Akwai abubuwan alheri a Tafa amma ba a fadi – Dagaci

Garin Tafa da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya kasance wurin yada zango ga direbobin manyan motoci. Aminiya ta zanta da Dagacin Dogon karfen Tafa, Malam Nasidi Adamu Yahaya inda ya yi bayani a kan tarihin kafuwar garin tare da wasu alheransa da yake son jama’a su rika tuna garin da su, ba wai na […]

Akwai abubuwan alheri a Tafa amma ba a fadi – Dagaci

Garin Tafa da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya kasance wurin yada zango ga direbobin manyan motoci. Aminiya ta zanta da Dagacin Dogon karfen Tafa, Malam Nasidi Adamu Yahaya inda ya yi bayani a kan tarihin kafuwar garin tare da wasu alheransa da yake son jama’a su rika tuna garin da su, ba wai na badala kawai ba:

 

Yallabai mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Nasidi Adamu Yahaya, ni ne Dagacin Dogon karfen Tafa. An haife ni a wani gari mai suna Kubacha a karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna. Daga can ne mahaifina Malam Adamu Sulaiman ya taso a 1975 ya zo ya kafa garin Tafa, a nan na bude ido. Na yi makarantar firamare ta LEA da ke garin Sabo-Wuse wanda kusan hade yake da garin nan duk da cewa yana Jihar Neja ne. Bayan nan sai na wuce Sakandaren Gwamnati da ke Dikko sai dai bayan na gama ban samu damar ci gaba ba sai na dukufa ga harkokin kasuwanci. Ina da matan aure 2, Kuma Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya 20, 15 na raye, 5 sun rasu.  

Mene ne tarihin kafuwar wannan gari na Tafa?

Kamar yadda na fada a baya mahaifina ya kafa wannan gari a  1975 lokacin yana daji ba hanyar mota sai ta kafa, sai an koma baya ta Suleja can ne hanyar mota take daya ta yi ta Tegina ta bi Birnin-Gwari ta wuce Kaduna, sai kuma daya wadda ta bi Keffi ta yi Lakwaja. Sana’ar kamun kifi ne ya kawo shi nan yana bin ruwa yana kama kifi. Na gaji wannar sana’ar a wajensa da kuma bangaren gidan mahaifiyata su ma ita ce suka sani. Bayan ya ji dadin wajen nan da Allah Ya kaddara zai kafa garin sai ya koma Kagarko ya samu Hakimi mai suna Sulaiman Babba ya yi gaisuwa ya ce ya ga wuri yana son kafa gari. Sai Hakimi ya ba shi dama. Da farko ya so a yi wa garin suna Sabuwar Kubacha tunda daga can muka taso muka zo nan, amma sunan bai zauna ba. Sai kuma aka ba da suna Unguwar Malamai, shi ma bai zauna ba, sunan rafin nan dai wato Tafa shi ne ya ture kowane suna. Hakimi Sulaiman Babba ya hada mahaifinmu da wani malami mai suna Malam Tanko (Allah Ya jikansu da rahama baki daya). To a lokacin sai Hakimi ya ce da Malam, “Ka bi Adamu zuwa wurin da ya kafa ka yi masa addu’a.” A lokacin mahaifina ya tashi daga bakin ruwa ya hauro ta tudu ya yi bukkarsa guda daya inda Masallacin Juma’ar nan yake a yanzu. A wurin ne yake gasa kifin da ya tara ya hau kekensa ya zaga zuwa wurare kamar Suleja da Izom da Lambata idan ya sayar ya dawo. Malamin ya tambayi mahaifinmu ko akwai kuma wata addu’a da yake bukata, sai ya ce yana fatan ko bayan ransa a gina Masallacin Juma’a na garin a daidai inda ya fara kafa bukkar nan, kuma abin da ya faru ke nan.  

Mene ne sanadin fara bunkasar wannan gari da masu manyan mota ba sa iya wucewa ba tare da sun yada zango ba?

Akwai wani wuri da ake kira Dumes wanda sansani ne na leburori, to a 1982 lokacin Shugaban kasa Shehu Shagari sai batun aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna ya tashi, sai aka yi rushe-rushe a wurin, hakan sai ya sa mutanen da rushe-rushen ya shafa suka yi hijira zuwa nan Tafa ciki har da ’yan mata ’yan duniya. Ka ji dalili na farko ke nan da garin nan ya fara haduwa, ana cikin haka kuma sai aikin tagwayen titi da ya ratsa ta garin nan ya yi Kaduna ya karaso nan inda har yanzu kullum bunkasa garin yake yi saboda su kansu direbobin manyan motocin suna gina gidaje su dawo da iyalansu nan ta yadda duk ta inda suka fito a kasar nan za su tsaya a gida kafin su yi gaba. Mahaifina ya yi ta kai-komo ta fuskar masarauta don tabbatar da cewa hukuma ta sa hannu wajen tsara garin, a lokacin nan muna karkashin karamar Hukumar Kachiya ce saboda ba a kirkiro karamar Hukumar Kagarko ba. Wani lokacin ya je Kachiya wani lokaci ya je Zariya ya samu Mai martaba Sarkin Zazzau ya gabatar masa da bukata ta fasalta gari, a karshe aka turo jami’an kasa da safiyo suka fitar da layuka daga nan kan tudu jama’a da sauran baki suka yi gine-gine a wuraren shi ya sa kake ganin duk inda ka ratsa a garin za ka ga gidaje a jeri ga tituna nan mike. 

Yaya yanayin tsarin masaurartar gari kuma?

A lokacin Gwamnan Jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi an samu karin ci gaba a tsarin masarautar garin inda a yanzu aka raba sarautar gida 2 kamar yadda tagwayen titi ya raba garin, akwai bangaren Gabas inda kanen mahaifina mai suna Shehu Sulaiman ke matsayin Dagaci, sai kuma ni a nan tsallaken Yamma, sannan garin a yanzu ya koma karkashin masarautar Jere.  

Ina ne asalin tsatson wadanda su ka kafa wannan gari?

Asalin iyayenmu dai mutanen garin Bunkure ne a Jihar Kano.

Yaya batun Hawan Sallah a ina ne ma’abuta sarautar wannan gari ke biki? 

Gabanin gwamnatin Gwamna Ahmad Makarfi ta rarraba masarautu Zariya muke zuwa Hawan Sallah, amma daga baya a shekarar 2000 sai muka koma zuwa garin Jere inda a can ne Sarkinmu yake wato Dokta Sa’adu Usman, sai dai idan muna da wata matsala, mukan kai wa hakiminmu da ke garin Kagarko.

Garin Tafa ya yi kaurin suna a abubuwan badala yaya kuke ji da wannan?

A gaskiya ba a yi mana adalci, akwai abubuwa na alheri da dama da wannan gari ya yi fice a kai, amma ba a tuna mu da komai sai abin da wadansu daga cikin baki ke yi. dan wannan gari mai suna Malam Ja’afar ya zo na daya a gasar karatun Alkur’ani ta kasa da a ka yi a Abuja a wani lokaci, amma duk jama’a ba sa ganin wannan. Sannan wannan wuri ya zama cibiyar gyara manyan motoci da samun kayan gyara a dalilin hakan ’ya’yanmu sun zama kanikawa wadansu direbobn manyan motoci duk wannan ci gaba ne amma ba a gani.