Akwai alheri a sana’ar kiwon kaji – Sani Kayarda
Alhaji Sani Umar Kayarda shi ne shugaban gonar kiwon kaji da kifi ta Kayarda Intergeted Farm (Jan bulo) da ke garin Kayarda, a karamar Hukumar Lere na Jihar Kaduna. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa akwai alheri da kwanciyar hankali a sana’ar kiwon kaji. Haka kuma ya bayyana yadda bude […]
Alhaji Sani Umar Kayarda shi ne shugaban gonar kiwon kaji da kifi ta Kayarda Intergeted Farm (Jan bulo) da ke garin Kayarda, a karamar Hukumar Lere na Jihar Kaduna. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa akwai alheri da kwanciyar hankali a sana’ar kiwon kaji. Haka kuma ya bayyana yadda bude wannan gona, da irin nasarorin da ya samu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar bude wannan gona kuma tun yaushe ka bude ta?
Kayarda: Ni dai farko bayan na kammala karatu, sai na kama harkokin kasuwancin masara. Ina sayen masara a wannan yanki namu na Lere ina kaiwa kudancin kasar nan. Kamar Benin da Fatakwal da Legas da Ibadan. Sai na ga duk inda muke kai masara, gidajen kaji ne muke kaiwa. Sai na sami wani likitan kaji na ce wai shin gidan kajin nan, ba zai yiwu a bude shi a wannan yanki na Lere ba? Sai likitan ya ce mani zai yiwu mana, domin yankin Lere wuri ne mai ni’ima mai sanyi, don haka babu abin da ba zai yiwu ba, a sha’anin noma da kiwo.
Shi ne nan take na fara wannan harka a gida a shekara ta 2002. Na je na sayo ‘ya’yan kaji guda 1,200 bayan dan lokaci sai duk suka mutu. Ban ji tsoro ba, na je na sake sayo wasu guda 1,200, to sai Allah Ya amfana mani su. Sai na fahimci cewa lallai wannan harka ta kiwon kaji akwai alheri a cikinta. Don haka na nemi wannan wuri, bayan na mallake shi, na bude wannan gona na gina dakuna guda hudu.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu kawo yanzu?
Kayarda: A gaskiya mun sami nasarori da dama a wannan gona domin mun koyi wannan sana’a mun iya ta, ko da wata matsala ta taso mun san yadda zamu magance ta. A gaskiya babu abin da zance sai dai na yi wa Allah godiya kan wannan harka ta kiwon kaji. Domin a yanzu a wannan gona muna da dakunan kaji guda 25, muna da kaji kusan dubu 30. Muna da ma’aikata wadanda suke aiki a wannan gona guda 54. Kuma mu ne muke hada abincin kajin da kanmu musamman idan masara tana araha. Wani lokaci kuma idan masara ta yi tsada sai mu sayi abincin a kamfanonin abincin kaji.
Yanzu ka ga zamu noma masara kuma zamu sarrafa wannan masara da muka noma mu baiwa kajin da muke kiwo. Don haka duk masarar da na noma a wannan gona take karewa, duk da cewa ina noma masara da yawa. Bayan masarar da na noma nakan sayi ta mutane na kara. A duk shekara na kan sayi masara kamar tirela 10 na ajiye, domin amfani da ita a wannan gona ta kiwon kaji. A duk wata kajin wannan gona suna cinye tirela daya da rabi. Ban da sauran dusar alkama da muke sayowa daga kamfanonin fulawa a Ibadan da Legas da muke hadawa da masarar.
Bayan haka duk kwan da muke fitarwa a wannan gona, baya zama domin muna da abokan ciniki a wurare daban-daban kamar Kaduna, Zariya, Kano da dai sauransu. Wata nasarar kuma ita ce kashin kajin da ake zuwa har Legas ko Ibadan a sayo. Mu ga shi nan a wannan gona muna zubawa a gonakin da muke nomawa. Yanzu ko waye ya yi iyaka da gonakina zaka ga amfanin gonata ta fi nasa kyau, saboda kashin kajin da nake amfani da shi.
Kuma a kowace shekara a kalla muna sayar da kashin kaji na kudi sama da naira miliyan 5, bayan mun debi wanda zamu yi amfani da shi, a gonakinmu. Kamar yadda na fada muna da ma’aikata da suke aiki a wannan gona mutum 54. A takaice idan muka kiyasta zamu ga mutanen da suke cin abinci a wannan gona sun kai mutum 500. Saboda ma’aikatanmu yawaicinsu maza ne, zaka sami wani yana da mata biyu da ‘ya’ya biyar, wani yana tare har da iyayensa. Ka ga a kalla idan za a bi daki-daki, wadanda suke cin abinci a wannan gona zasu kai mutum 500. Saboda haka babu abin da zamu ce sai dai mu yi wa Allah godiya.
Aminiya: A matsayinka da wanda ya dade a cikin wannan harka ta kiwon kaji, ya ya zaka bayyana mahimmancin wannan sana’a ga al’umma?
Kayarda: Tsakani da Allah ina baiwa jama’a shawarar su kama wannan sana’a ta kiwon kaji. Domin akwai alheri da kwanciyar hankali a cikinta. Domin a kullum wani abu zai shigo maka, babu asabar ko lahadi kullum kaza zata yi maka kwai. Kuma idan mutum yana tunanin cewa wai kaji suna mutuwa, to babu harkar da babu asara. Don haka harkar kiwon kaji ma akwai asara, amma samun ya fi yawa sosai da sosai. Komai na rayuwa yana dadi yana da wahala. Amma tsakani da Allah ni dai ina baiwa jama’a shawara, su shigo harkar kiwon kaji domin akwai alheri sosai a cikin ta.
Aminiya: Na lura akwai wajen kiwon kifi a wannan gona. Shi kuma ya ya aka yi ka fara shi?
Kayarda: Yadda aka yi na fara wanna kiwon kifi shi ne a wannan gona akwai wani babban rami, da yake ajiye ruwa. Sai na yanke shawarar kawo kifi don na gwada. Shi ne na tura Jos aka kawo mani, kananan kifi muka zuba a wannan rami. A cikin wata uku sai kifin nan ya yi girma kamar cinya, saboda abincin da muke ba su. Daga nan sai na fadada wannan kiwo na kifi, yanzu ina da wajen kiwon kifi babba, wanda muke amfani da shi sosai. Kuma ana zuwa daga Jos ana sayen wannan kifi.