Akasarin wadanda za a nada ministoci na da hannu a matsalolin Najeriya — Masani

Dole ne Tinubu ya tsara wa ministocinsa jadawalin aiki tare da da tabbatar da sun aiwatar da shi cikin rikon amana.

Akasarin wadanda za a nada ministoci na da hannu a matsalolin Najeriya — Masani

Masanin Shari’a da Difilomasiyyar Kasa-da-Kasa Barista Mainasara Kogo Umar ya yi suka a kan tsarin jujjuya mukaman shugabanci ko tsayawa takara a tsakanin wasu kalilan din mutane, maimakon shigo da sababbin kwakwalwa don ba da gudunmawar basirarsu.

Ya ce zai yi wuya a samu wani ci gaba mai ma’ana a shugabancin wadanda aka gabatar da sunayensu a gaban Majalisar Dattawa don tantance su su zama ministoci.

Barista Mainasar Kogo ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce, “Ban yi tsammanin wadannan mutum 28 da aka gabatar, su ne wadanda aka yi ta boye mana sunayensu ba.

“Zai yi wuya kasa ta samu ci gaba mai ma’ana matukar wasu ’yan kalilan ne za su yi ta yin karbakarbar mukaman minista ko gwamna ko sanata a tsakaninsu, maimakon a rika ba da dama ga wasu sababbin kwakwale su ma su shigo don a samu sauyi.

Ya, ce “Mafi rinjayen wadanda aka fara gabatar da su a gaban Majalisar Dattawa don tantancewa, su ne ungozoman yawancin matsalolin da muke fuskanta a Najeriya.

“Ragowar da suka kasance ba su taba rike mukamai ba kuwa, idan aka bincika watakila za a samu gyauro ne na wadanda Hukumar EFCC ke bincika, ko wadanda kotuna suka bad a umarnin a hana ba su wani mukami, ko wadanda suka rasa shaidar aikin yi wa kasa hidima, da sauransu.”

Barista Mainasara Kogo Umar ya ce hakan na nufin zai yi wuya a samu sauyin gudanar da aiki a sabuwar gwamnatin yanzu daga wadda ta gabace ta, ta tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Da yake bayani kan hakkin shugabanci, masanin ya ce Sashi na 130 na Tsarin Mulkin Najeriya ya ce zababben Shugaban Kasa shi ne Shugaban Gwamnati wanda ake bukatar ya yi wa ’yan kasa adalci bayan tallata kansa gabansu a lokacin yakin neman zabe, sannan ya sha rantsuwa yin adalci a lokacin da yake rike da Alkur’ani ko Baibul.

Ya ce sassa na 147 da na 150 da 153 da 158 sun bai wa Shugaban Kasa ko Gwamna damar ya zabi hadiman da za su tallafa masa wajen aiwatar da aiki, saboda haka idan wadanda ya zaba suka gaza laifin na komawa kansa ne duk da cewa su ma za a tuhume su.

“Saboda haka dole ne Shugaban Kasa ya tsara wa ministocinsa jadawalin aiki tare da zagewa wajen ganin sun aiwatar da shi cikin rikon amana.”

“Dole ne ya tsaya tamkar shi ne minista na kowace ma’aikata tare da tabbatar da cewa ministocin sun aikata daidai.

“Idan ba haka ba, zai yi wuya a samu wani canji mai ma’ana da hakan zai iya kai ga maimaita abin da ya faru ga gwamnatin baya,” in ji masanin.

Da ya juya kan jinkirin da aka fuskanta kan gabatar da sunayen ministocin kuwa inda wasu ke ganin hakan zai iya shafar aikinsu.

Barista Mainasara ya ce ba lallai ne a fuskanci hakan ba, sai dai ya ce dole ne gwamnati ta yi la’akari da cancanta wajen zabar ministoci, maimakon sakayya inda yawanci ake zargin shi ne abin da aka yi la’akari da shi kan wadanda aka gabatar da sunayen nasu.

Ya ce dole ne kuma wadanda za a nadan su fuskanci manyan matsaloli da ke gaban kasar nan da zaran an rantsar da su wadanda ya ce sun hada da na matsalar tsaro da ta rarrabuwar kai a tsakanin mabambatan yankuna da kabilu ko addinai.

Ya ce dole ne su yi adalci a tsakanin al’ummar kasa don rage gibi da ke tsakanin talaka da mai kudi, sai kuma kawo abin da zai rage matsalar hauhawar farashin kaya da rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa.

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan