Akan halin da jam’iyyar PDP ta samu kanta

Ko shakka babu duk abin da ya ba ka tsoro wata ranar shi ne zai ba ka tausayi, a yau kai tsaye ina magana ne akan halin da jam’iyyar PDP ta samu kanta, bayan rasa mulkin da ta yi.  Yau an wayi gari rigingimu sun fara kunno kai a jam’iyyar, wanda ko shakka babu dama […]

Akan halin da jam’iyyar PDP ta samu kanta
Akan halin da jam’iyyar PDP ta samu kanta

Ko shakka babu duk abin da ya ba ka tsoro wata ranar shi ne zai ba ka tausayi, a yau kai tsaye ina magana ne akan halin da jam’iyyar PDP ta samu kanta, bayan rasa mulkin da ta yi. 

Yau an wayi gari rigingimu sun fara kunno kai a jam’iyyar, wanda ko shakka babu dama don suna rike da madafun iko ne ya sa har sunka kwashe shekarun 16 ba tare da samun manyan matsaloli a jam’iyyar ba. Amma yanzu kam! Mun zura na mujiya nan da ‘yan shekaru kadan, sai an wayi gari jam’iyyar ta canza suna, take ko yin maja da wata jam’iyyar daban.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi, Tashar Bagu, 08069807496.

Komai ya ba ka mamaki…
Zuwa ga Edita hakika komai ka gani idan ya ba ka mamaki wata rana, sai ya ba ka tausayi domin yau wai PDP ce ke cewa wai kwamitin da Janar Muhammadu Buhari ya nada domin karbar mulki yana matsa musu. Mu da suka dinga matsa mana duk can baya basu gane tallakawan Najeriya na cikin wahala ba, yanzu sun gano ramau ba tada dadi ke nan.
To ina kira ga magoya wa ’yan kwamiti baya domin su dinga matsa musu har sai sun tatse hanjin cikinsu domin fitar da zaluncin da suka yiwa mutanen Najeriya na irin barnan da suka yi na man fetur da bangaren wutar lantarki da su Namadi Sambo suka sayarwa kansu da sauran abubuwan da bamu sani ba. Kuma sauran da ba’a bayyana ba mun san da Janar ya hau zai bayyana wa ’yan Najeriya komai da fatar Allah Ya karawa masa lafiya da kwanciyar hankali domin ya samu ya gyara mana kasarmu daga irin barnar da PDP ta yi.
Daga Usman Adamu Aliero, Jihar Kebbi, 07061594299.

Kira ga
Gwamna Isa Yuguda
Salam Aminiya, ku ba ni dama nayi kira da babban murya ga gwamnan Jihar Bauchi Mai barin gado wato Isa Yuguda, cewa mu matasa masu kishin jihar, masu akidar canji munaso Yuguda, ya fada mana me ne ne gwamnatinsa ta yi mana da kudin da Gwamnatin Tarayya ke bawa kananan hukumomin jihar 20, domin yanzu haka a matsayin mu na matasa wanda ba mu gamsu da halin da kananan hukumomi ke ciki a mulkinsa na shekaru takwas, ba mun shirya tsaf domin kai wannan magana ga hukumar EFCC dama duk wata hukuma da doka ta amince da shi domin neman bayani akan magudan kudin da kananan hukumomin suka samu, amma ko kashi 20 cikin 100, na wannan kudi ba a kashe su ga al’uma ba. Su waye ne suka cinye mana kudin kananan hukumomin Bauchi Yazamo dole kuma muna da ’yancin ayi mana bayani.
Daga Ahmadu Manager Bauchi, 08065189242.

Kira ga sabuwar gwamnatin Jihar
Jigawa
Assalamu alaikum Aminiya, ku ba ni dama na yi kira ga sabuwar gwamnatin Jihar Jigawa mai jiran Gado, karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Badaru cewa idan suka kama aiki da ta yiwa Allah ta soke jarrabawar karin girma da ake yiwa ma‘aikatan jihar a halin yanzu.
A maimakon haka kamata ya yi Sabuwar gwamnatin ta duba cancanta da kwarewar mutum akan aikinsa wajen ciyar da shi gaba.
Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia, 08060353382.

Yaba wa dan majalisar
wakilai
Salam Edita, don Allah ka ba ni dama nayi tsokaci tare da yaba wa dan majalisar wakilai wanda ya fito daga karamar hukumar Ajingi da Gaya saboda yadda ya fito ya ba da shawarar rage makudan kudin da ake ba su a majalisa duk da dimbin matsalolin da talakawa ke ciki hakika yadda ake amfani da wadannan kudin akwai barna mai yawan gaske. Kuma yakamata sabuwar gwamnati ta Janar Buhari ta duba wannan shawarar tare da amfani da ita ta haka ne za’a kara samun damar yin ayyuka. Kuma zai rage hanyar da ’yan siyasarmu ke yi a lokacin yakin neman zabe wato a mutu, ko a yi rai. Daga karshe iya kira ga sauran ’yan majalisa da su yi koyi da wannan wajen bankado wasu badakaloli domin kawar da su.
Daga Aminu Abdu Baka Noma, Sani Mai Nagge, Kano,08099479880.

Matsalar tsaro a
Najeriya, nesa tazo kusa
Tun bayan gudanar da zaben ranar 28 ga watan Maris, wanda a cikinsa ne Allah Ya tabbatar da sabon Shugaban kasarmu kuma jagoran canji a Najeriya, Janar Muhammadu Buhari, na jam iyyar APC, ga alamu an samu saukin aika-aikar da akewa lakabi da Boko Haram, domin tun da fari an ce jami’an tsaro sun amso wasu garuruwa da ada suka gagare su shiga a yankin Arewa-maso-Gabas, daga nan sai muka ji cewa an sake kubuto da wasu bayin Allah da ke a hannun wadancen mutane a yankuna daban-daban. Haka nan sai ga wata babbar nasara, inda aka ayyana damke wani da ake zargin yana ba su tallafin abinci da ma ababen hawa, daga nan sai kuma jami’an tsaro suka fidda faifan bidiyon yadda suke samun galaba. Duka dai sai mu yima Allah godiya domin shi ne mai maganin duk wani ko wasu da ke son ganin sun haddasa matsaloli a cikin al’umma.
Daga Mukhar Ibrahim Saulawa Katsina, 0706643451.