Aikin samar da kamfanin lantarki na Jihar Sakkwato ya kai kashi 98 –Gwamnatin Sakkwato
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce aikin samar da wutar lantarki da ya shafe sama shekara goma ana yi ya kai matakin karshe na kammalawa, inda nan ba da jimawa ba za a fara more aikin da gwamnatin ta gada daga Gwamnatin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko. Kwamishinan Makamashi da Albarkatun Man Fetur Alhaji Aliyu Balarabe Dandin-Mahe […]
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce aikin samar da wutar lantarki da ya shafe sama shekara goma ana yi ya kai matakin karshe na kammalawa, inda nan ba da jimawa ba za a fara more aikin da gwamnatin ta gada daga Gwamnatin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
Kwamishinan Makamashi da Albarkatun Man Fetur Alhaji Aliyu Balarabe Dandin-Mahe ne ya sanar da haka a wajen taron kara wa juna sani karo na biyu da wani dan kishin jihar Injiniya Zayyanu Tambari Yabo ya shirya mai taken ‘Makamashi ga Ci gaban Kasa’, inda ya ce aikin samar da kamfanin wutar lantarki mallakar jiha ya kai kashi 98 na kammalawa kuma za a kaddamar da aikin a farkon badi.
Kwamishinan ya ce gwamnatinsu ta himmatu kan harkar makamashi domin sanin amfaninsa inda ta samar da rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana a wasu kauyukkan jihar.
A wurin taron, Injiya Zayyanu ya bayyana dalilin kiran taron, inda ya ce “Muna godiya ga mahalarta taron karo na biyu kan yadda suka karbi gayyatar, abin ya kara min karfin gwiwa a kan wannan kudiri nawa. Mun fito da wannan tunani ne domin mu bai wa al’umma dama su samu wata kafa ta tattaunawa da masana domin ci gaban jama’armu game da lamuran yau da kullum,” inji shi.
“Daular Usmaniyya an kafa ta ce kan ilimi, don haka dole ne mu ci gaba asassa asalinmu don ci gaban jiharmu. Kamar yadda muka yi, na gayyato masana daga wurare daban-daban a tattauna kan makamashi da ci gaban kasa, haka za mu ci gaba da tattaunawa kan ci gaban al’umarmu har a samu nasara,” inji Injiniya Zayyanu.
An tattauna kan lamura da yawa a fannin makamashi da ba su kamata a rika wasa da su ba a gefen gwamnati da jama’a da suka kunshi gane cewa makamashi yana da matukar muhimmanci ga rayuwar mutum, kuma akwai bukatar matasa su shiga harkar bunkasa makamashi don ba da ta su gudunmkwa da sauransu.