A’isha Adamu Minjibir: Kada a yi karya don tsoro

Hajiya A’isha Adamu Minjibir ita ce shugabar kamfanin sufurin yawon bude ido na Ashmin trabels, ta yi aiki a bankin Arewa, ta koyar a makarantar sakandaren ’yan mata da ke danbatta a Jihar Kano. Ta ce kada a yi karya don tsoro. TarihinaSunana A’isha Adamu Minjibir, an haife ni a karamar Hukumar Bichi a Jihar […]

A’isha Adamu Minjibir: Kada a yi karya don tsoro

A’isha Adamu Minjibir	Hajiya A’isha Adamu Minjibir ita ce shugabar kamfanin sufurin yawon bude ido na Ashmin trabels, ta yi aiki a bankin Arewa, ta koyar a makarantar sakandaren ’yan mata da ke danbatta a Jihar Kano. Ta ce kada a yi karya don tsoro.

Tarihina
Sunana A’isha Adamu Minjibir, an haife ni a karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano. Na yi firamare a Giginyu Primary School Kano. Daga nan sai na je Kwalejin gwamnatin ’yan mata (GGC)ta  Dala. Na karanta tarihi a Jami’ar Bayero Kano. Na yi hidimar kasa a Kano, inda na yi aiki da bankin ‘Tropical Commercial Bank’ a Kano. Bayan na gama hidimar kasa sai na fara aikin koyarwa. Na koyar a makarantar da ake kira Shahuci, makaranta ce ta yada addinin musulunci da koyar da Larabci. Na koyar da darasin Tarihin Musulunci (Islamic History) a makarantar har na zama shugabar wannan fannin (HOD). Na koyar tsawon shekara uku, daga nan  na zamo mataimakiyar shugaban sakandaren ‘yan mata (GGSS) ta danbatta. A nan kuma na yi aikin wata shida zuwa tara.
Daga nan sai na koma aiki a bankin Arewa (Bank of the North), inda kuma aka kai ni Legas. A lokacin mutane ba sa son zuwa wani wuri. A lokacin mu kalilan ne muka tashi daga Kano zuwa Legas. Nagode wa Allah da Ya ba ni damar aiki a Legas, saboda idan ka yi aiki a inda ba mazaunarka ba za ka ga cewa ka bar jama’arka ka shiga sabon wuri, al’adunku daban, yarenku daban. Har sai ka zauna ka fahimce su. To a hankali wannan ya sa na iya zama da mutane. Na yi tsawon shekaru shiga a Legas, sai aka dawo da ni Abuja. Ina zuwa Abuja sai na dauki hutu na koma Jami’ar Jos na yi digiri na biyu a kwas din dokar kasa-da-kasa da kuma diflomasiyya (International Law and Diplomacy) na shekara daya. Sai na dawo na ci gaba da aikin banki. Ina cikin aikin ne sai na yi tunanin aikin banki za ka ritaya ko kuma ya bar ka. Idan ka yi ritaya me za ka yi? Ina cikin nazarin, sai na rika duba intanet ko zan samu abin yi. Tun da aikin banki akwai gajiya, sai na yi tunanin kan yadda mutane za su rika shakatawa, yadda za su huta ba sai ka bar kasarka ba. Kuma hutun nan ba sai da kudi mai yawa ba. To shi ne na yi tunanin bude kamfanin Ashmin Trabels and Tours, daga nan na yi masa rajista domin sayar da tikiti don masu yawon bude ido a Najeriya ko a waje.  Akwai wani wuri a Jihar Jigawa da muka gano ana kiran wajen ‘Baturiya’ wannan wuri ne wanda akwai tsuntsaye daban-daban na duniya. Amma da yawan mutane ba su san da wurin ba. Da gwamnati za ta gyara wurin ba sai an fita waje don kashe kudade da yawa ba. Da tsohon Gwamnan Babban Banki Najeriya, Soludo ya ce ya kamata bankuna su hade, shi ne ni ma na ce lokaci ya yi da zan bar aikin banki, ni ma na nemi nawa. Alhamdulillah ga shi na bude ofishin nan kuma ina da ma’aikata shida.
Abin da ya taba faruwa da ni a lokacin da nake karama
Ina da shekara 18 mahaifina ya rasu. A duk duniya babu abin da na fi kauna kamar mahaifina, saboda ya rike kowa da kowa. Da malami ne sai ya karanci shari’a ya zama lauya. Har yanzu idan ina magana na ce ni ce wance, sai mutane sun yi addu’a kafin wani abin ma su taimaka mini da shi. Na waje ke nan ma balle mu na gida. Nakan kwanta da shi kuma na tashi da shi. Sai dai yadda aka ce Allah ne mai bayarwa kuma mai daukewa. Kullum in na tuna, sai na ce ‘Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un’. A gaskiya abu ne da ba zan taba mantawa da shi ba.
Shakuwa tsakanin iyayena
Na fi shakuwa da mahaifina saboda akwai wani abu daya da nake tunawa. Idan ba mu da lafiya, shi namiji ne, yana aiki, amma zai tashi da kansa ya kai mu asibiti. Kun ga idan da ba lafiya yawanci mahaifiyarsa ke kai shi asibiti. Amma shi ya fi kai mu, sai ya ga kamar shi zai fi yi wa likita bayani. Zai tambayi likita wane irin abinci marar lafiyan da ya kai zai ci. Idan aka dawo da kansa zai kwantar da kai, ya dauki magani ya ba ka. Na tuna a lokacin ina aji biyar a sakandare da za a mini allura, sai na taho jikinsa ya rike ni. Kin ga da girmana sai likitar ta ce ban san na girma ba a lokacin kuma shekaruna 16. Kin ga irin shakuwar ke nan. Mutum ne mai ba da shawara. Lokacin da zan shiga sakandare a Dala ya ba ni shawarwari, kuma har yanzu ina tuna su kuma ina amfani da wadannan shawarwari. Kuma shi da kansa zai kai mu makaranta duk da cewa akwai direba. Kuma ni ce babbar ‘yarsa. Ya rasu a 1978.
Abubuwan da na koya daga iyayena
Na koyi iya zama da jama’a, da kuma mutunta jama’a. A lokacin da nake karama, masu aikinmu tare suke cin abinci da maza kannena. Na tashi na ga kowa daya ne a gidanmu. Na koyi ba kowa girmansa. Na koyi tarbiya irinta da ba ta yanzu ba.
Yadda muke taimaka wa mata
Ina cikin wata kungiya da muke cire kudi daga aljihunmu muna tarawa, don taimaka wa mata ta hanyar koya musu aikin hannu; kamar yin sabulu da kuma yadda za su sarrafa zobo. Mukan ba su kamar jari. Idan suka samu riba sai su rika biya a hankali. Muna yin hakan ne ba tare da mun gaya wa jama’a ba. Muna da kungiyar addini da muke irin wadannan ayyukan. Mukan zabi  ’ya’yan talakawa masu ilimi sosai mu kai su makaranta.
Inda na fi sha’awar zuwa hutu
Na fi son na yi hutu a Najeriya. Na fi son in je kauyenmu don na ga yadda rayuwarsu take gudana da kuma yadda zan taimaka musu. In shiga cikinsu mu yi wasa da dariya har na manta da duk wata damuwa. Da haka nake duba wurin da zan gyara don a rika zuwa yawon bude ido. A irin haka ne na gano ‘Baturiya’;  inda akwai tsuntsaye da dama.

kalubalen da na taba fuskanta
Akwai abubuwa da dama wadanda nake fuskanta a kamfanin Ashmin trabels dina. Akwai wasu hukumomin gwamnati a maimakon su sayi tikintinmu, sai su sayi na ‘Airline’ kun ga Airline din nan idan suka kwashi kudinsu, kuma ba mu da Airline a Najeriya. Akwai kamfanin jiragin sama na British Airways da KLM da sauransu. Idan gwamnati ta dauki kudin ta ba su, tana mantawa cewa wadannan ribar kasashen Turawa ne. Kuma a duk duniya ba za ku ga ofishin Airline a cikin gari ba sai a Najeriya. Ya kamata duk wani ofishin Airline ya zama yana filin jirgi. An kuma ba kamfanonin sufurin jiragen sama damar sayar da tikitin kamfanin Airline. To amma a Najeriya ba haka ba ne, wannan ce babbar matsalarmu. Ya kamata gwamnati ta rika bi ta hanyarmu don sayan tikiti domin duk ribar da muka samu, za mu yi amfani da ita don gyara kasarmu. Kuma za mu taimaka wurin ci gaban kasarmu.
Burina
Allah Ya sa mu gama da duniya lafiya. Muna son idan yau Allah Ya dauki ranmu Ya sa abin da muka yi ya bi tafarkin gaskiya. Burina a nan shi ne in ga kowa ya samu abin yi. Amma fa duk abin da za ku yi ya zamanto na halal.
Farin cikin zama uwa
Abin farin ciki ne, tun da ka haifi ’ya’ya, ka yi musu aure kuma har kana da jika Alhamdu lillah. Ba zan iya bayyana farin cikin ba, saboda kyauta ce daga Ubangiji.
Motsa jiki
Nakan yi zarga-zirga don motsa jiki.
Abinci
A da nakan ci kowane irin abinci, amma yanzu saboda shekaru nakan ci ganyayyaki da ’ya’yan itace. Kuma ina shan ruwa da yawa.
Abin da nake so ana tuna ni da shi
Ina son a tunani a matsayin mai gaskiya. Ina son duk abin da zan yi kamar yadda addini na ya ce; in rike Allah kuma in rike gaskiya. Kuma na tuna haka mahaifina ya gaya mana. Ya ce “duk abin da za ku yi, ku yi gaskiya ko kuna bakin kura, ku fadi gaskiya. Kada ku yi karya don tsoro. Domin, ba a cewar gaskiyar wane ta kare, sai dai a ce karyar wane ta kare.” Domin na tuna da na yi aikin banki na shekara 16 a ce ni na dauki biro da kaina na rubuta a kan cewa yau na bar aikin banki. Komai za a yi a rike gaskiya.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya