Akwai azzalumai a APC – Sanata Bala Muhammad
Sanata Bala Abdulkadir Muhammad dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP ya zanta da ‘yan jarida ciki har da Aminiya inda ya bayyana kudirinsa ga Jihar Bauchi. Yaya batun sulhunta ’yan Jam’iyyar PDP da suke ganin ba a musu daidai ba? Mun kafa kwamiti karkashin jagorancin Sanata Bala Adamu Kariya domin a samu […]
Sanata Bala Abdulkadir Muhammad dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP ya zanta da ‘yan jarida ciki har da Aminiya inda ya bayyana kudirinsa ga Jihar Bauchi.
Yaya batun sulhunta ’yan Jam’iyyar PDP da suke ganin ba a musu daidai ba?
Mun kafa kwamiti karkashin jagorancin Sanata Bala Adamu Kariya domin a samu maslaha da zaman lafiya. Sannan kuma kwamitin na da nasaba da jawo wadanda aka yi musu rashin adalci da fin karfi a sauran jam’iyyu.
Wasu na gani kun makara domin wasu daga cikin wadannan mutanen sun riga sun shiga wasu jam’iyyu?
Gaskiya ba mu makara ba domin gogaggun ’yan siyasa a siyasar Bauchi mafi yawansu mun riga mun isa gare su, mun yi magana da su kuma muna ci gaba da magana da su. Ka san muna da al’adar sauraron nagaba da jin maganarsa, saboda haka ne muke ganin wannan kwamitin dattawan suna da kimar da idan suka musu magana cikin yardar Allah za su saurare su, kuma muna godiya ga Allah, an samu nasara da dama.
Ana ganin musamman a Arewa cewa duk wanda ba ya tare da Buhari kamar ba nagari ba ne, yaya za ku magance wannan?
To, Hausawa sun ce ai jiki magayi. Kowa ya ji a jikinsa kuma kowa ya gani. Idan an ce wanda bai tafiyan Buhari ba mutumin kirki ba ne, su wadanda suke tafiyar Buhari me suka tsinana wa jama’a? azaba aka gana wa mutane. Shi Buharin ba ya nan ne aka gana wa jama’a azaba a jihar Bauchi? Babu mukamin da Buhari bai ba Bauchi ba, me wadanda aka ba suka yi don kyautata wa al’ummar jihar Bauchi? akwai azzalumai da yawa a APC, meye suke yi wa Bauchi? PDP kuma kun ga abun da muka yi a Bauchi a lokacin da muke rike da mukamai, kowa ya san abun da muka yi, mun taimaki jama’ar Bauchi, mun kwantar musu da hankali. Kuma an samu ci gaba sannan kullum muna tare da jama’a.
An ga wasu hotunanka a dandalin sada zumunta tare da Buhari, ko me hakan ke nufi?
Ni ban san yadda wannan abun ya fito ba, watakila an ga cewa abin da muke yi wa talaka ya zo daidai ne, tunda daman mu ne a Jam’iyyar ANPP Allah Ya nufa muka karbi gwamnati a Jihar Bauchi, ni kuma na tafi Majalisar Dattawa. Tare muke da Buhari a ANPP a wancan lokacin, amma shi yanzu yana Jamiyyar APC ni kuma ina Jam’iyyar PDP.
Ya alakarka da Buhari?
Akwai alaka mai kyau kuma ta zaman lafiya a tsakani.
Me za ka ce game da yadda ’yan takara suke daukan alkawura a lokacin neman zabe, amma idan suka samu nasara su yi shiru?
Babban abu shi ne a fara hada kan al’umma, saboda abun da yake gabanmu kalubale ne babba wanda dole ne sai an jajirce. Mutane wadanda ba su san Allah ba, ba su kuma san ya kamata ba, abun da kawai suke yi shi ne amfani da dattijo Shugaban Kasa Muhammadu Buhari su samu kujera, amma abin da suke yi daban da yadda aka aka yi tsammani, ana musu kyakkyawar tsammani amma a wajensu wayonsu ne ko dabararsu ke ya ba su. Saboda haka ne suke duk abin da suke so, kuma suke raba kanmu.
Yaya kuke ganin za ku fafata da gwamna mai ci?
Akwai Nasara a tafiyarmu sosai, akwai haske sosai cikin gwagwarmayar, amma abu ne wanda ba za mu dauka da wasa ba, domin yaki da azzalumi dole sai an dage sai kuma an dirje.
Duk abin da suke so su yi na amfani da kudi da amfani da hukuma musamman hukumar zabe, da kuma sauran abubuwan da suke son yin amfani da matasa domin kun ga abin da da suka yi a zaben cike gurbi na sanata da aka yi kwanakin baya a Bauchi. Sun soke mana kuri’unmu sun yi amfani da kudi, to mun riga mun gane, kuma muna son jama’a su sani abin da ba zai kashe maka kishin ruwa na kwana bakwai ba, to bai kamata a sayar da ’yanci ba a kai ba. wannan kudin da ake bayar wa ba za mu bari a bayar ba ma, saboda ma’aikata ne suke zuwa su raba kudin kuma kudin na mutanen Bauchi ne. Za mu sanya mutanen Bauchi su kwace kudin. Sannan hukumar da ake amfani da su, ya kamata su sani su ne suke da alhakin samar da zaman lafiya, mu ba za mu sake yarda a soke mana kuri’a ba kuma ana kawo kudi ana raba wa a mazabu ba.