Akwai babban kalubale a gaban Buhari – Gurgusku

Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma dan Kwamitin Amintattunta a Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gurgusku Potiskum, ya shawarci Shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari kan ya sa himma wajen kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar jihohin Arewa tare da samar wa matasa aikin yi da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Alhaji […]

Akwai babban kalubale a gaban Buhari – Gurgusku
Akwai babban kalubale a gaban Buhari – Gurgusku

Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma dan Kwamitin Amintattunta a Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gurgusku Potiskum, ya shawarci Shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari kan ya sa himma wajen kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar jihohin Arewa tare da samar wa matasa aikin yi da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Alhaji Ibrahim Gurgusku ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce Shugaba mai jiran gado yana da babban kalubale a gabansa idan aka lura da yadda al’amura da dama suka tabarbare.
Alhaji Ibrahim Potiskum wanda ya gode wa ’yan Najeriya, musamman matasa maza da mata da suka fito suka zabi Muhammadu Buhari da sauran wadanda suke da yakinin za su yi musu adalci a yayin tafiyar da gwamnati. Ya ce zaben da ya gabata ya nuna wa duniya cewa lallai Najeriya kasa daya ce al’umma daya.
Don haka sai ya yi fata Shugaban kasa mai jiran gadon da sauran shugabanni da wakilan al’umma da za su kama ragamar mulki su yi kokari su sauke nauyin da Allah Ya dora musu. Ya ce duk da cewa kowa ya san Muhammdu Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana da son ciyar da kasa gaba, akwai bukatar sauran shugabanni da jama’ar kasa su dafa masa wajen aikata gaskiya da rikon amana tare da bin doka da oda don ceto kasar nan.