Aikin Jonathan muke goyon baya ba takararsa ba -Tanko Yakasai

A kwanakin baya ne aka fito da wata kungiya mai suna Majalisar Dattawan Arewa, a karkashinn jagorancin Alhaji Tanko Yakasai, wadda bayan ta kammala taronta a Kaduna ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Jonathan. Aminiya ta tuntubi Tanko Yakasai domin ya yi karin haske game da dalilinsu na nuna goyon bayansu ga Jonathan, bayan wata […]

Aikin Jonathan muke goyon baya ba takararsa ba -Tanko Yakasai

A kwanakin baya ne aka fito da wata kungiya mai suna Majalisar Dattawan Arewa, a karkashinn jagorancin Alhaji Tanko Yakasai, wadda bayan ta kammala taronta a Kaduna ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Jonathan. Aminiya ta tuntubi Tanko Yakasai domin ya yi karin haske game da dalilinsu na nuna goyon bayansu ga Jonathan, bayan wata kungiya mai kama da tasu da ke karkashin shugabancin danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule ta nuna babu ruwanta da Jonathan. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Kwanan nan ne aka ruwaito kun kafa wata sabuwar kungiya a Kaduna, za mu so ka gaya mana sunanta da manufofinta.
Tanko Yakasai: Sunanta Majalisar Dattawan Arewa. Manufofinta su ne hada kan al’ummar Arewa da ta kunshi mabambantan kabilu da yankuna da kuma addini, ya alla musulmi ne ko kirista. Sai kuma karfafa zaman lafiya a tsakanimu da ma jama’ar Kudu don samar da zaman lafiya a kasa baki daya.
Aminya:  Gabanin wannan kungiya akwai wadansu masu take irin nata, ba ka ganin kafa ta zai jawo rabuwar kai a maimakon hadin kai da kuke da’awa?
Tanko Yakasai: Watakila don kwanan nan aka haife ka. Tun a lokacin da marigayi Sardauna yake da rai Arewa take rabe a siyasance da kuma kungiyance. Daga cikin jam’iyyu da kungiyoyi da ake da su akwai NEPU da UNBC da Inorotos Koforafo da Borno Youth Mobement da Kano State Mobement da Zamfara State Mobement da Northern Youth Mobement, akwai Katagum State Mobement, akwai Kilba Tribal Union da dai sauransu. Duk wadannan kungiyoyi ne na siyasa, sai kuma jam’iyya, kuma suna shiga zabe. Amma a yanzu a Arewa jam’iyyu nawa ne ake da su? Ai ba su wuce 3 ba.
Aminiya: Ko kungiyarku na da bambanci da takwarorinta da suka gabace ta, kamar ta ACF da kuma ta su Ango Abdullahi.
Tanko Yakasai: Gaba dayanmu muna karkashin kungiyar ACF ne, wadda ke matsayin bishiya, ta su Ango Abdullahi, wato ta su Maitama Sule da kuma tamu, na matsayin rassa. Mu dai tamu ta yarda tana karkashin ACF, mun yarda ita ce babbar kungiya da duk wata kungiya da ke Arewa ya kamata ta kasance a karkashinta, ba matsayin kishiyarta ba.
Aminiya: Ko akwai shirin yarjejeniya ta hadin gwiwa a tsakaninku don samar da matsaya guda a kan al’amura?
Tanko Yakasai: A halin  yanzu babu. Sai dai kuma da ma ai idan ka ga kungiyoyi sun bambanta, idan kuma ra’ayi ya bambanta, ka ga sai ka yi naka, shi ma wanda ke da bambanci da naka, ya yi nasa. Kuma da ma Allah Ya ce da Ya so sai Ya yi daukacin al’umma iri daya. Haka dai aka bambanta, ra’ayinka daban da na mahaifinka, kamar yadda naka ke matsayin daban da na danka.
Aminiya: kaddamar da kungiyarku ke da wuya, sai ga bayani kun ayyana shugaban kasa Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo a matsayin gwanayenku, wannan na nuna cewa su ne suka dauki nauyinku?
Tanko Yakasai: Ku dai ’yan jaridan zamani malalata ne, ba ku karatu ko bincike. Ni na yi edita. Karanta abu nake yi in kuma bi bayani daki-daki, don gudun kada na ruwaito abun da ba shi ba. Amma tsaya, bari na ba ka takardar jawabin bayan taro da muka fitar, ka karanta da kanka ka ji ko akwai inda muka ambato wannan a cikin abun da muka gabatar.
Aminiya: Na karanta takardun, ga su nan kashi biyu, wanda ka ce shi ne jawabinku na bayan taro, a cikin bayanan akwai inda kuka ce,  “kungiyarku na alkawarin taimaka wa shugaban kasa da mataimakinsa wajen ganin sun samu nasara a al’amura da suka sa a gaba.” Ganin burin sake dawowarsu, bayan kammala wannan wa’adi na daya, na daga cikin muhimman al’amura da ke gabansu, Wannan na nufin abin da kuke bayani akai ke nan, idan zan sake tambayarka zancen kun ayyana su a matsayin ’yan takaranku na matsayin gaskiya ne?
Tanko Yakasai: Ashe ya kamata ka sake yi mini wannan tambaya, abin da ka karanta bai ishe ka amsa ba? To ba zan yi bayanin ba, duk abin da ka ga dama ka je ka fada. Mu dai muna nufin goyon bayansu a aiki, ba a zabe ba, idan ko zaben ne muke nufi ba za mu boye ba, don babu wanda muke tsoro, kuma kamar yadda ka karanta, mun ce za mu taimaki shugaban kasa da mataimakinsa a abin da suka sa a gaba, ba mu ce dan takara da mataimakinsa ba, bare ku ce takara muke nufi, ba aikin da suke yi ba.
Aminya: Yanzu ga shi Arewa ta zama kamar marainiya wajen aiwatar da ayyuka da kuma rigingimu da take fama da su a gefe guda, wane kokari kuke yi a tsakaninku wajen ganin mulki ya sake dawowa a hanunta a nan gaba?
Tanko Yakasai: A cikin kungiyarmu babu shugaban kasa, babu gwamna, babu dan majalisa, su ya kamata ka je ka yi musu wannan tambaya. Sai dai a namu bangaren kamar yadda ka nemi sani, za mu yi iya kokarinmu wajen ganin an samu hadin kai a tsakanin mabiya addinanmu da ke cikin mabambanta kabilun da muke da su, don ganin mun gudu tare, mun tsira tare.
Aminiya: Ko a yau na ga wata jarida da ta ruwaito cewa a karshe Shugaban kasa Jonathan ya samu nasarar farraka Arewa, sun ambato kungiyoyinku, sun kuma ambato wadansu abubuwan daban.
Tanko Yakasai: Ba zan ce komai a kan wannan  ba. Su Bafarawa da Shekarau da suka fita daga wannan sabuwar jam’iyya zuwa PDP, ’yancinsu ne, kamar yadda su ma gwamnoni da suka bar PDP suka koma jam’iyyar a baya, kuma a wancan lokacin ban ji an ce an raba Arewa ba, sai a yanzu. Ai a baya jam’iyyar PDP din nan ta mutanen Arewa ce, saboda a cikinta akwai gwamnoni 23, inda Arewa  ke da 15, ragowar 8 ne kawai daga cikin gwamnoninta daga Kudu, amma a yanzu ba haka al’amarin yake ba.
Shekara biyu da suka wuce na fito na yi yaki da Jonathan a kan kada a takura wa marigayi Shugaba ’Yar’aduwa har ya rubuta takardar sauka daga kan mulki. A lokacin duk jaridunku babu wadda ta goyi bayana. Mutum hudu da muka fara gwagwarmayar tare, haka suka gudu daya bayan daya, na rage daga ni sai Bashir dalhatu. Guda aka ba shi mukami a gwamnati, guda biyu kuma da ke da tabo, aka yi musu barazana, haka su ma suka gudu. Haka dai na je na rubuta wa Majalisar Dattawa takarda na samu shugabansu Dabid Mark na ce batun “doctrine of necessity” babu shi a kundin tsarin mulki su bari, amma ba a goyi bayana ba. Sannan na goyi bayan yaron da ya kai kara a kotu a kan wannan al’amari, haka muka yi ta zuwa kotu har aka gama shari’ar da shi, cikin mutane biyar din nan babu wanda ya je.
Sannan kuma ya tsaya takara ya fafata da Jonathan, ni kadai na zagaya jihohin kasar nan 36 wajen neman masu sa masa hannu, kamar yadda tsarin tsayawa takara ya nuna, aka bar ni ni kadai na zama kamar alu-ja. Sai yanzu ne wani zai zo ya nuna min son Arewa? To ya yi latti.
Aminiya: Ka koka a kan fitar wadansu gwamnoni daga jam’iyyar PDP zuwa wata jam’iyya a matsayin koma-baya ga Arewa, ba ka ganin tsanani ne ya kai ga yin hakan?
Tanko Yakasai: To barin PDP da suka yin ya taimaki Arewa? Ai akwai wadanda suka bari, su ba su fuskancin musgunawar ba, amma ai kishin Arewar ta sa sun ci gaba da jure wa zama a cikin jam’iyyar haka nan. Kai dai bukata ce tasu ta kansu ta sa su ficewa daga PDP zuwa jam’iyyar,  ba ta Arewa ba

Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi

Aminiya ta kuma tuntubi Farfesa Ango Abdullahi, kakakin Majalisar Dattawan Arewa da danmasanin Kano yake jagoranta domin jin abin da zai ce game da bayanin da su Tanko Yakasai suka yi, inda ya yi bayani kamar haka:

Aminiya: Alamu na nuna cewa tsoronku shi ne kada Jonathan ya ce zai wuce da mulki, su Tanko Yakasai da su Yusuf Mamman ga ra’ayinsu daban da naku, Arewa ta rarrabu zuwa ACF da NU da NEF da NUC, to yaya za ku yi tasiri, kuma mene ne bambancin kungiyarku da ta su Tanko Yakasai?
Farfesa Ango: Ka san dattijo daban, tsoho daban, akwai bambanci tsakanin shekaru da yawa da kuma dattaku. Ra’ayinmu shi ne muna son Shugaban Najeriya ya kasance dan Arewa ba mu bambance kabila ko addini ba. Shi kuma Tanko Yakasai ya ce yana son Shugaban kasa ya kasance ba dan Arewa ba, Jonathan yake so, bambancinmu ke nan. Kuma abin da muke gaya wa mutane ke nan.
Aminiya: Yanzu dai kanku bai hadu ba ke nan?
Farfesa Ango: Ka taba gani ko a gidanka kai ya hadu? Domin ko tsakaninka da matarka da ’ya’yanka ana sabawa. Kuma duk inda ka tara jama’a, za ka iske akwai makwadaici, akwai mayunwaci, akwai mayaudari. Wannan ya rage nasu kuma ya kamata mutane su yi alkalanci. Idan mutanen Arewa na ganin ba hakkinsu ba ne su tabbatar da cewa cikin shekara 14 an kware su shi ke nan, idan kuma sun ga cewa za su sake, kamar yadda suka yi a baya, shi ke nan ya rage nasu. Kuma ai sun fadi dalilinsu na cewa ba ruwansu da maganar Arewa, idan kuma talaka bai samu yadda yake so ba, ba yadda zai yi illa iyaka ya yi kokarin gane wa ya damu da shi kuma wa ke kare martabarsa, idan kuma ya dauki ta ’yan bokon ba ni na iya, masu son cika aljifansu, shi ke nan.

Dalilin da ya sa ba za mu halarci taron kasa ba
Aminiya: Kun ce ba ku yarda da taron kasa ba, yanzu kuma har an fara shirya yadda za a tura wakilai, shin kuna nan kan bakanku?
Farfesa Ango: Ra’ayinmu bai sauya ba. Abin da muke cewa shi ne ba ma musun cewa jama’ar kasa su zauna daga lokaci zuwa lokaci, su tattauna kan matsalar kasar, abu ne da ya kamata a yi kuma duk kasashe suna yin hakan. Amma abin da ya kamata a lura shi ne me ya kawo halin da ake ciki game da kiran wannan taro? In ka tuna har zuwa wata shida da suka wuce Shugaban kasa ya tsaya cewa ba za a yi wannan taro ba, ya ce ba ya da amfani ba za a yi ba, mene ne amfanin ’yan majalisa da jama’a suka tura Abuja suke tattauna batutuwan wadanda suke wakilta?
Sai ga shi cikin kankanen lokaci, a bikin cikar mulkin kai na Oktoba, ya ce ya sauya ra’ayi ya kamata a yi wannan taro. Tunaninmu ba abin da ya kawo hakan illa matsin da ya samu, ta fuskar siyasa da kabilanci da addini da ake amfani da su wajen tafiyar da lamuran kasar nan daga kusa da nesa. Su ne suke karfafa masa gwiwar idan ya yi taron, zai samu kubuta lokacin zaben da yake son ya shiga. Ba ma fargaba, idan za a yi abu da kyau. Shi ya sa tun farko muka ce muna so a yi taro mai cikakken iko da zai tattauna kowace matsalar da ta shafi kasar nan, har da cewa kasar za ta iya zama wuri daya ko mun gaji da juna kowa ya kama gabansa, duk a shirye muke.
Aminiya: Mene ne tunaninku kan taron da kuma fa’idar da zai haifar?
Farfesa Ango: Tunaninmu shi ne su wane ne za su halarci taron? Ta yaya za a fito da su kuma wace ajanda za a tattauna a kai? Kafin a yi taro, sai an tabbatar da su wane ne suka damu a yi taron kuma ta wace fuska za tabbatar an ba kowa dama ya tura wakilan da suka dace wurin taron. Don haka a kasa irin wannan, ba za a tabbatar an samu wakilai na kwarai, ba tare da zabe ba. Kwamitin da Shugaba Goodluck ya nada ya kewaya kasa ya zo da shawarar a zabo wakilai biyu bisa uku daga mazabun da jama’a suke. Amma yanzu ba mu san ajandar da suke da ita ba, kan wannan taro illa za a yi ne don Jonathan ya dadada wa mutanensa. Da farko, idan za a yi taron a tabbatar an tsara shi yadda ya dace da wakilan jama’a na gaskiya, amma a halin yanzu abu ne a kudundune, ba batun samar da wakilai na gaskiya cikin lamarin saboda alamu sun nuna Shugaban kasa ne zai nada wakilan da yake so ta hanyar amfani da ’yan barandarsa da suke mulki tare don kare manufofinsa da na jama’arsa, saura ko oho, kuma hakan bai dace ba. Saboda idan ka lura, wannan shekara da muke ciki shekarar zabe ce, kuma ana maganar ta yi taron za a fito da wasu manufofi da za su kawo sauyin tsarin mulkin kasar nan. Alhali wannan batu yana bukatar abubuwa da dama da dokar kasa ta tanada. Kuma maganar da suke kai yanzu ita ce kundin tsarin mulkin da ake da shi bai yi daidai da Najeriya ba, in ba wannan ba wace magana suke yi? Yau aka ce in zo a matsayin Gwamna na bayar da wakili da zai je, ba wanda zan bayar sai yarona da na dora kan ra’ayin ubangidana a siyasance da zamantakewa, kuma zai je ne ba a matsayin wakilin mutane ba, sai dai wakilina kuma wakilin iyayen gidansa. Kuma kowa ya san ba hanyar da ke fitar da wakilai na gaskiya, sai ta hanyar zabe. Don haka babu wani amfanin yin wannan taro yanzu, domin an rubuta wa Shugaban kasa takardu da dama cewa a dage taron, sai bayan an gama zaben badi, kasa ta zauna cikin sukuni, sai a zo a tattauna duk abin da ake so. Kuma idan ya ce sai ya yi, sai ya je ya yi. Sai me? Mu dai za mu zuba ido ya yi abin da yake so, don mun san ba ya da amfani kuma ba abin da zai amfanar. Kuma ku ne ’yan jarida, ba ku gaya musu. Domin a kullum muna rubutawa muna ba su kuma hakkin da ke kanmu ke nan, ku kuma hakkinku bayyana wa mutane mun ce taro bai yi daidai ba.
Aminiya: Kana gani idan ba ku shiga cikin wannan taro ba ana iya barin Arewa a baya?
Farfesa Ango: Ba abin da wannan taro zai kulla kuma a kasar nan ba yadda za a bar Arewa a baya, sai ta ga dama. Ba abin da ba mu gaya wa wakilan Arewa ba, kuma su ma kansu majalisar wakilai daya aka ba su kuma ba irin jawabai da rubutun da ba mu yi ba, wannan taro ba abin da zai haifar. Kuma yadda Arewa ta rabu, haka su ma ’yan Kudu sun rabu, amma namu ya fi muni saboda kullum suna kare muradunsu ne. Don haka ba za mu hana duk mai zuwa wannan taro zuwa ba, mun dai san ba abin da taron zai kulla, sai munafunci ga Arewa.
Aminiya: Ina aka kwana kan batun zuwa kotun duniya kan kisan gillar da aka yi wa ’yan Arewa?
Farfesa Ango: Muna nan kan wannan batu, kuma duk rubutun da ya kamata mu yi, muna yi, muna tara hujjojinmu. Wadanda kuma suka ga sun fi mu sauri su ma ba za mu hana su yin abin da suka yi niyya ba. Ku jira, idan mun je kotu sai ku tarbi bayanan ku ga yadda za su kasance. Kuma duk lokacin da muka gama shiri, za mu shigar da wannan kara saboda mu ne muka kirkiro wannan magana, sai a zuba ido a ga yadda za mu taka rawarmu kuma muna da shaidu. Idan an je shari’a, ba wasa ake zuwa yi ba da hujjoji ake yi. Kuma lokacin da ake wuta a Borno da Yobe da wasu jihohin Arewa, ba abin da ba mu rubuta kan wannan matsala ta cin zarafin ’yan Arewa. Tun Mayun 2012 muka ba Shugaban kasa babbar takarda kan abubuwan da suka damu kasar nan kan tsaro, amma ku ’yan jarida wani lokaci ba ku yi wa lamuran karatun baya.