Ainihin abin da Gwamnan Kano suka tattauna da Nuhu Ribadu
Majiyoyi a fadar shugaban kasa da gwamnatin Kano sun bayyana ainihin abin da aka tattauna a ganawar sirrin tsakanin Gwamna Abba da Nuhu Ribadu
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro Malm Nuhu Ribadu hakuri kan zargin shi da gwamnatin jihar ta yi da tsoma baki a rikicin Masarautar Kano.
Gwamna Abba da bakinsa ya ba wa Nuhu Ribadu hakuri a lokacin ziyarar da ya kai ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro da ke Abuja a ranar Alhamis.
Ganawar sirrin ta faru ne kwanaki shida da Gwamnatin Abba nada Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano, bayan ta tube Sarki Aminu Ado Bayero.
Gwamna Abba ya yi haka ne bayan ya sanya hannu kan sabuwar dokar masautun jihar da majalisar dokokin jihar ta yi wa kwaskwarima.
Gwamnan ya kuma ba sa wa’adin awa 48 ga sarakunan jihar biyar da sabuwar dokar ta tube su fice dafa fadar masarautun.
Daga baya gwamnan ya ba jami’an tsaro umarnin tsare Sarki Aminu Ado Bayero wanda bayan ya dawo Kano, ya kuma tare a Fadar Nassarawa.
Hakan ya sa aka girke jami’an tsaro a fadar, lamarin da ya haifar da zargin goyon bayan Sarki Aminu daga Gwamnatin Tarayya.
Ana iya tuna cewa Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdulsalam Gwarzo ya zargi Nuhu Ribadu da hannu da kuma taimaka wa Sarki Aminu Ado Bayero da rakiyar jami’an tsaro.
Amma Ribadu ya nesanta kansa da lamarin tare da barazanar maka shi a kotu idan bai janye zargin ba.
Mataimakin gwamnan dai ya janye zargin tare da ba wa Nuhu Ribadu hakuri, yana mai cewa kuskure aka samu a bayanan da gwamnatin jihar ta samu a kan lamarin da ya haifar da zargin.
Duk da cewa Gwamna Abba ya bayyana ganawar sirrin da suka yi da Nuhu Ribadu, wani mai kusanci da ganawar ya shaida mana cewa gwamnan yana ganin cewa duk cewa hakurin da a ba wa Ribadu ta kafofin yada labarai kadai bai wadatar ba, ya kamata ya yi masa magana da kansa kan abin da da faru,
“Da Hausa Abba da Nuhu Ribadu suka tattauna inda ya ba Ribadu hakuri kan maganganun mataimakinsa na makon jiya.
“Gwamnan yana ganin hakurin da aka bayar a kafofin yada labarai bai wadatar ba, shi ya sa ya zo Abuja da kansa,” in ji majiyar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tabbatar da ziyarar gwamnan da kuma ban hakurin ga Nuhu Ribadu.
Sanusi Bature ya kara da cewa gaanawar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Ribadu ta mayar da hankali ne kan halin da ake ciki na dambarwar Sarautar Kano tun bayan rushe masarautun jihar da aka yi da kuma dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II.
“Lura da kwarewa, mutunci da kuma kimar Ribadu ta sa gwamnatin jihar ta ga dacewar janye zargin tare da ba shi hakuri,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito cewa al’ummar Kano na ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda suka saba a yayin da ake cika mako guda da dawo da Sarki Sanusi II.
A yayin da wakilan Darikar Tijjana suka yi mubaya’a gareshi, Aminiya ta ruwaito cewa har yanzu akwai jami’an tsaro a zagaye da fadarsa ta Kofar Kudu da kuma karamar Fadar Nassarawa da Sarki Aminu yake, kuma jama’a na ci gaba da harkokinsu babu wata fargaba.