Akwai alamun Shugaba Nkurunziza ne zai lashe zaben Burundi
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, na ci gaba da kidaya kuri’u tun bayan rufe rumfunan zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Burundi ranar Talata.Duk da cewa abokan hamayyar Shugaba Pierre Nkurunziza sun kauracewa zaben, alamu na nuna cewa shugaban mai ci ne zai lashe zaben a karo na uku. Zaben dai ya […]
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, na ci gaba da kidaya kuri’u tun bayan rufe rumfunan zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Burundi ranar Talata.
Duk da cewa abokan hamayyar Shugaba Pierre Nkurunziza sun kauracewa zaben, alamu na nuna cewa shugaban mai ci ne zai lashe zaben a karo na uku. Zaben dai ya sha suka daga ciki da wajen kasar.
kasar Amurka ta bayyana zaben a matsayin maras sahihanci ta kuma yi barazanar sanya wa ‘yan kasar takunkumin shiga Amurka.
Jim kadan gabanin fara zaben a ranar Talata, an samu rahoton rasuwar wani dan snda da wani farar hula guda bayan wani hari wani a birnin Bujumbura, wurin da aka kwashe watanni ana zanga-zangar adawa da shugaban. Gidan talabijin na Al Jazeera ya ruwaito cewa an kashe daya daga cikin ’yan adawa a cikin dare.
Akalla kusan mutane miliyan hudu ne suka cancanci kada kuri’a a zaben, wanda ’yan adawa da masu rajin kare hakkin dan Adam suka kaurace masa, bisa zargin rashin adalci.
Hukumar zaben kasar dai ta ce sakamakon zai fito cikin kwanaki uku.