Aisha Buhari da matar Tinubu sun yi ran gadin Fadar Shugaban Kasa

A ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ga Bola Tinubu mai jiran gado.

Aisha Buhari da matar Tinubu sun yi ran gadin Fadar Shugaban Kasa

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta karbi bakuncin matar shugaban kasa mai jiran gado, Sanata Remi Tinubu, inda suka yi rangadin muhimman wurare a bangaren iyalan shugaban kasa a Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata.

Aminiya ta gano cewa Aisha Buhari ta bayyana wa Sanata Remi cewa bangaren Glass House da ka fadar shugaban kasa shi ne aka ware domin zaman iyalan shugaban kasa mai jiran gado.

Ta ce: “Bangaren da ke tsauraran matakan tsaro an ware shi ne ga shugaban kasa mai barin gado da iyalansa.”

Ta bayyana cewa an ware bangaren ne domin bayar da damar yin kwaskwarima domin tarewar shugaban kasa mai jiran gado.

A nata bangaren, Sanata Remi Tinubu ta bayyana godiyarta da kuma shirinta na yin aiki tukuru domin ci gaban Najeriya.

A ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ga Bola Tinubu mai jiran gado.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan