Ya kamata gwamnatin Najeriya ta cire tallafin wutar lantarki —IMF
IMF ta ce gwamnatin Najeriya na daukar nauyin abubuwan da suka fi karfinta.
Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya shawarci Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ta cire tallafin lantarki gaba daya.
Wannan na cikin wani rahoto da IMF ya wallafa a shafinsa na Intanet, inda ya ce gwamnatin Najeriya na dorawa kanta abubuwan da suke neman fin karfinta.
- Ba mu da hannu a kara farashin kayan abinci – ’Yan kasuwar Singa
- Amarya ta yi wa ango yankan rago a Neja
Asusun ya ce akwai bukatar ta janye tallafin lantarki kamar yadda ta cire na man fetur.
Asusun ya bayar da wannan shawarar ne a matsayin hanyar da Najeriya za ta bi domin farfado da tattalin arzikin kasar da yake tangal-tangal.
Wannan dai na zuwa ne, bayan da Gwamnatin Tarayya ta ce tallafin wutar lantarki daga watan Janairu zuwa Satumban 2023 ya lashe Naira biliyan 375.8, yayin da masu amfani da wutar lantarki suka biya jimillar Naira biliyan 782.6.
IMF ya yaba wa gwamnatin Najeriya kan sauye-sauyen da ta aiwatar zuwa yanzu amma ya sake nanata cewa akwai bukatar lallai a cire tallafin lantarki kamar yadda aka cire na man fetur.
’Yan Najeriya dai na kokawa kan yadda rayuwa ta yi tsada a kasar biyo bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Cire tallafin ya sanya farashin kayayyaki da na masarufi yin tashin gwauron zabi a kasar, lamarin da ya sa mutane da kokawa kan halin matsi da suke ciki.
Sai dai a gefe guda Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako biyu din daidaita farashin kayayyaki a kasar.