Aikin majalisa ba na sabon-shiga ba ne – Buba Kalallawa
Aminiya: Me ya jawo hankalinka ga neman kujerar Majalisar Tarayya duk da kana dan majalisar jiha?Buba Kalallawa:To alhamdulillah a gaskiya kamar yadda ka sani cikin ikon Allah bayan zaben bara, Allah Ya yi ’yar majalisarmu ta tarayya Hajiya Khadija Bukar Abba ta samu matsayin Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje inda kujerarta ta zama ba kowa […]
Aminiya: Me ya jawo hankalinka ga neman kujerar Majalisar Tarayya duk da kana dan majalisar jiha?
Buba Kalallawa:To alhamdulillah a gaskiya kamar yadda ka sani cikin ikon Allah bayan zaben bara, Allah Ya yi ’yar majalisarmu ta tarayya Hajiya Khadija Bukar Abba ta samu matsayin Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje inda kujerarta ta zama ba kowa dole a cike gurbi. To sai Hukumar Zabe ta kasa sanar da cewa za a yi zaben cike gurbi, don haka bisa fafatawar da muka yi a baya da kuma kiraye-kiraye da jama’ata daga kananan hukumomin hudu na in fito don neman wannan kujera ne ya sa na fito takarar.
Aminiya: Yaya aka yi ka kasance a Majalisar Dokokin Jihar Yobe a matsayin wakilin Wajen Damaturu har sau biyar?
Buba Kalallawa: To ka san dukan zababben wakilin al’umma muddin mutane suka fito suka ce ka zo ka tsaya musu takarar wani matsayi, to ba ka da zabi illa ka amince da bukatarsu. Kuma ita siyasa mun fara tsunduma cikinta ne a shekarar 2002 a zaben cike gurbi sakamakon rasuwar babanmu tsohon dan majalisarmu ta Wajen Damaturu Alhaji Idris Kalallawa wanda shi ne tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Jihar. Allah da ikonSa sai mutane suka aminta in zo don tsayawa a zaben cike-gurbin hakan kuwa aka yi, da aka yi zabe sai Allah Ya ba ni nasara. Sirrina shi ne zaman lafiya da kokarin yin aikin raya kasa ga al’ummata, kamar samar da ruwan sha da ba da wutar lantarki da ba da tallafi ga harkokin ilimi da kokarin samar wa matasa aikin yi da makamantansu. Wannan shi ne sirrin dadewata a majalisar, kuma aikin majalisa ya zama tamkar jini da tsoka a gare ni.
Aminiya: Wane tabbaci za ka bayar ga mutanen mazabarka game da yi musu wakilci nagari?
Buba Kalallawa: To kamar yadda kowa ya sani aikin majalisa Allah Ya sa muna da kwarewa, ba sabon yankan rake ba ne, tsohuwar zuma ce. Kuma akasari dokoki irin na majalisar jiha da muke amfani da su, kusan ire-irensu ne Majalisar Tarayya ke amfani da su. Ina ganin insha Allahu ba zai zama mana matsala ba. Don haka ina ba da tabbaci ga al’ummar mazabata cewa, matukar suka zabe ni don wakiltarsu a Majalisar Tarayya, ba za su yi nadama ba domin kuwa za mu gudanar musu da ayyukan raya kasa tare da faranta musu rai musamman ganin cewa mazabata yanki ne da al’ummarsa suka fi dandana kudarsu a rikicin Boko Haram.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga ’ya’yan jam’iyyarku ta APC game da zaben share-fagen don a samu a gudanar da shi cikin natsuwa?
Buba Kalallawa: Abin da zan ce shi ne, ko wane ne zai yi zabe, akwai bukatar ya yi la’akari da abin da zai zaba domin rayuwarka da ta ’ya’yanka da yankinka. A kauce wa zaben tumun-dare da zai jefa iyalanka da yankinka cikin matsala. Kuma mutane su zama masu bin doka da oda domin duk abin da za a yi, a yi bisa bin tsari na doka tare da hada kai, kuma ina fata a bari a gudanar da zabe na gaskiya.