Akin Hajji: kungiyoyi sun nuna rashin jin dadinsu ga gwamnatin Kalaba

Siyasa ta shigo cikin hukumar alhazai ta Jihar Ribas har ma Musulmin Jihar sun nuna rashin jin dadin su game da yadda gwamnan Jihar Nyesom Wike ya nada shugabannin hukumar ba tare da sanya mambobin kungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI ba. Da kuma sauran kungiyoyin musulmi, ‘yan arewa da kuma ‘yan asalin Jihar Ribas da […]

Akin Hajji: kungiyoyi sun nuna rashin jin dadinsu ga gwamnatin Kalaba
Akin Hajji: kungiyoyi sun nuna rashin jin dadinsu ga gwamnatin Kalaba

Siyasa ta shigo cikin hukumar alhazai ta Jihar Ribas har ma Musulmin Jihar sun nuna rashin jin dadin su game da yadda gwamnan Jihar Nyesom Wike ya nada shugabannin hukumar ba tare da sanya mambobin kungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI ba. Da kuma sauran kungiyoyin musulmi, ‘yan arewa da kuma ‘yan asalin Jihar Ribas da kabilar yarabawa da na Jihar Edo.
A zamanin gwamnatin Peter Odili da ta shude ana yin hadin gambiza ne ta inda kowanne ana ba shi wakilci a hukumar amma a yanzu da kida ya canza sai rawar ma ta canza.
A korafin da kungiyoyin suka yi a wasikar koke da kin amincewa da shugabannin suka rattaba hannu zuwa ga gwamna kungiyoyin sun ce bai kamata a yanke hukunci haka ba, ba batare da an shawarce su ba.