na Muryar Amurka ’yan Najeriya ne sai aka ce za a dauki dan Nijar a 1995, aka nemi mu mika takardu, lokacin Grema Bukar shi ne daraktan Amfani, mu uku muka yi jarrabawar neman a dauke mu, sai Allah Ya ba ni sa’a.
Aminiya: Shekaru nawa kika yi a Amfani kafin ki zo Muryar Amurka?
Halima: Na yi shekara hudu daga 1992 zuwa 1996, kuma mutum na farko da fara koya mini aikin rediyo shi ne Shehu kaura Allah Ya  jikansa da rahama, ma’aikacin ofishin jakadancin Najeriya ne a Nijar, yana gabatar da wani shiri da ake kira ‘Mu  Zagaya Duniya Mu sha Labari,’ to ya ce hankalinsa ya zo kaina ne domin yana saurarenna a tashar Amfani sai ya ce Halima muryarki ta rediyo ce kuma kina da kwazo don haka bari in koya miki, to da haka ya sa ni cikin wannan shiri nasa, da ma kuma shi ma’aikacin Rediyon Rima ne kafin ya fara aiki a ofishin Jakadancin Najeriya da ke Nijar. To da haka na dan fara fitowa a cikin gidan rediyo. Allah Ya yi wa Shehu kaura rasuwa sakamakon hadarin mota.
Aminiya: Wane bambanci kika gani a tsakanin aiki a gida Afirka da nan Amurka?
Halima: To mu fara da kayan aiki, batu na gaskiya shi ne idan kana aiki a gida ko kasarku sai ka ga cewa duk wani gidan rediyo bai da kayan aiki sai naku, ashe ba haka ba ne sai ka je wata kasa musamman nan kasar Amurka, domin idan ka ga kayan aikinsu, sai ka ce ashe mu gida muna can muna fama da reza ne, saboda za ka ga inda aka ci gaba, saboda za ka ga manyan rediyoyi ne za a hada da kaset amma duk da haka duniya za ta ji, amma dai kayan aiki sai idan ka zo nan.  Su ma Amfani sun bunkasa domin idan ka je za ka ga suna da kayan aiki na zamani amma bai kai na nan ba. Kuma wani abu shi ne ba za a hada aikin gida da nan ba domin wani abu shi ne yanayin biya ya sha bamban.
Aminiya: To mu dubi bangaren ma’aikata nan kuma me za ki ce?
Halima: bangaren ma’aikata ba a ma gamawa saboda yanayin biyan ma ina nufin albashi, ya dace a ce dan jarida ko ina yake cikin duniya ya zamo a sahun farko na masu samun albashi mai tsoka, saboda ya samu kwanciyar hankali kuma zuciyarsa ba za ta je ga wajen wani ba har ya karbi kudin wani ya zo ya fadi abin da ba shi ne ba. Don haka akwai bukatar kafofin watsa labaranmu na gida Afirka, su mayar da hankali wajen kyautata albashin ’yan jarida.
Halima: To, mu dubi huldar ’yan jarida da mutane a nan da kuma gida me ya bambanta su?
Aminiya: Mu fara da ’yan jaridar gida, tsakani da Allah akwai wadanda mu a Nijar muke ce wa ’yan jaridar tuwo. Wadanda kowa ma zai iya kiransu ya yi maganar da ya ga dama ya ba su abin da bai taka kara ya karya ba, domin su rubuta labarinbatanci ga wani, duniya ta karanta kuma a dauka da gaske ne alhali karya ne. Kuma a bangare guda akwai ’yan jaridar da suka san aikinsu suna kuma yi tsakani da Allah, suna kare martabar jama’a da martabar aikin, suna gudanar da shi yadda ya kamata. A gaskiya akwai wadanda suke ’yan jarida ne na gaskiya masu zuwa su nemo labaran gaskiya su rubuta ainihin abin da suka gani ko suka ji.  Sai dai wani abu shi ne ’yan jarida a nan Amurka suna da ’yancin da ya yi yawa, wanda a gaskiya ba na sonsa, idan da ina da iko da na rage wa ’yan jaridar kasar nan wannan ’yanci, aikin da zai ba ka dama ka kira sunan Shugaban kasa ka zazzage shi ko ka kira uwar Shugaban kasa ka aibanta ta, gaskiya wannan ’yanci ya yi yawa, da ina da dama da na rage shi, ko in sa dokar da za ta hana su fadin wasu abubuwa.
Aminiya: Ba ki ganin ’yancin da suka samu ya sa shugabannin wadannan kasashe suke shiga taitayinsu ba su yarda su yi abin da ’yan jarida za su ji har su yi musu fallasa?
Halima: Na yarda, amma duk da haka gaskiya tonon sililin wata sa’a yana yin yawa mu ma a kasashenmu na Afirka akwai masu kamanta gaskiya, amma duk da haka domin ka ga nan shugabanni sun san ko rami suka shiga suka yi abu dan jarida zai shiga ramin ya gano ko ya dauko ma hoto ya fito ya nuna, shi ya sa sau tari za ka ga ba za su yi wani abin ba, amma dai gaskiya ’yancin ’yan jaridar ya yi yawa a nan kasar, kuma idan ’yanci ya yi yawa sai ya koma wani abu kamar hauka.
Aminiya: To, a matsayinki na mace kuma ma’aikaciyar jarida aikin da bai san mace ba, ba hutun karshen mako ba na bikin Sallah ko Kirismeti yaya kike sasanta wannan lamari da batun kula da iyali?
Halima: Farko dai ina yi wa Allah godiya da Ya ba ni miji wanda yake da fahimta sosai, kuma ya fahimci wannan aiki da nake yi, kuma yana taimakawa kwarai da gaske, domin ba sauki a ce kana aiki ga ’ya’ya, ga miji kuma ga aiki, kai ba aikin jarida ba, inda duk aka ce mace na aiki kuma tana da wadannan to gaskiya sai a hankali. Balle namu da aiki ne da bai da lokaci, ba ni mace ba har ku maza ya kamata ku iya tafiyar da lokaci, misali mun san cewa a rana muna da awoyi 24 na san cewa idan na zo ofis zan yi awa takwas, idan na koma gida ga sauran abubuwan da zan yi a ba kowa hakkinsa, idan aka samu fahimta tsakanin maigida da yara, sai ka ga ba wata matsala. Misali yara a kasar nan idan ka yi musu bayani suna ganewa, sun san irin aikin da mamansu take yi, sai ka ga ba matsala.
Aminiya: Shirin da kuke yi da Ibrahim Alfa Ahmed na “A bari ya huce” da kuke yawan barkwanci, shin kukan tattara bayanai ne ko kuna atisayen abin da za ku fada cikin shirin?
Halima: A’a ba wani atisaye ko takarda ba mu shiga da ita sau tari ma sai ya shiga sutudiyo, sai ya bugo waya ya ce Halima ina sutudiyo. Amma ba mu tattauna komai yawancin labaran ko dai labarai ne da suka faru a Nijar ko Najeriya ko masu saurare suka aiko mana, takardar da muke shiga da su wata sa’a su ne na fadin suna ko aure ko wani abin farin ciki ko akasi, amma ba wani atisayen da muke yi.
Aminiya: Shirinki na noma wasu za su ce ai wannan shirin namiji ya kamata a ce yana gabatar da shi, ko kin taba yin noma ne?
Halima: Na yi noma sosai saboda babanmu ya yi gonaki da yawa, musamman kiwo ka san Bafillace ba a raba shi da kiwo da noma. Yanzu haka idan na gama aikin rediyon idan Allah Ya ba ni tsawon rai zan koma in samu wata katuwar gona in noma ta kuma in yi kiwo, ina sha’awar noma da kiwo.
Aminiya: Kina da ’ya’ya, kaddara yau su ce wannan aiki suke son yi mene ne matsayinki?
Halima: Aikin jarida aiki ne mai kyau idan ka tsaya kan gaskiya ba ma aikin jarida ba duk aikin da kake yi, idan ka tsare gaskiya za ka fara lafiya ka kare lafiya.
Aminiya: To, ganin cewar da kika yi ’yancin ’yan jarida ya yi yawa a nan shi ya sa na yi wannan tambaya?
Halima: To, ai mu da muke yi ai ka ga muna la’akari da addininmu da al’adunmu, akwai wasu abubuwa na cin mutunci da ba mu yi wadanda duk da yake muna da ’yancin yi inda za mu yi, domin mutum idan ka yi tunanin karshenka gida za ka koma kuma wadannan mutanen da ka rika gaya musu magana domin kawai kana kasar da ta ba ka ’yanci. Ka san nan ba mu gudun fadin gaskiya, duk wanda ya yi ba daidai ba, ba daga kafa za a fadi gaskiya, amma ciki girmamawa da sanin ya kamata amma ba cikin cin mutunci ba. Cikin ’ya’yana har yanzu ba wanda ya ce yana son yin aikin jarida daga soja sai injiniya, wanda ya ce abin da yake so ya yi ke nan yana iya yi.
Aminiya: Idan aka ce ki ba ’yan jaridarmu na Afirka shawarar yadda za su kyautata aikinsu me za ki ce?
Halima: To, da farko zan ce su yi ilimin aiki, domin mutane da yawa suna dauka cewa aikin jarida aiki ne da kowa zai iya shiga. kwarai kowa zai iya shiga amma idan ya yi ilimin aikin ya san dokokinsa ya san abin da ya kamata ya yi da wanda bai kamata ba. Kamata ya yi a ce akwai wata cibiya da za a kafa bayan wata uku-uku ko shida-shida tana horar da ’yan jarida, domin kullum rayuwar duniya ana ci gaba da kara ilimi, kullum wani abu sabo yake zuwa, ba ka ganin nan koyaushe ana aikowa idan kana son samun horo sai ka rubuta ka je ka yi, to ya kamata su ma ’yan jaridar Afirika su rika samun horarwa a kai-a kai sai aikinsu ya yi kyau. Kuma su rike gaskiya su guji kwadayi domin idan ka ga dan jarida da gidan da ya wuce daya to, a bincike shi, domin aikin jarida ba na yin kudi ba ne na samun martaba ne da farin jini ga jama’a, wanda shi kansa babban jari ne a rayuwa domin idan ka yi fice inda duk ka shiga kowa na son ganinka ko yin hulda da kai. Ba sai an yi ta bin ministoci ko gwamnoni ba, komai kankatar albashinka a samu wadatar zuci, ina kara fadi aikin jarida ba a tara kudi da shi sai arzikin mutane.
Aminiya: Mene ne idan kin tuna a wannan aiki, kikan rika jin dadi?
Halima: Babban abin da ya faranta min rai shi ne yadda nake amfani da wannan aiki wajen taimakon   ’yan uwa a can gida Nijar, domin yanzu duk lokacin da aka nemi wani taimako a gida sai ka ga na iya taimakawa. Ko kafin na zo nan ina taimakawa, duk  da ba  za a hada albashin da ake biyana a Nijar da  na nan ba,  to duk sa’ilin da na tuna wannan sai na ji dadi.
Aminiya: Mane ne a wannan aiki ya taba bata miki rai?
Halima: Abin da ke bata min rai idan na tuna shi ne yadda a wani lokaci can baya lamari ya cakude a nan ofis domin ba jituwa a tsakanin mu ma’aikatan wannan sashi, ya kai akwai lokacin da idan zan shigo   aiki gabana har faduwa yake yi, ba na murna idan zan zo aiki. To duk lokacin da na tuna wannan sai na ji ba na jin dadi, to amma Allah cikin ikonSa yanzu komai ya zame tarihi sai dan abin da ba a rasa ba, domin mutum tara yake bai cika goma ba, amma bayan wancan ba ni da wani abu da nake tunawa ya bata min rai.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya