A’ishatu fil jami’a

A’ishatu fil jami’a  Wata rana yaumul Juma’a An yi batun ‘E’ ko A’a daliba ta taki sa’a Labarinta ya zarta ba’a Ita ce mafificiyar dalibai Babanta na biyan matsabbai Zamanin da babu kwabbai Kar a nunkemu a baibai Daga Haurubja zuwa Dubai Tarho ne samma’a Kyandir ne sham’a Inji mutanen birnin san’a’a Mu dai mu […]

A’ishatu fil jami’a

A’ishatu fil jami’a 

Wata rana yaumul Juma’a

An yi batun ‘E’ ko A’a

daliba ta taki sa’a

Labarinta ya zarta ba’a


Ita ce mafificiyar dalibai

Babanta na biyan matsabbai

Zamanin da babu kwabbai

Kar a nunkemu a baibai

Daga Haurubja zuwa Dubai


Tarho ne samma’a

Kyandir ne sham’a

Inji mutanen birnin san’a’a

Mu dai mu yi sana’a

Don ribatar sa’ar kowace sa’a


Gyaran jar miya

Gararumar gyaran duniya

Gamagarin al’umma a kyautata niyya

Gangamin ginin bangon Haurobiya

Ganiyar bunkasar jikokin iya


Takarkarewar takara

Takun tunkarar tuwon tara

Tura ta kai bagon makura

Titibiri masomin gardi gangara

Takura ke haifar da kangara


Fafajiyar koyon wasatsake

Gashin kaza mai wake-wake

Tafiyar tsutsar  gamba a tamke

Kurtun tawada a cike

Da alkalami ake cake-cake


Wannan likita ce

Waccan malama ce

Wata ma lauya ce

Ana ta yi mata ce-ce- ku-ce

Haurobiyawa na da yawan zance


A doka misali da kwatance

A daina duk wani kauce-kauce

Ko nuna bambance-bambance

Babban kwado ne rummace

Rama da garin gero an yi kawance


A kawar da juhala

A tabbatar da adala

Bin doka ya malala

A daina sa wasu su hasala

Ai azama ban da kasala


Al’umma ai masalaha

Masu kyakyata dariya hahaha

A wage baki ha

Fanka ita ce mirwaha

Mu sarara ai raha



A jerin darussan da suka arce na yi wa ’yan makaranta watsattsaken makala mai taken ”LAULAYIN ALAYEN LAUYE-LAUYE,” inda na nusar da mu yadda aka nuna wa wata lauya wariya wai saboda ganin lullubin HIJABI da ILIMI an yi kawance. Ni kuwa gabanin aukuwar wannan lamari ina zuwa birnin Dabo inda ba a dabo, sai na ga wata ’yar dugwi-dugwi mai suna Bobo tana yi wa kanwarta wakar A’ishatu fil jami’a, har ni ma na samu kara yawan baitocin waken.

Bobo dai ta iya bobo da kambo irin na ’ya boko, shi ya sa ma idan ta shiga cikin ’yan uwa da kawaye sai ta yi ta karya harshe kamar ta ci kilishi tana yaren Ingilishi yayin da ta kanga gilashi. Kuma duk darasin da aka yi wa su Fici da Nanawo, wato yayyenta, cikin sauki za ta yi koyi ka koyar, wato kwaikwayon wasan kwaikwayo. Ganin irin wannan hazaka da zalaka ta ’yan dugwi-dugwi, ta sanya bayan na RIIRITA-TAYA daga kwadagon lalubben na-koko a garin tako-tako da ke Haurubja sai na rika zarya a farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai ta ’ya’yan Inna da Baba, inda na rika baje na-mujiya wajen ganin babban abin ta’ajibi.

Duk wanda ya kai ’ya’yansa irin wadannan makarantu tabbas zai jinka wa masu MAKARANSUWA (makarantun kasuwa, kodayake dai ana yi musu lakabi da MASU ZAMAN KANSU) makudan matsabbai, su kuwa su turo masa da dimbin aikin watsattsake da falle shafukan wagagen littattafai ya yi tare da ’yan dugwi-dugwi da ke tsalle-tsalle a gidansa. Kuma tun daga farkon mako zuwa Juma’a, matukar dai mutum na hankoron ganin A’isha a jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya, sai ya rika sawo TALIYAR INDON-MAMI, a cakuda da ’ya’yan kaji wadanda ba a kyankyashe ba. Uwa-uba ma sai an hada da wasu kayan kwalam da makwalashe na ’yan tande-tande da lashe-lashe. Wannan lamari dai ya sanya da kaina na ce wa ’yan makarantar bokoko a makarantun al’umma ko dai ku kara himma Ko kuwa in ce da ku CIM-BIN-kWALAM!

Ni dai zamanin da na halarci farfajiyar kwankwadar fura mai kyau ta GUDUN-DANDI a Hutun-dutse da ke can a Jihar dakin-kara, madurgujin tuwo ake ba mu, mu hada da koko da kosai don dundume kururu. Ganin irin kwalam da makwalashe da ake lashewa, sai na fara wasafawa a kwakwalwa, cewa, da za a dubi kolo da titibiri ’ya’yan malam, ai da sun daina DANDAZON DUMBUZAR DAMBU, har su karke da aikin KABU-KABU, domin babu mai yi musu BAMBU, sai dai a bar su su yi ta gararamba a kwararo-kwararo. Lallai a rika dama musu kokon gero da tuka musu tuwon dauro da nau’ukan abincin hatsin acca da iburo. Sannan su samu horo, don samun abin gudanar da rayuwa mai tudun dogaro. Aiwatar da wannan manufa za ta sanya su yi kafada-da-kafada da irin su A’ISHATU FIL JAMI’A su ma su zamto zakakurai a cikin dalibai, ko da iyayensu sun kasance KUTARE da MAKAFI.

Haurobiyawa, musamman Arewatawa, ina ta kokarin nusar da mu cewa ko da mun tattara ’yan lelenmu a farfajiya mai kyau, amma sauran ’ya’yan al’umma ko oho, mu sani ‘akwai sauran rina a kaba.’ Domin ISKA ba ta da da, BARIKI  ba ta da burki, illa dai kawai da zarar mutum ya fito shakatawar shan iska yana da zabin zama dan BANZA a banzar bazara. Lallai mu tarairayi rayuwar  ’yan dugwi-dugwi don samar da al’umma NAGARGARU, amma ba GAGARARRU ba, wadanda ke shafe tsawon SHEKARU suna ta fasa mana GARU.

Baban-burin-huriyya don gwamnatinka ta cimma burinta na TSINTSIYA madaurinki guda babu TSIYA-TSIYA,  sai a tarairayi rayuwar marasa galihu, ta yadda za su san cewa, duniya ta amince su ma sun HAIHU, a daina mayar da su HUHUN-MA’AHU.