Akeredolu ya lashe zaben Gwamnan Ondo

Akeredolu ya samu nasara a 15 daga cikin kananan hukumomi 18 na jihar Ondo

Akeredolu ya lashe zaben Gwamnan Ondo

Rotimi Akeredolu

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban Jami’ar Ibadan, Farfesa Abel Idowu Olayinka, wanda shi ne Babban Bature zabe na INEC,  yayin bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi ya ce Akeredolu ya samu nasara ne da kuri’a 292,830.

Alkaluman sun nuna Akeredolu da ke neman wa’adin mulki na biyu a jam’iyyar APC ya samu gagarumar rinjaye a 15 daga cikin Kananan Hukumomi 18 na jihar.

Babban abokin hamayarsa, Eyitayo Jegede na jami’ar PDP ya samu kuri’a 195,791 a matsayi na biyu a zaben.

Mataimakin Gwamnan, Agboola Ajayi wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar ZLP shi ne ya zo na uku bayan ya samu kuri’a 69,127.

Nan gaba aka sa ran Farfesa Abel ya sanar da sakamakon zaben na karshe a hukumance.