Barazanar direbobi ta kawo karancin mai a arewacin Najeriya
Kungiyar Direbobin Tankokin Mai ta Kasa (PTD) ta umarci dukkan mambobinta da su dakatar da dakon man daga jihar Legas zuwa arewacin Najeriya har illa masha Allah. PTD a wata sanarwa da ta fitar ta bakin shugabanta na kasa, Mista Saliman Oladiti ranar Laraba ta ce matakin ya zama wajibi biyo bayan matakin gwamnatin jihar […]
Kungiyar Direbobin Tankokin Mai ta Kasa (PTD) ta umarci dukkan mambobinta da su dakatar da dakon man daga jihar Legas zuwa arewacin Najeriya har illa masha Allah.
PTD a wata sanarwa da ta fitar ta bakin shugabanta na kasa, Mista Saliman Oladiti ranar Laraba ta ce matakin ya zama wajibi biyo bayan matakin gwamnatin jihar Neja na hana manyan motoci amfani da titunan da su ka hada birnin Minna na jihar daga tsakar daren 15 ga watan Satumbar 2020.
Da zarar dokar dai ta fara aiki, dukkan tireloli da tankoki ba za su sami damar ratsawa cikin jihar ba.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya jagoranci rufe karshen hanyar garin Bidda a wani kwarya-kwaryar biki.
Ya ce sun dauki matakin ne saboda su ba kamfanin da ke aikin gyaran hanyoyin damar kammalasu cikin hanzari.
To sai dai kungiyar direbobin ta ce daga ranar Alhamis za su dakatar da dakon man har sai abinda hali ya yi.
Kungiyar ta ce, “Hanya daya tilo da ta rage za mu iya amfani da ita kuma ba ta da kyau. Ita ce hanyar Bida zuwa Agai zuwa Lapai wacce ta kuma dangana da Lambata. Wannan hanyar tarkon mutuwa ce.
“A lokacin da mu ka sami labarin matakin gwamnatin jihar na rufe hanyar, na yi magana da ministan ayyuka ta hannun wani mai taimaka masa, amma har yanzu abin takaici babu abinda aka yi.
“Mu a matsayinmu na ahugabanni, dole mu dauki matakan da za su kare rayukan mambobinmu daga hatsari na ba gaira ba dalili.
“Saboda haka daga ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba za mu dakatar da dakon mai daga jihar Legas zuwa arewacin Najeriya.
“Kuma muddin gwamnatin tarayya ba ta gyara titinan da za mu yi amfani da su ba, ba za mu dawo da dakon mai zuwa arewa ba,” inji kungiyar direbobin.