Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari

Ari ya bayyana irin barazanar da ya fuskanta bayan ƙin amincewa a tafka maguɗin zaɓe.

Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari

Tsohon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya ce bai damu da korar da aka yi masa ba, amma yana nan a kan bakansa cewa Aisha Binani ta jam’iyyar APC ce, ta lashe zaɓen gwamna na 2023.

An dakatar da Hudu Ari bayan da ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun kafin a kammala tattara sakamakon ƙuri’u.

Sai dai ya ce yana da hujjojin da ke nuna cewa Binani ta doke Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Da yake magana da manema labarai a Bauchi, Ari ya rantse da Alƙur’ani mai girma cewa manyan jami’an zaɓe sun yi watsi da hujjojinsa kan maguɗin zaɓe.

Ya zargi shugaban sashen Kimiyya da Fasaha na INEC a Adamawa da yin aringizon ƙuri’u, sannan jami’an tsaro sun kama wasu jami’an gwamnati suna canza sakamakon zaɓe.

Ari ya kuma zargi shugaban INEC da kotun zaɓe da yin watsi da bayanansa.

Ya ce ba a ba shi damar kare kansa ba, ko kuma tuntuɓar iyalansa domin yanke shawarar ɗaukar matakin shari’a.

Ya ce bai damu da korarsa daga aiki da aka yi ba, illa ɓata masa suna da aka yi a kafafen yaɗa labarai.

Ya ƙara da cewa rayuwarsa ta shiga hatsari yayin da ake gudanar da zaɓe, inda ya bayyana yadda shi da wasu jami’an zaɓe aka yi musu barazana don su ayyana gwamna mai ci a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar.

A cewarsa, an janye masa tsaro bayan ya ƙi amincewa da buƙatar.

Duk da cire shi daga muƙaminsa, Ari ya dage kan cewar ya bi dokokin zaɓe kuma ya yi abin da ya dace.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu gaskiya da adalci a lokacin zaɓe, tare da gargaɗin cewa rashin yin hakan zai iya jefa dimokuraɗiyya cikin wani hali.

Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa

Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri

Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa

Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Bello Turji a Zamfara