Akwai barazanar kai wa Majalisa harin ta’addanci- Shugaban Majalisa

Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da samun rahoton barazanar kai wa Majalisar dokokin Najeriya hari da wasu ’yan ta’adda ke shirin kai wa. Sanata Ahmed, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin ganawarsa da shugabannin tsaro, inda ya ce mutane da dama da ba’a san ko su wanene ba, […]

Akwai barazanar kai wa Majalisa harin ta’addanci- Shugaban Majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da samun rahoton barazanar kai wa Majalisar dokokin Najeriya hari da wasu ’yan ta’adda ke shirin kai wa.

Sanata Ahmed, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin ganawarsa da shugabannin tsaro, inda ya ce mutane da dama da ba’a san ko su wanene ba, suna shige da fice a majalisar ba tare da samun takardar gayyata ba.

Shugaban Majalisar ya bayyanawa mahalarta taron cewa, shi da kansa ya samu rahoto daga hukumar tsaron farin kaya ta DSS dangane da yiwuwar samun hare hare a majalisar, don haka ya nemi hukumomin tsaro su karfafa tsaro a majalisar domin kawar da yiwuwar kowanne irin hari.

Mai magana da yawun shugaban majalisar, Ola Awoniyi, ya ce shugaban Majalisar ya gargadi jami’an tsaron kamar haka; “Duk jami’in tsaron da muka ba shi aikin tabbatar da tsaro, sai kuma muka kama shi da hannu cikin wata matsala, za mu tabbatar da an hukunta shi.”

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa