‘Aisha Mai kyuya’
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan an yi Sallah lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Aisha Mai kyuya’. Labarin ya kunshi yadda yawan son jiki ke jefa mutum halaka. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Akwai wata yarinya mai kyuya sunanta Aisha. Mahaifiyarta ta tsufa sosai. Komai aka sata ta yi sai […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan an yi Sallah lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Aisha Mai kyuya’. Labarin ya kunshi yadda yawan son jiki ke jefa mutum halaka. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Akwai wata yarinya mai kyuya sunanta Aisha. Mahaifiyarta ta tsufa sosai. Komai aka sata ta yi sai ta ki. Ba abin da yake burgeta kamar ta ga ta ci abinci ta kwanta bacci.
Suna da wata saniya wadda mahaifiyarta ta takan kai ta kogi domin ta sha ruwa kuma ta yi wanka. Ran nan mahaifiyar ta fada jinya da har ta kasa jan saniyar zuwa bakin kogi.
Sai ta dau minti ta bai wa Aisha ta roketa da ta kai saniyar ta sha ruwa. Da farko ba ta so zuwan ba sai da ta ga minti. Sai ta amsa, ta kori saniyar.
A hanyarsu ta zuwa bakin kogin, sai ta kasa hakura saboda son ci irin nata, sai ta daure saniyar a bakin bishiya ta zauna ta rika shan minti. Ga kishin ruwa ya dame saniyar ta kosa ta gama ta kai ta ta sha ruwa.
Aisha na gama shan mintin, sai ta kori saniyar zuwa gida ta yiwa mahaifiyar ta karya cewa saniyar ta sha ruwa, ta kuma koshi.
Abin ya bai wa saniyar haushi, sai ta tsine wa Aisha. Ta ce Allah Ya ba ta ’ya’ya tsuntsaye wadda sai sau daya a shekara za su sha ruwa.
Ana nan Aisha ta zama budurwa tayi aure. Tana haihuwa a maimakon a ga dan mutum, sai aka ga katuwar tsuntsu.