Ainihin dalilin tsadar albasa a Nijeriya
Na je saya a kasuwa, amma na dawo ban saya ba, tsadar ta yi yawa. Albasa ’yar kaɗan sai ka ji ana maganar dubbai.”
Karin maganar nan da ke cewa ‘kar a yi tuya a manta albasa’ tana neman rasa ma’anarta, sakamakon halin da mutane ke ciki, inda sayen albasa domin girki ke neman gagarar iyalai.
Mutane da dama da suka je kasuwa da niyyar sayo ta, sun ce sun haƙura, wasu kuma sun ƙare da sayen abin da za a ce, a gashe ba mai a dafe babu romo.
“Na je sayen albasar da zan yi wa iyalina tsaraba a inda na je hutu a Arewa, amma na ga ta yi tsada, har fasa sai ɗan kasuwan ya ce in daure in saya domin ana ganin zuwa watan Janairu za ta qara tsada,” in ji Malam Abdulrahman Suleiman.
Za mu daina girki da ita:
Mis Rosemary Andrew ta shaida Aminiya cewa, “yanzu albasa ta fi komai tsada a cikin kayan abinci. Na je saya a kasuwa, amma na dawo ban saya ba, tsadar ta yi yawa. Albasa ’yar kaɗan sai ka ji ana maganar dubbai.”
- NAJERIYA A YAU: Haɗarin da ke tattare da aiwatar da kasafin kuɗi biyu a lokaci guda
- Manufofina sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya — Tinubu
Malama Salma, ta ce, “kashin albasa ƙwara uku Naira 500. Ta N1,500 na saya na haƙura.”
“Abin ya ɗaure min kai, sai mu haqura yadda muka yi lokacin da dankalin turawa ya yi tashin hauka. Yo ina dalili? Ai babu dole, albasa sai ka ce nama,” in ji Malam Muhammad na Abubakar, cikin fushi.
Wani magidanci a Abuja, Malam Nura Ibrahim, ya ce, “yanzu Naira dubu 13 ake sayar da albasa cikin ƙaramin kwandon shara. A haka ma ana ganin nan gaba tsadar za ta ƙaru.”
Malam Ibrahim Mohammed, wani ma’aikaci a Abuja, ya ce da ya yi bulaguro iyalinsa sun kira suna masa kukan tsadar albasa, ko zai samu da sauƙi a Kaduna ya zo musu da ita. Ya ce, “Da na ji kuɗinta a inda nake, sai na kira na ce musu kawai su saya a can. Ta yi tsadar, ga wahalar ɗauko ta.”
Da yake magana kan tsadar albasar, Mista Chukwuemeka John, ya ce, “mutanenmu a Kudu su saba da tsadarta, ƙwara uku N2,000. Amma idan a Arewa da ake noma ana kukan tsadarta, to mutanenmu fa? Yanzu wani lokaci ni ke tura musu ita ko kuɗin daga nan Arewa.”
Ainihin dalilin tsadar
A yayin da magidanta ke kokawa kan tsadar albasar, masu kasuwancinta sun buƙaci tallafin gwamnati bisa yanayin da aka shiga na ƙarancinta da kuma tashin gwauron zabon da ta yi a bana.
Mai unguwar Yusuf Abdullahi, manomin albasa wanda ya kwashe shekara kusan 45 yana dillancinta, ya yi wannan kira ne a yayin da yake bayyana wa Aminiya ainihin abubuwan da suka haifar da tsadar albasa da kuma ƙarancin nata a bana.
Mai Unguwa Yusuf da ke kasuwancin albasa a Zariya, Jihar Kaduna, ya bayyana cewa tsadar takin zamani da na man fetur da na sauran kayan noma sun taka muhimmiyar rawa wajen tsadar albasa a wannan lokaci. Sa’annan uwa uba, ambaliyar ruwan sama da aka samu a jihohin da aka fi noman ta.
Ya ce, “sanin kowa ne ana noman albasa ne a lokacin rani da damina kuma tana da matuqar amfani ga rayuwar ɗan Adam.”
Acewarsa, “babban dalilin da ya ƙara haifar da ƙarancin albasa da tsadarta a wannan karon shi ne yadda wasu daga cikin jihohin da ake noman ta suka haɗu da matsalar ambaliyar ruwan sama, musamman jihar Borno da Yobe da Jigawa da sauransu kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da albasa.”
Ya bayyana cewa manyan garuruwan da aka fi noman ta da samar da ita su ne “Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Jigawa da Yobe da kuma Jihar Filato. Sai kuma wadda ake shigowa da ita daga maƙwabtanmu ƙasar Nijar.”
Mai Anguwar ya ce, “a lokutan baya farashin buhu ɗan solon nan baya wuce Naira dubu 25 zuwa Naira dubu 30 a nan Zariya da yake mu da shi muke amfani.
“A yanzu kuwa shi babban buhun suna sayo shi ne a Sakkwato a kan kuɗi Naira dubu 260 zuwa 270 a kan kowane babban buhu, sannan ga kuɗin mota ga kuma ɗan wahalhalu da ake yi kafin a iso.
“Sai kuma manyan ƙalubalen da suka fi shafar noman albasa su ne, akwai tsadar taki da kuma tsadar man fetur wadda masu noman ta da rani ke fuskanta.”
Saboda haka ne Mai Anguwa Yusuf Abdullahi ya miƙa ƙoƙon bararsu ga masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati su waiwayi masu moman albasa ta hanyar ba su tallafi domin gudun fuskantar ƙarancinta a nan gaba.
Haka nan kuma ya shawarci masu samarwa da sayarwa da su himmatu wajen inganta sana’arsu tasu.