Aki: Matar tauraron Nollywood ta haifi da na biyu

Tauraron Nollywood, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya haifi dansa na biyu

Aki: Matar tauraron Nollywood ta haifi da na biyu

Matar tauraron fina-finan Nollywood, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya samu dansa na biyu.

Aki ya sanar cewa matarsa Nneoma Nwaijah, ta haihu ne ta shafinsa na Instagram a karshen mako.

A jikin sakon ya dora hotonsa da na mai jegon da kuma jaririn, inda ya rubuta cewa, “jama’a ku taya mu murnar samu haihuwar da namiji. Godiya ta tabbata ga Allah.”

Sai dai Chinedu bai bayyana lokacin da mai jegon ta sauka ba.

Wannan ne da na biyu da Allah Ya azurtata Chinedu da Nneoma Nwaijah da shi tun bayan aurensu a shekarar 2011.

A shekarar 2017 ne Neoma ta haifi dansu na fari, shekaru shida bayan aurensu.

Chinedu Ihezie, ya shahara da taka rawar barkwanci musamman a fim din ‘Aki na Ukwa’ a shekarar 2002 inda da ya fito a matsayin Aki tare da Osita Iheme, wanda ya fito a matsayin ‘Paw Paw’.

Chinedu ya taka rawa a fina-finai sama da 150, ciki har da wanda ya yi tare da shahararren jarumin Kannywood, marigayi Rabilu Musa Ibro.