Aikin likita na so yi, ba na jarida ba – Sahabi Aliyu

Alhaji Sahabi Aliyu, daya ne daga cikin fitattun ma’aikatan gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, inda ya fara aiki da gidan rediyon tun lokacin ana kiransa da Gidan Rediyo da Talabijin na Kaduna, wakilinmu ya samu zantawa da shi a gidansa da ke garin Kalgo, a karamar Hukumar Kalgo da ke Jihar Kebbi, domin jin yadda […]

Aikin likita na so yi, ba na jarida ba – Sahabi Aliyu

Alhaji Sahabi Aliyu, daya ne daga cikin fitattun ma’aikatan gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, inda ya fara aiki da gidan rediyon tun lokacin ana kiransa da Gidan Rediyo da Talabijin na Kaduna, wakilinmu ya samu zantawa da shi a gidansa da ke garin Kalgo, a karamar Hukumar Kalgo da ke Jihar Kebbi, domin jin yadda aikin jarida yake a da da kuma yanzu da sauransu:

Ranka ya dade mene ne takaitaccen tarihinka?
An haife ni a garin Kalgo a Gundumar Gwandu a 1952, na shiga makarantar firamare a garin Kalgo a 1960, bayan na gama a 1967, na wuce sakandaren Birnin Kebbi da ake kira Kwalejin Nagari yanzu, na gama a 1971. Bayan na gama sakandaren sai na rubuta jarrabawa neman shiga jami’a don in yi karatun likita, sai Allah bai sa na ci jarrabawar ba. A rayuwata ba aikin da ya shiga zuciyata irin aikin likita. Ina nan zaune a gida a 1973 sai gidan rediyo talabijin na Kaduna ya dauke ni aiki. Inda aka tura ni na fara aiki shi ne Sakkwato, lokacin ana Jihar Arewa maso Yamma, na zo na karba a hannun Sanda Adamu Tsafe a matsayin wakilin rediyo talabijin Kaduna.
Ina nan Sakkwato a 1975 na samu shiga wata makaranta a Ingila, inda na yi Difloma na shekara biyu kan aikin jarida, kuma gwamnatin Jihar Arewa maso Yamma ta lokacin ta dauki nauyin karatuna, a lokacin ba sai dan wane ba, kuma da ma ni dan jihar ne.
A lokacin ina makaranta ina aiki da BBC, wannan ya taimake ni ga karatuna da kuma yadda ake aikin jarida, musamman ma aikin rediyo. Bayan na dawo daga Ingila a 1978, lokacin ana kokarin a fara siyasar Jamhuriya ta Biyu da ake ce wa siyasar Shagari, a lokacin sai rediyo talabijin Kaduna suka yi tunanin su aika da wakilai a jihohi wadanda za su rika aiko da rahotanni domin wayar da kan jama’a a kan siyasa, musamman mutanen Arewa.
To ina daya daga cikin wadanda aka tura jihohi, sai aka tura ni Sakkwato inda na bari kafin in wuce Ingila, tun a 1978 nake Sakkwato har zuwa 1982. Bayan da aka dauke ni daga Sakkwato sai aka tura ni Kano na shekara biyu, bayan nan sai aka sake tura ni Sakkwato a 1985 har zuwa 1989, a lokacin na kai matsayin babban ma’aikaci. Daga nan sai aka maida ni Legas a matsayin kuma jakada, ni ke kula da wakilan kudancin kasar nan kuma ina aikowa da rahotanni da kuma kowane aiki, in dai ya shafi rediyon Kaduna ni ke kula da shi, shekara hudu na yi a Legas.
Bayan ka baro Legas sai ka fada ina?
Bayan na baro Legas ina Kaduna a 1992, sai Gwamnan farar hula na farko na Jihar Kebbi Alhaji Abubakar Musa Garkuwan Yawuri, ya aiko aka kira ni, na same shi a gidan gwamnati ya ce mani dalilin da ya sa ya aika aka kira ni domin yana son ya yi aiki da ni ne, idan na yarda zai ba ni Sakataren Watsa Labarai na Gwamna, amma in je in yi shawara. Nan take na ce masa to akwai sharudda, na bayyana masa ya ce ya amince. Na ce masa zan je in yi wa gidan Rediyo Najeriya na Kaduna bayani. Bayan na fara aiki da shi, daga bisani sai soja suka karbi mulki aka turo Kanar Tunde Bello a matsayin Gwamnan Soja na Jihar Kebbi, ina nan tare da Tunde Bello sai wata rana ya kira ni daga ni sai shi, ya ce mini zai yi mani canjin aiki zai maida ni Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar a matsayin darakta. Da aka ba ni wannan mukami daga nan sai na fara shirye-shiryen yin ritaya da aiki daga Rediyon Najeriya na Kaduna a cikin shekarar 2007, da kuma daga aiki, domin na yi shekara 35 ina aikin gwamnati.
Da ka yi ritaya ina aka dosa?
Bayan na yi ritaya ina nan gida zaune da gwamnatin Obasanjo ta kirkiro da gidajen rediyo na FM a duk hedikwatar jiha, lokacin za a bude na jihar Kebbi sai Daraktan Shiyya Alhaji Yusuf Nuhu ya kira ni ya ce za a ba ni Janar Manaja na FM da ke Birnin-Kebbi. Sai na ce bayan na bar gidan Rediyon Kaduna, me zai sa ku ce in dawo. Sai ya ce mini an duba cikin Jihar Kebbi da Sakkwato da Zamfara babu wanda ya kai matakin da nake da shi da ya yi ritaya daga Rediyon Najeriya Kaduna sai ni. Bayan ’yan kwanaki kadan sai ga shi sun aiko mini da takardar kama aiki a matsayin Janar Manajan FM na Birnin Kebbi. Amma yanzu kimanin wata biyar ke nan da na ajiye masu aikinsu, har ma sun turo wani sabon Janar Manaja wanda ya canje ni.
Yaya za ka kwatanta aikin jarida a da, da yanzu?
A halin gaskiya ba za ka hada aikin jarida a da, da yanzu ba, saboda ko a da shugabanninmu suna nuna mana mu so aiki mu kuma kare mutuncin inda muke aiki, domin da zarar ka zubar da mutuncinka to har inda kake aiki mutuncin wurin ya zube. Shugabanninmu suna nuna mana duk yadda ka mutunta kanka haka wurin aikinka za a dauke shi. Gaskiya wannan jan kunne da shugabanninmu suka yi mana ya sa mu wakilin da suka tura jihohi mun samu daukaka, kuma Rediyon Najeriya ya samu daukaka fiye da yadda ake zato. Kuma a lokacin muna aiki fiye da yadda ake zato, mutum ba ya tunanin me zai samu, saboda ana ba mu hakkinmu yadda ya dace, ga albashi mai tsoka, domin mun fi yawanci wadansu ma’aikatu albashi, kuma ko da mutum ya tashi daga hedikwatar jihar, ko da da Gwamna ya je wata karamar hukuma domin neman labari za a biya shi nan take da zarar ya rubuta, ba wata gardama. Kuma a lokacin ma’aikaci idan ba a ba shi kayan aiki ba, ba zai je aiki ba, domin akwai kudin sayen kayan aiki kuma ga kayan aikin, jira ake yi wani ya lalace, da zarar ka kai koke nan take za a ba ka wani sabo.
Sai dai kuma a lokacin akwai wahalar aikawa da rahoto domin lokacin babu na’urar kwamfuta, sai dai ka yi amfani da wayar tarho ko ka aika ta mota ka ba direba ya kai ofis. Kuma a lokacin da zarar ka tura labari komai rashin kyansa edita ya san yadda zai yi masa kwaskwarima domin ya shiga, amma yanzu sai dan jarida ya tura labari fiye da biyar amma da kyar guda daya ya fito, saboda su kansu editocin na yanzu suna da wata bukata ta daban. Misali za ka ga idan edita ya fito daga Jihar Kebbi to da wuya jarida ta fito ba ka ga labarin Kebbi ba, komai rashin muhimmancinsa. Lokacin da, idan kana bisa gaskiyarka a matsayin wakilin inda kake, to ba wanda ya isa ya taba ka, komai matsayin mutum, to gidan rediyon ko gidan jaridar da kake wakilta tana ba ka kariya ba wanda ya isa ya taba ka, in dai kana bisa gaskiyarka kuma kana yi masu yadda suke so.
Koda ka yi wani abu wanda ya bata wa wani rai, in dai bisa gaskiyar aikinka ne to wannan gidan rediyo ko gidan jarida zai ba ka cikakkiyar kariya.
A lokacin su dahiru Modibbo da Mohmmed Sulaiman da Mohammed Ibrahim da Ibrahim Ahmed Kwantagora, wadannan mutane suka samu a hanya ta yadda gaskiya muka iya, aikin muke so, kuma ba su taba nuna mana bambanci ko son abin duniya ba. Kullum tunaninsu yaya mutuncin Arewa da shugabannin Arewa za su kasance. Labarun da za a kawo labaru ne na kariyar mutunci ne ko na fallasa ne ga kasa ko ga al’umma, to kullum ana kiyaye da irin wadannan abubuwan. Suna kula da hakkin kowa, ba mai tauye maka hakki, amma yanzu kai ke aiki amma wanda ke zaune a ofis yana shan raba shi ne zai tauye maka hakki, bai san irin kai-da-kawowar da kake yi ba a kullum safe da dare.
Sannan in aiki ne komai wahalarsa sai ka tsaya ka yi shi, ko da aikin nan ya kai rayuwarka ta fada cikin wahala, in dai za a samu abin da zai taimaki jama’a ne.
Kuma shugabanninmu na wancan lokaci sun yi mana horo da babu jin tsoro idan ka tashi game da aikin nan, kuma mutum komai mukaminsa ko shi wane ne, ko da Shugaban kasa ne ka tunkare shi ba wata fargaba. Idan kana hira da mutum ka yi tunanin kai kanka kana iya rike wannan matsayi, ka yi tunanin mutum ne dan uwanka kake hira da shi, kada ka yi tunanin matsayinsa, ka yi tunanin abin da zai fada wa jama’a domin ka watsa wa al’umma.
Kuma a gaskiya yanzu aikin jarida, a wasu fannoni yana da sauki, wasu kuma babu sauki, amma rashin dadinsa ya fi yawa, dadinsa yanzu samun saukin aikawa da labari a cikin sauri da kuma sauti mai kyau.    
Domin akwai hanyoyi masu sauki na aikawa da rahoto ba kamar da ba; sai dai yanzu an fi kashe kudi wajen aikawa da labarai.
Kuma yanzu ba aika shi ke da wahala ba, nemo labarin ya fi wuya, misali yanzu dan jarida zai je ofishin wani ma’aikacin gwamnati ko na dan siyasa ya ce yana son ya ji wane irin matsaloli ne ma’aikatarsa ke fuskanta, ko wane irin ci gaba aka samu, ka ga duk tambayar babu wata fallasa, amma sai ka ji ya ce maka babu komai ko kuma ya ce an hana mu hira da ’yan jarida.
Amma da zarar ka ce wane irin godiya za ka yi wa gwamna a kan ayyukan da yake a fadin jihar nan, sai ka ga kafin ka fidda kayan aiki har ya fara bayani. Amma ka tambayi dukiyar jama’a da yake shugabanta ya yi bayanin nasarorin da aka samu ko matsalolin da ke akwai domin a yi wa al’umma bayani ko akwai wata shawara da wani zai ba da domin ci gaban wannan ma’aikata da yake jagoranta ya ki.
Kuma dan jarida yanzu ba a ba shi hakkinsa, kuma yana fama da rashin kayan aiki, kafafen watsa labarai kalilan ne suke ba ma’aikatansu kayan aiki, ko ka ga idan rekoda ne ko kyamara sai wani ya dawo aiki ya a je, sannan wani ya dauka ya je aiki. Masu aiki a ofis ke nan, amma wakilai na waje za ka ga dan jarida ba ya da kyamara ba rikoda ba na’urar kwamfuta ta aika labari, ta yaya dan jarida zai yi mutunci inda ya je nemo labarai?
Yawancin ’yan jarida saboda ba a mutunta aikin da wurin da kake wa aiki, sai ka ga dan jarida da wayar hannu yake hira da mutum, wata wayar ko dauka ba ta yi, ka ga ba mutunci, kuma wurin da kake wakilta ba ka mutunta su ba.
Duk wannan laifin wurin da suke wa aiki ne, domin su ne ba su ba da kayan aiki da hakkin da ya kamata, shi ke sa suna bin hanya ta rashin gaskiya, sai ka ga dan jarida yanzu kamar almajiri, domin ta haka ne zai rayu, shi ke daukar nauyin kansa ya biya kudin hayar gida ya sa wa motarsa mai domin zuwa nemo labarai, idan babu ya hau acaba ko keke NAPEP.
Aikin jarida aiki ne mai wahalar gaske rago ba ya aikin, yana son naci da jajircewa, mai yin sa ba ya tunanin  ya yi kudi. Maimakon a yi wa dan jarida tanadi mai kyau ta yadda zai kauce wa shiga wata hanya marar kyau, saboda dan jarida tamkar alkali ne, idan alkali ba ya da wadata dole ya ci hanci. Shi ya sa hukuma ke ba alkalai albashi mai tsoka da zai kare mutuncinsu, to haka ya kamata a yi wa ’yan jarida idan ana son su tsare gaskiya. A yi masu tanadi na kwarai ta fuskar biyan bukatarsu da kuma kayan aiki, domin su kare kasa da al’ummarta.
Aikin jarida ya tanadi son aikin da jajircewa, dogon karatu ba shi ne aikin jarida ba, domin ka gan ni nan ban taba shiga jami’a ba, amma kuma ka dubi matsayin da na rika a aikin jarida, za ka ga wanda ya yi digiri amma wanda ya yi sakandare ya koya masa aikin domin dadewa da basirar da yake da ita a aikin.
Wace shawara za ka ba ’yan jaridar yanzu?
Sahabi Aliyu: Shawarar da zan ba ’yan jarida ita ce su kare kansu da al’ummar kasar da kuma inda suke wakilta, kodayake yanzu kafafen watsa labarai sun yi yawa, amma mun sani wasu an kafa su ne saboda wata biyan bukata ta kashin kai ko ta siyasa ko ta addini ko yanki ko kabilanci. Duk ta fuskar da mutum ya kafa gidan jarida ko rediyo ta wannan bangaren zai karkatar da ma’aikatansa domin bukatarsu ta biya. Masu yi don kasa da al’ummar kasa ’yan kalilan ne. Wallahi idan ka ga wani labari a wasu jaridu ko kare ba ya ci.
Ranka ya dade matanka da ’ya’yanka nawa ?
Ina da mata  biyu da ’ya’ya 22.