Akwai alaka mai kyau tsakanin Kudu da Arewa – Etsu Nepe

Etsu Nupe, Alhaji Dokta Alhaji Yahaya Abubakar ya bayyana cewa akwai alaka kyakkyawa tsakanin Arewacin Najeriya da takwarorinsu na Kudanci Ya bayyana haka ne lokacin da ya zanta da Aminiya a Kalaba ranar Asabar da ta gabata, lokacin da aka gayyace shi a matsayin babban bako mai kaddamar littafin tarihin wani hamshakin dan siyasa mai […]

Akwai alaka mai kyau tsakanin Kudu da Arewa – Etsu Nepe

Etsu Nupe, Alhaji Dokta Alhaji Yahaya Abubakar ya bayyana cewa akwai alaka kyakkyawa tsakanin Arewacin Najeriya da takwarorinsu na Kudanci

Ya bayyana haka ne lokacin da ya zanta da Aminiya a Kalaba ranar Asabar da ta gabata, lokacin da aka gayyace shi a matsayin babban bako mai kaddamar littafin tarihin wani hamshakin dan siyasa mai suna Goddy Jeddy Agba.

Bayan da aka tashi taron wakilinmu  ya tambaye shi ko yadda alaka take tsakanin sarakunan gargajiya na Arewacin kasar nan da kuma takwarorinsu na Kudanci. Ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka, kasancewar duk al’ummarsu suke yi wa aiki daidai iyawarsu, tare da kare muradun al’ada da dokokin kasa.

Etsun na Nupe ya kara da cewa, irin wannan alaka ce ma ta sanya ya halarci wannan muhimmin taro, domin yaukaka zumunci tsakanin al’ummomin yankinsa da na Kudu, kasancewar ana zaune a kasa daya kuma akwai musharaka tsakanin kowane bangare.