Akuya ta haifi dodo bayan an yi mata tiyata
A yau Litinin ne wani abun al’ajabi ya faru a garin Ilesha a jihar Osun, inda wata akuya ta haifi wata irin halitta mai kama da dodo bayan an yi mata tiyata. A cewar likitan da ya yi wa akuyar tiyata Dakta Afolabi Joseph, an yi mata aikin ne domin ceto ranta, ya ce an […]
A yau Litinin ne wani abun al’ajabi ya faru a garin Ilesha a jihar Osun, inda wata akuya ta haifi wata irin halitta mai kama da dodo bayan an yi mata tiyata.
A cewar likitan da ya yi wa akuyar tiyata Dakta Afolabi Joseph, an yi mata aikin ne domin ceto ranta, ya ce an yi aikin tiyatar cikin nasara.
Haka zalika, sakatariyar hulda da manema labarai ta ma’aikatar noma a jihar Osun, Segilola Babalola ta shaida wa Aminiya cewa halittar da akuyar ta haifa nada karamin kai da kafafu 8, ta ce halittar mai kama da dodo ta mutu jim kadan da haihuwarta amma uwar na nan da ranta.