Ainihin dalilin da aka kori Gombawa Motors daga tashar gwamnatin Gombe
An samu korafe-korafe da dama daga sauran masu gudanar da kasuwanci a tashar kan ayyukan kamfanin.
Kamfanin Principal Facilities Management Limited da ke kula da gine-gine ya bayyana cewa an kori kamfanin Gombawa Motors Nigeria Limited daga babbar tashar motoci ta Ibrahim Dankwambo Mega Park da ke Gombe ne bisa zargin take dokoki da ƙa’idojin gudanar da ayyuka a tashar.
A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 25 ga Yuni, 2026, wadda aka aika wa shugaban kamfanin Gombawa Motors, kamfanin mai kula da gudanar da tashar ya ce matakin ya biyo bayan ƙudurin Kwamitin Kula da Ibrahim Dankwambo Mega Park da aka cimma a ranar 25 ga Yuni.
- Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin Sojin Amurka a Bahrain da Kuwait
- ’Yan bindiga sun kashe limami da wasu mutum 3 a Sakkwato
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan an lura cewa Gombawa Motors na ci gaba da karya dokoki da ƙa’idojin da aka amince da su wajen gudanar da ayyuka a tashar.
Har ila yau, wasiƙar ta ce an samu korafe-korafe da dama daga sauran masu gudanar da kasuwanci a tashar kan ayyukan kamfanin, waɗanda suka yi zargin ya yi watsi da ƙa’idojin aiki da aka shimfiɗa domin tabbatar da tsari da adalci a cikin tashar.
Kamfanin Principal Facilities Management ya ce, sakamakon saɓawa ƙa’idoji kuma bisa ƙudurin kwamitin kula da tashar, an kori Gombawa Motors daga tashar ta Ibrahim Dankwambo Mega Park.
Sanarwar ta umurci kamfanin da ya fice daga harabar tashar cikin awa 24 da karɓar wasiƙar.
A cewar kamfanin, an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da inganta gudanar da ayyuka a tashar, tare da umartar Gombawa Motors da ya bi umarnin ba tare da ɓata lokaci ba.
An kuma aika kwafin wasiƙar zuwa kamfanin haraji na Gombe Revenue Optimization Company Limited (GROCOL), shugaban Kwamitin Kula da tashar Ibrahim Dankwambo Mega Park, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Darakta na Hukumar DSS ta Jihar Gombe, da kuma Kwamandan Hukumar Sibil Difens na Jihar Gombe.