Akshay Kumar ya shirya daukar sabon fim
Matashin jarumin fina-finan Indiya, Akshay Kumar ya kammala kintsawa domin fara daukar sabon fim dinsa mai suna ‘Baby.’Fim din, wanda na gumurzu ne, za a fara daukar shi ne a biranen Nepal da Istanbul na kasar Turkiyya da kuma Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.daya daga cikin kamfanoni uku da suka yi hadin […]

Matashin jarumin fina-finan Indiya, Akshay Kumar ya kammala kintsawa domin fara daukar sabon fim dinsa mai suna ‘Baby.’
Fim din, wanda na gumurzu ne, za a fara daukar shi ne a biranen Nepal da Istanbul na kasar Turkiyya da kuma Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
daya daga cikin kamfanoni uku da suka yi hadin gwiwar shirya fim din, wato T-Series, ya bayyana cewa Neeraj Pandey ne zai ba da umurni. Haka kuma ya tabbatar da cewa za a kammala fim din cikin lokaci, domin fitar da shi kasuwa a Janairun badi.
“Ina matukar murna da na hada hannu da kamfanonin shirya fina-finai na ‘Friday Filmworks’ da ‘Crouching Tiger Motion Pictures,’ domin samar da fim din ‘Baby.” Inji Shugaban kamfanin ‘T-Series,’ Bhushan Kumar, wanda daya ne daga cikin kamfanonin da suka yi hadin gwiwa domin shirya fim din.
Ya ci gaba da cewa: “A kamfaninmu, mun yi amanna da fitar da fina-finan zamani, wadanda suka dace da al’ummar zamani. Har kullum muna daraja ayyukan darakta Neeraj. Mun dogara da fasaharsa da ta Akshay, domin samar da ingantaccen fim mai kayatarwa ga masu kallo.”