Aikin mai shawara bai baci
Akan ce aikin mai shawara bai baci sai dai rashin rufin asiri. Irin abin da ya faru ke nan ga Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honorabil Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya yi tsallen badake daga jam’iyyarsa ta PDP, ya tsunduma cikin ta APC, ya kuma nemi tsayawa takarar shugabancin kasa, amma sai ga shi ya […]
Akan ce aikin mai shawara bai baci sai dai rashin rufin asiri. Irin abin da ya faru ke nan ga Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honorabil Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya yi tsallen badake daga jam’iyyarsa ta PDP, ya tsunduma cikin ta APC, ya kuma nemi tsayawa takarar shugabancin kasa, amma sai ga shi ya yi kyawun kai, tun ya tuntubi na gaba da shi, wadanda suka shawarce shi cewa kada ya yanko lomar da ta fi bakinsa, ya bari tukuna sai kundunsa ya kara karfi. Saboda haka nan an ce yanzu takarar Gwamnan Jihar Sakkwato zai yi.
Yanzu dai wannan al’amari ya zamanto tarihi, amma irin wanda ba za a yi saurin mancewa da shi ba, sai an ga yadda ta kaya. An dai ce banza ba ta kai zomo kasuwa, da dalili. Mutane da yawa sun rantse, wasu ma sai da suka saba laya sa’ilin da suka hakikance cewa wadanda ke kokarin tadiye Arewa ne, don su kai ta kasa, kada ta yi tasiri, ko don tsira daga sharrin ‘yan Kudu da ‘yan barandarsu a Arewar, suka ingiza Aminu Tambuwal fitowa neman takara a jam’iyyar APC, don dai kawai ya yi wa wadanda suka rigaya suka sha gabansa kancal ko kafar ungulu. Idan ba domin akwai wadanda suka daure masa gindi ba cikin jiga-jigan da ake gani su ne shugabannin Arewa, wane mutum, in ji mutuwa? Ai wasan kokouwa ba guragu ne ba.
To, ya amince da hujjar da madaura suka ba shi na cewa shi ba dan tatsitsi ne ba, kuma shi ba dandagajin siyasa ne ba, wuyarsa ta isa yanka, saboda haka nan yana iya fitowa a fafata, domin a ganinsu ai ko tsakanin dutse da kwai ma ana yin karo. E, ba makawa ana iya yin karon, amma fa sau guda za a yi, daga nan kowa zai san matsayinsa. Shi ya sa bayan mahankalta, manazartar al’amuran siyasa sun ba shi shawara sai Tambuwal ya ga ashe da can ya so ne ya yi kamun gafiya irin ta |aidu wanda ya saki ta hannu, ya bi ta guje, daga karshe ya yi batan-bakatantan Ya gane cewa masu yi masa ingiza-mai-kantu-ruwa dai so suke su zuga gwaiwa ta hau kaya don ta tsiyaye a banza. Shi da kansa ya ga tilas ne a matsayinsa na tatsitsin ]an siyasa ya tsaya a matsayinsa, kada yaba zai bari zancen ‘yan duniya ya rude shi ba.
Da farko dai an danganta ficewar Tambuwal daga PDP da burinsa ne na yin takarar gwamna a APC, amma sai ga shi nan ya yi azarbabiyar da aka tabbatar ba za ta haifa masa da mai ido ba. Kaman yadda gwamnonin jam’iyyar APC, na jihohin Yarbawa suka fayyace jim kadan bayan Tambuwal ya fitar da maitarsa a fili, ba za su amince da shi ba, musamman ma saboda ganin cewa shi maciji ne wanda bai yi kansa ba, sai anda aka haka, ya llabo, zai shige abinsa. Baicin haka nan kuma suka ce kashinsa bai yi kwari ba a siyasance, saboda haka nan ta yaya za a aza masa kayan da aka tabbatar baras wa zai yi, ba zai kai inda aka aike shi ba? Wadancan gwamnonin sun yi amanna cewa ko da Tambuwal ya samu tikitin takara a jam’iyyar APC ba zai iya yin galba kan Shugaba Jonathan ba, domin ruwa ba sa’an kwando ne ba.
To irin abin da makiya Arewa ke so ke nan, wato su cicciba wani jigari-jigari yin takarar shugabancin kasa daga yankin, a maimakon wani mai gwabi, wanda idan har aka fafata da shi, aka samu naman dafawa, shi ma zai samu na gashi. Abin da ake bukata a Arewa shi ne da, guda kwakkwara, ba yuyuyun da aka tayar da su da rana-tsaka don takawa na kwarai burki ba.
A takaice dai ana so ne a samu wanda zai iya cin zabe, ya kuma kafa ingantacciyar gwamnatin da za ta kawo canjin da aka dade ana nema, sa’annan kuma jam’iyyarsa ta samu rinjayen wakilai a majalsun kasa da kuma gwamnoni don ta magance kisisina da kutungwilar da ake yi wa jama’a. Dangane da haka Janar Muhammadu Buhari ne ake gani zai iya huce wa jama’ar Arewacin kasar nan takaici game da haka.
Dalili kuwa shi ne a shekarar 2011 shi da jam’iyyarsa ta CPC sun shige wa jam’iyyar PDP hanci da dukunkune, yayin da suka hana ta samu rinjayen da ta saba samu a majalisun kasa a shekarun 1999, 2003 da kuma 2007, kuma hakan ya zamanto mata nakasun da ya hana ta yin rawar gaban hantsi a siyasance da kuma hana mata damar daukan munanan matakan can-canja yanayin al’amura don muzgunawa wasu jinsi da kuma hana su cin gajiyar arzikin kasarsu. Babu makawa jam’iyyar PDP da kuma wasu shugabannin Arewa da suke daure wa karya gindi ba za su so ganin jam’iyyar APC ta tsayar da dan takarar da zai sa ta samu wakilai da yawa a majalisun tarayya da kuma gwamnonin jihohi a 2015 ba domin kada kutungwilar da suka yi na canja kundin tsarin mulkin da aka kitsa a taron kasar da aka yi a bana ya sha ruwa, sababbin majalisu da gwamnoni su ki amincewa.
Dangane da haka ana iya cewa wajibi ne tsoffin shugabannin kasa, ‘yan asalin Arewa, walau na soji da kuma na farin hula da sarakuna da manyan malaman addinin Musulunci su fito fili, kiri-kiri, su nisanta kawunansu daga yunkurin da ake zargi suna da hannu a ciki na dakile dan takarar da aka yi amanna shi ne zai iya kai Arewa gaci a zabe mai zuwa. A yanzu dai alamu sun nuna cewa goyon bayan Jonathan suke yi a kaikaice. Idan kuma har suka ki dagewa su nuna goyon bayansu ga daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasa daga Arewa, to ba za a yi kuka da kowa ba sai da su, domin kuwa al’ummarsu za su shiga cikin matsanancin tasku, za su ga wulakancin da ya fi na yanzu, sa’annan za su dawwama cikin gagarumar wahalar da za ta sa su gwammace mutuwa da rayuwa. Allah Ya saukake.