Akwai bukatar kotu ta yanke hukunci kan cancantar takarar Jonathan – kungiyar ACF
kungiyar Kare Maradun Arewa ACF ta nemi kotu ta yanke hukuncin a kan kararraki da ke gabanta dangane da cancantar takarar shugaba Goodluck Jonathan a zaben 2015, kafin 18 ga watan gobe na Disamba. A cewar kungiyar, ranar 18 ga watan Disamba ne ranar da Hukumar Zabe ta kasa ta saka ga kowace jam’iya ta […]
kungiyar Kare Maradun Arewa ACF ta nemi kotu ta yanke hukuncin a kan kararraki da ke gabanta dangane da cancantar takarar shugaba Goodluck Jonathan a zaben 2015, kafin 18 ga watan gobe na Disamba.
A cewar kungiyar, ranar 18 ga watan Disamba ne ranar da Hukumar Zabe ta kasa ta saka ga kowace jam’iya ta gabatar da sunan dan takararta a Zaben 2015.
A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai a jahar, mai dauke da sa hannun babban sakatarenta, Konar Jip Ubah, kungiyar ta ce akwai matukar mahimmanci ga ‘yan Najeriya su ji sakamakon kararrakin da aka kai gaban kotu kan cancantar takararsa kafin shekara mai zuwa.
kungiya ta kuma ce abin takaici ne a ce duk da abubuwan da ke faruwa a kasar nan ‘yan arewa da ke aiki karkashin gwamnatin Jonathan sun ki ficewa daga gwamnatinsa, a maimakon haka ma da su ake duk wata makarkashiya, domin cutar da ’yan kasar nan ta hanyar sata da rashin iya mulki, wanda a cewarta hakan bai da ce ba, amma kuma duniya ce za su yi bayani.
“A wajen taron mun kuma tattauna yadda shugaban kasa ke neman a tsawaita dokar ta baci a yankin Arewa maso Gabas a kuma jihohin Borno da Adamawa da Yobe. A baya dokar tabacin babu abin da ta haifar illa rashin tsaro, don haka muke kira ga ’yan majalisu da kada su yarda su amince da tsawaita wannan doka.
“Muna kuma kira da kaukausar murya ga ’yan majalisun kada su amince da bukatar bangaren zartarwa ga dokar.
“Mun kuma yi Allah wadai da harin bam da wasu mata ’yan kunar bakin wake suka kai a Maiduguri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30. Wadannan hare-hare ke sa mu rika yin tambayan ko gwamnatin tarayya za ta iya magance wadannan matsaloli.
“Wannan rashin tsaro na sanya ’yan Najeria fara tunanin neman kare kansu, domin kuwa an rigaya an kai su bango,” inji su.
ACF Sun kuma nemi gwamnatin tarayya ta rika barin ’yan sanda su yi aikinsu yadda ya kamata ba tare da yi masu shisshigi ba.