Aisha ta kwashe gudunmawar da ta kai ofishin APC a Taraba

Tsohuwar Ministar harkokin matan Najeriya Aisha Alhassan, wanda ta yi murabus daga mukaminta, yayin daga bisani ta fita daga jam’iyyar ta ta APC. Kafin fitar ta daga jam’iyyar APC ta baiwa ofishin jam’iyyar Kwamfutoci da kujeru da dai sauran kayan da ake bukata na gudanar da ayyukan ofis dake Jalingo. A cewar Sakataren APC na […]

Aisha ta kwashe gudunmawar da ta kai ofishin APC a Taraba

Tsohuwar Ministar harkokin matan Najeriya Aisha Alhassan, wanda ta yi murabus daga mukaminta, yayin daga bisani ta fita daga jam’iyyar ta ta APC.

Kafin fitar ta daga jam’iyyar APC ta baiwa ofishin jam’iyyar Kwamfutoci da kujeru da dai sauran kayan da ake bukata na gudanar da ayyukan ofis dake Jalingo.

A cewar Sakataren APC na jihar Mista Aaron Artimas  ya ce, Aisha Alhassan ta kwashe kayan ofis din da suka hada da: kafet da na’urar sanyaya daki da tebura da ta bayar da gudunmawa lokacin da tana mambar jam’iyyar APC.